Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda dangin Adeleke suka mamaye siyasar jihar Osun
- Marubuci, Abubakar Maccido
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
Iyalan Chief Raji Adeleke na daga cikin fitattun ƴan siyasar da suka daɗe suna tasiri a tarihin siyasar Najeriya, musamman a jihar Osun.
Tafiyar siyasar dangin ta samo asali ne shekaru da dama da suka gabata, tun daga lokacin Jamhuriyya ta Biyu, inda suka rike muƙamai a majalisa, har zuwa samun shugabancin gwamnati a matakin jiha.
Ahalin wannan gidan sun gaji siyasa a matakin kasa da kasa tun farko, tare da goyon bayan jama'a, karfin kudi da kuma mutuncin sunan iyalin.
Wannan ya samo asali ne daga uban gidan, Chief Raji Ayoola Adeleke, wanda ya kasance babban jigo a siyasar Najeriya a Jamhuriyya ta Biyu. Ya wakilci Osun a matsayin sanata tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983.
Wa'adin da ya yi a majalisar dattawa ya taimaka wajen kafa sunan dangin a siyasar kasa, tare da bude kofar da sauran 'ya'yansa za su bi su shiga harkokin siyasa.
A tsawon shekaru, dangin Adeleke sun ci gaba da kasancewa cikin manyan ƴan siyasa a Osun, inda wasu suka riƙe muƙamin gwamnan jiha har sau biyu da sanatoci uku.
Tasirinsu a mulkin dimokuraɗiyya, tun daga Jamhuriyya ta Biyu zuwa yanzu, ya sa dangin Adeleke suka mamaye tarihin siyasar jihar Osun.
Yaushe siyasarsu ta fara?
Tafiyar siyasar dangin Adeleke ta kasu zuwa matakai uku: nasarar Raji Adeleke a matsayin sanata a Jamhuriyya ta Biyu; zaman Isiaka Adeleke gwamna da kuma sanata, da kuma zaman Ademola Adeleke gwamna a wannan dimokuraɗiyya.
Marigayi Chief Raji Ayoola Adeleke
Marigayi Chief Raji Ayoola Adeleke, wanda aka haifa ranar 27 ga Disamba, 1923, shi ne ɗan siyasa na farko daga dangin Adeleke.
Ya kasance mai fafutukar kare haƙƙin ma'aikata kuma sanata a lokacin Jamhuriyya ta Biyu, inda ya wakilci mazabar Sanatan Jihar Osun ta 11, wadda ta ƙunshi ƙananan hukumomi shida: Ede, Osogbo, Irepodun, Ifelodun, Odo Otin da Ila Orangun.
Ya halarci makarantar St Peter's Primary School da ke Ede tsakanin 1935 zuwa 1938, sannan ya shiga Ibadan Grammar School, inda ya kammala karatun sakandare a 1943.
A shekarar 1947, ya samu takardar shaidar aikin jinya daga Medical Department Nursing School. Ya kuma kasance ɗaya daga cikin mambobin farko na ƙungiyar ma'aikatan jinya ta Najeriya da aka kafa a 1948.
Raji ya zama mataimakin shugaban United Labour Congress of Nigeria, Daraktan Tsare-tsare na Federal Labour Advisory Council, sannan shugaban reshen kungiyar Red Cross ta Najeriya a Ede, Osun.
A shekarar 1976, aka ba shi sarautar Balogun na Ede a ƙarƙashin jam'iyyar Unity Party of Nigeria, UPN.
Ya lashe zaɓen sanata a zaɓen majalisar dokokin Najeriya na 1979.
Ya yi aure sau biyu. Matarsa ta biyu, Mrs Nnena Esther Adeleke, ta fito daga tsohuwar Enugu.
Ya haifi 'ya'ya biyar, ciki har da Sanata Isiaka Adeleke da Ademola Adeleke.
Marigayi Sanata Isiaka Adeleke
Marigayi Isiaka Adetunji Adeleke, wanda ya rayu daga 15 ga Janairun 1955 zuwa 23 ga Afrilun 2017, ya kasance sanata a Najeriya sau biyu. Ya wakilci Jihar Osun daga 2007 zuwa 2011 a jam'iyyar PDP, sannan ya sake lashe zaɓe a ƙarƙashin Jam'iyyar APC a shekarar 2015.
Ya fara zama ɗan Majalisar Dattawan Najeriya a shekarar 2007. Ya tsaya takarar sake komawa majalisar a ƙarƙashin PDP a zaɓen Afrilun 2011, amma ya zo na biyu da kuri'u 77,090.
Isiaka Adeleke ya shiga siyasar manyan jam'iyyu a farkon shekarun 1990, jim kaɗan bayan ƙirƙirar Jihar Osun daga tsohuwar Jihar Oyo a watan Agustan 1991.
Isiaka Adeleke ya shiga siyasa a shekarar 1991 a matsayin sabon shiga, bayan dawowarsa daga Amurka, inda ya amfana da ƙirƙirar Jihar Osun, dokar sojoji da ta hana wasu tsofaffin 'yan siyasa shiga siyasa, da kuma arzikin iyalinsa da kuma kyakkyawar alaƙar da yake da ita a yankin.
Ya tsaya takarar gwamnan Jihar Osun ƙarƙashin Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), jim kaɗan bayan dawowarsa daga Amurka.
Ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye duk da adawar da wasu fitattun masu faɗa-a-ji a siyasar jihar suka nuna masa.
Bayan juyin mulkin soja na watan Nuwamban 1993, wa'adin Adeleke na farko a babban ofishin siyasa ya zo ƙarshe.
Bayan rushewar Jamhuriya ta Uku, ya shiga ƙungiyar Afenifere, wata ƙungiyar zamantakewa da al'adun Yarbawa mai kuma tasiri a siyasa, wadda ta kasance muhimmiyar ƙungiyar adawa da mulkin soja.
Daga baya ya fice daga Afenifere ya koma Jam'iyyar Democratic Party of Nigeria (DPN), ɗaya daga cikin jam'iyyun da ke da alaƙa da shirin sauyin siyasa na zamanin mulkin Janar Sani Abacha.
Lokacin da Najeriya ta koma mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, Adeleke ya koma takarar zaɓe.
A zaɓen gama-gari na shekarar 2007, ya tsaya takarar kujerar Sanatan gundumar Osun West a ƙarƙashin PDP kuma ya yi nasara.
Adeleke ya sake tsayawa takarar kujerar Sanata mai wakiltar Osun West a zaɓen shekarar 2011 a ƙarƙashin PDP.
Sai dai ya sha kaye a hannun Mudasiru Oyetunde Hussein na Jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN). Rahotanni sun ce Adeleke ya samu kuri'u 77,090, yayin da Hussein ya samu 121,971.
Gwamna Ademola Adeleke
Ademola Adeleke, wanda aka haifa a ranar 13 ga Mayun 1960, shi ne gwamnan Jihar Osun na yanzu. Mahaifinsa, Sanata Raji Ayoola Adeleke, ya yi sanata a Jamhuriya ta Biyu, yayin da babban ɗan'uwansa, Sanata Isiaka Adeleke, ya zama gwamnan farar hula na farko na Jihar Osun.
Ko da yake Adeleke ya ce ya fara shiga harkokin siyasa tun da daɗewa, sai bayan rasuwar ɗan'uwansa Isiaka a watan Afrilun 2017 ne ya zama fitaccen ɗan siyasa a bainar jama'a.
Bayan rasuwar Isiaka Adeleke yana kan kujerar Sanata mai wakiltar Osun ta Yamma, Ademola Adeleke ya tsaya takarar kujerar da ya bari.
Ya tsaya takarar ne a ƙarƙashin PDP kuma ya lashe zaɓen cike gurin a watan Yulin 2017.
A baya Adeleke yana da alaƙa da APC, amma ya koma PDP a shekarar 2017 kafin ya tsaya takarar kujerar Sanata.
Bayan shafe kusan shekara guda a Majalisar Dattawa, Ademola ya mayar da hankalinsa kan takarar gwamnan Jihar Osun.
Ya lashe zaɓen fidda gwani na PDP na takarar gwamnan Jihar Osun a watan Yulin 2018, inda ya doke ɗan kasuwa Akin Ogunbiyi da ƙuri'u bakwai.
Zaɓen gwamnan da aka gudanar a watan Satumban 2018 ya zama ɗaya daga cikin zaɓukan da suka fi jawo ce-ce-ku-ce a tarihin siyasar Osun. Da farko, Adeleke ne ya samu mafi yawan ƙuri'u a babban zaɓen, amma INEC ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba, tare da umartar a gudanar da zaɓen ƙarin kuri'u.
Bayan kammala zaɓen, an ayyana ɗan takarar APC, Gboyega Oyetola, a matsayin wanda ya yi nasara.
Adeleke ya ƙalubalanci sakamakon a kotu.
A watan Maris na 2019, Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamnan Osun ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen 2018, tare da soke zaɓen ƙarin kuri'un.
Sai dai a ranar 5 ga Yulin 2019, Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gboyega Oyetola, lamarin da ya kawo ƙarshen yunƙurin farko na Adeleke na zama gwamnan Osun.
A shekarar 2022, Adeleke ya sake komawa siyasar Osun domin wani yunƙurin zama gwamna.
PDP ta tsayar da shi a matsayin ɗan takararta a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 16 ga Yulin 2022.
A wannan karon, ya sake fuskantar mutumin da ya doke shi shekaru huɗu da suka gabata, wato gwamnan da ke kan mulki, Gboyega Oyetola na APC.
Adeleke ya lashe zaɓen, inda aka bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.
A shekarar 2026, Ademola Adeleke ya sake lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun, inda ya tsaya takara a ƙarƙashin Jam'iyyar Accord kuma ya doke ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji. Wannan nasara ta ba shi damar ci gaba da zama gwamnan jihar na wani wa'adi.
Shin dangin Adeleke sun taɓa faduwa zaɓe?
Iyalin Adeleke sun taɓa faduwa a zaɓe, duk da cewa suna daga cikin 'yan siyasa masu ƙarfi a Jihar Osun.
- Isiaka Adeleke ya fadi zaɓen Sanata na 2011
Ɗaya daga cikin rashin nasarorin zaɓe da dangin Adeleke suka fuskanta shi ne a shekarar 2011.
Isiaka Adeleke, wanda ya taba zama gwamnan farar hula na farko na Jihar Osun sannan ya lashe kujerar Sanata mai wakiltar Osun a shekarar 2007, ya sake tsayawa takarar kujerar a shekarar 2011 a ƙarƙashin PDP.
Ya sha kaye a hannun Mudasiru Oyetunde Hussein na Jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).
- Ademola Adeleke ya fadi zaɓen gwamnan Osun na 2018
Bayan ya lashe kujerar Sanata mai wakiltar Osun ta Yamma a zaɓen cike gurbi na shekarar 2017, Ademola Adeleke ya tsaya takarar gwamnan Jihar Osun a shekarar 2018 a ƙarƙashin PDP.
Zaɓen da aka gudanar a ranar 22 ga Satumban 2018 ya dauki hankali.
Ga yadda sakamakon ya kasance:
Ademola Adeleke – ƙuri'u 254,698
Gboyega Oyetola, APC – ƙuri'u 254,345
Sai dai INEC ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba, sannan ta gudanar da zaɓen zagaye na biyu a ranar 27 ga Satumba.
Bayan zaɓen, an ayyana Oyetola a matsayin wanda ya yi nasara da:
Gboyega Oyetola – ƙuri'u 255,505
Ademola Adeleke – ƙuri'u 255,023
Bambancin ƙuri'un ƙarshe da ke tsakaninsu shi ne kuri'u 482 ne kawai.
Ƙalubalen da iyalan Adeleke suka fuskanta
- Rashin nasara a zaɓe*
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da dangin Adeleke suka fuskanta shi ne rashin samun nasara a wasu zaɓuka, duk da shahararsu a siyasa.
Isiaka ya fadi zaɓen Sanata na 2011, yayin da Ademola ya sha kaye a zaɓen gwamnan Osun na 2018.
- Ƙarfin abokan hamayya a siyasa
Dangin Adeleke sun fuskanci manyan abokan hamayya a siyasar Osun.
Ɗaya daga cikin misalan shi ne ACN da kuma APC a jihar.
A shekarun 2010, APC ta fafata ƙarƙashin Gwamna Rauf Aregbesola, sannan daga baya ƙarƙashin Gboyega Oyetola.
Ademola Adeleke ya fuskanci wannan ƙalubalen lokacin da ya tsaya takarar gwamna a 2018, sannan ya sake fuskantar irin wannan ƙalubalen a 2022.
- Rikicin cikin gida a jam'iyyu
Wani ƙalubale da iyalan suka fuskanta shi ne dangantakarsu da jam'iyyun siyasa. 'Yan'uwan Adeleke ba su cikin jam'iyya guda ɗaya a duk tsawon rayuwarsu ta siyasa.
Misali, Isiaka yana PDP kafin daga baya ya koma APC.
Ademola ma yana APC kafin ya koma PDP jim kaɗan kafin zaɓen cike gurbin Sanatan Osun ta Yamma na shekarar 2017.
A lokacin, an danganta komawarsa da wasu takun-saƙa da suka taso bayan rasuwar Isiaka da kuma neman tikitin APC.
- Rasuwar Isiaka Adeleke
Rasuwar Isiaka Adeleke a ranar 23 ga Afrilun 2017 ta kasance wani babban sauyi a tarihin siyasar gidan.
Mutuwarsa ta haifar da gibi a siyasar dangin Adeleke.
Ademola daga bisani ya shiga takarar neman maye gurbinsa a Majalisar Dattawa.
Ademola ya bar APC ya tsaya takara a ƙarƙashin PDP, inda daga baya ya doke ɗan takarar APC, Mudasiru Hussein, a zaɓen cike gurbin.