Abu 4 da gwamnatin Najeriya ta ce ta yi da kuɗin tallafin man fetur da ta tara

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Gwamnatin Najeriya ta bayyana adadin kuɗaɗen da ta fara daga tallafin man fetur da ta cire a watan Mayun 2023.

A lokacin cire tallafin, Shugaba Tinubu ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon yadda ake zargin cewa wasu tsiraru na amfani da tallafin wajen arzurta kansu.

Inda kuma ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen gudanar da ayyukan cin gaban ƙasa.

Sai dai tun bayan cire tallafin ƴanƙasar da dama sun ci gaba da aza ayar tambaya kan nawa gwamnatin ta tara, kuma me ta yi da shi.

To amma a karon farko gwamnatin ta bayyana kuɗaɗen da ta tara sakamakon matakin da yadda ta kashe su.

Nawa gwamnati ta tara daga cire tallafin?

Ministan Kuɗin ƙasar, Taiwo Oyedele ya ce an tara jimillar naira tiriliyan 15.8 daga kuɗaɗen tallafin man fetur ɗin tsakanin watan Yunin 2023 da Disamban 2025.

Yayin wani taron manema labarai kan nazarin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Najeriya ta aiwatar daga 2023 zuwa 2026, mista Oyedele ya ce nan ba da jimawa ba gwamnati za ta fitar da cikakken rahoto kan yadda aka kashe kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin.

"Tsakanin Yunin 2023 da Disamban 2025, an tara naira tiriliyan 15.8 daga kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur domin amfanin ƙasa."

Ministan kuɗin ya ƙara da cewa gwamnati ta samu ƙarin naira tiriliyan 3.1 a matsayin kuɗaɗen shiga masu zaman kansu, mafi yawansu daga kuɗaɗen haraji da hukumomi da cibiyoyin gwamnati suka tara.

Oyedele ya ce jimillar kuɗaɗen da gwamnatin gwamnatin Tinubu ta tara daga cire tallafin man fetur da sauran kuɗaɗen shiga da bashin da aka karbo ya kai naira tiriliyan 20

"Idan aka haɗa komai wuri guda, kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta samu a wannan lokaci daga cire tallafin man fetur da sauran kuɗaɗen shiga da kuma bashi sun kai naira tiriliyan 20.4."

Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ƙara karɓar naira tiriliyan 11.9 a matsayin bashi tsakanin Yunin 2023 da Disamban 2025.

ƴan ƙasar da dama dai na sukar gwamnatin da ci gaba da karɓar bashi duk da cire tallafin na man fetur da gwamnatin ta yi.

Sai dai Mista Oyedele ya bayar da masar cewa nauyin da ke kan gwamnati na da yawa.

''Gwamnati ta kashe naira tiriliyan 30.64 wajen aikace-aikace tsawon lokacin cire tallafin na man fetur'',in ji shi.

Ta yaya gwamnati ta kashe kuɗaɗen?

Ministan ya kuma yi ƙarin haske kan hanyoyin da gwamnatin ta bi wajen kashe kuɗaɗen, waɗanda ya ce sun taimaka wajen toshe wa gwamnatin wasu hanyoyin.

Ya bayyana hanyoyi uku da ya ce ta nan ne gwamnatin ta kashe kuɗaɗen waɗanda suka haɗa:

Raba wa matakan gwamnati uku

Ministan kuɗin ya ce daga cikin naira tiriliyan 15.8 da gwamnatin ta samu sakamakon cire tallafin man fetur, naira tiriliyan 5.4 sun shiga asusun Gwamnatin Tarayya, yayin da aka raba naira tiriliyan 10.4 ga gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi.

Mista Oyedele ya ce jihohi da ƙananan hukumomi sun samun wannan kaso ne, saboda ba gwamnatin Tarayya kaɗai ba ce cire tallafin ya shafa ba.

Ya ce gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ma sun fuskanci tasirin matakin, wanda hakan ya bayyana a tsarin rabon kuɗaɗen shiga na tarayya.

A cewarsa, ya zama wajibi a tabbatar jihohi da ƙananan hukumomi sun amfana daga kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin.

A lokuta da dama an sha jin shugaba Tinubu na cewa gwamnatinsa ta ƙara yawan kuɗin da ake bai wa jihohi a wata-wata sakamakon cire tallafin na man fetur.

Ƙarin albashi da alawus ɗin ma'aikata

Ministan kuɗin ya ce mafi yawan kuɗaɗen sun tafi ne wajen aiwatar da sabon ƙarin albashin da gwamnati ta yi a shekarar 2024.

Oyedele ya ce gwamnati ta yi amfani da naira tiriliya 9 wajen aiwatar da sabon ƙarin albashin ma'aikata da alawu-alawus ɗinsu.

Ministan ya ce wannan kuɗi ya zarce gaba ɗaya naira tiriliyan 5.4 da Gwamnatin Tarayya ta samu daga kasonta na kuɗaɗen cire tallafin man fetur ɗin.

A watan Yulin 2024 ne Shugaba Tinubu ya amince da naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ƙasar, daga naira 30,000 da ake biya a baya.

Oyedele ya ce kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta kashe wajen ƙarin albashin sun fi yawan kason da ta samu daga cire tallafin man fetur ɗin.

Biyan basuka

Oyedele ya ce gwamnati ta kashe wani kaso na kuɗaɗen wajn biyan bashin da ake bin ƙasar daga ƙetyare.

A cewarsa kuɗaɗen da aka kashe wajen ƙarin albashi da kuma biyan bashin ƙasashen waje su ne manyan abubuwan da suka fi laƙume kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin.

''An kashe kusan naira tiriliyan 9.37 wajen biyan bashin ƙasashen waje'', in ji shi.

Ministan ya ce ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa wajen biyan bashin ƙasashen wajen sun yi yawa ne sakamakon faɗuwar darajar naira.

Ya bayyana cewa duk da cewa ana lissafa bashin ne da dalar Amurka, ana biyan sa ne da naira kuma hakan ya sa adadin kuɗin ya ƙaru sosai.

"Idan a baya muna biyan dala miliyan ɗaya a matsayin kuɗin ruwa kan bashin ƙasashen waje, to yanzu ma dala miliyan ɗayar ake biya. Kum idan ka duba a baya ana canjin dala kan naira 460, yayin da yanzu ta kai naira 1,415, ka ga dole adadin kuɗin da muke biya ya ƙaru sosai."

Ya ƙara da cewa idan lokacin biyan bashi ya yi, ba za a iya yin ciniki ko neman jinkiri ba.

''Dole ne a biya, domin jinkirta biyan bashi ko kasa biya gaba ɗaya na da tasa mummunar illar," kamar yadda ya bayyana.

Yin manyan ayyuka

Hanya ta uku da ministan ya ce an yi amfani da kuɗaɗen cire tallafin ita ce gudanar da manyan ayyukan da abubuwan more rayuwa da gwamnati ke yi.

''Wannan fanni ya laƙume kusan naira tiriliyan 6.5'', in ji shi.

Ministan ya ce akwai ayyuka da dama da abubuwan more rayuwa da gwamnatin da gudanar ta hanyar amfani da waɗannan kuɗaɗe.

Daga ciki ya lissafa gina tituna masu yawa johohin ƙasar daban-daban.