Coventry ta dauki Awoniyi daga Forest fam miliyan 9
Coventry City ta kammala ɗaukar ɗan wasan gaba na Najeriya Taiwo Awoniyi daga Nottingham Forest kan kuɗin fam miliyan 9.
Ɗan wasan mai shekaru 29 ya koma Coventry kafin wasan buɗe kakar Premier League da za su yi da zakarun gasar Arsenal ranar Juma’a, yayin da kulob ɗin ya koma gasar ta matakin farko bayan shekaru 25 da rashin halarta.
Awoniyi ya samu gaisuwar ban girma (guard of honour) daga ‘yan wasan da ma’aikatan Forest kafin fara rabin na biyu na wasan sada zumunta na ƙarshe da suka buga da Brest ranar Lahadi. Hakan ya ba shi damar yin bankwana da magoya baya a filin City Ground, inda ya shafe shekaru huɗu da suka gabata.
Kocin Forest, Oliver Glasner, ya ce bayan nasarar da suka samu da ci 2-0 a kan ƙungiyar ta Ligue 1:
"Tabbas yana cikin mafi kyawun mutane da na taɓa haɗuwa da su. Kullum yana da kirki, yana murmushi."
Ya ƙara da cewa:"Kowa a cikin kulob ɗin yana son sa, kuma na ga cewa magoya baya ma suna son sa domin wannan shi ne irin abin da mutane ke girmamawa.
Kullum yana ba da kashi 100 cikin 100 domin ƙungiyar, kuma ko yana benci ma yana bayar da cikakken goyon baya. Shi ya sa ya cancanci irin wannan bankwana da wannan gaisuwar ban girma. Mun yanke shawarar yi masa hakan, kuma ina masa fatan alheri a sabon kulob ɗinsa, amma ba lokacin da za su kara da mu ba."Awoniyi ya zama ɗan wasa mafi tsada da Nottingham Forest ta taɓa saya a lokacin da ya koma daga Union Berlin a shekarar 2022 kan kuɗin fam miliyan 17.2.
A tsawon zamansa a Forest, ya ci ƙwallaye 23 a wasanni 103. Sai dai ya kasance a baya wajen samun gurbin buga wasa idan aka kwatanta da Chris Wood da Igor Jesus, kuma ba a saka shi cikin tawagar Forest da ta buga Europa League a kakar wasan da ta gabata ba.