Kun san shafe dogon lokaci cikin talauci na iya shafar lafiyar ƙwaƙwalwarku?

    • Marubuci, Mariam Mjahid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mwandishi BBC Swahili
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 10

Ka buɗe wayarka da safe, sai ka tarar da saƙon bashi. Lokacin biyan kudin haya na karatowa, kuɗin makarantar yara suna jiranka, farashin abinci kuma na ci gaba da tashi.

Maimakon fara ranar cikin natsuwa, tunaninka ya mamaye da tambaya guda ɗaya: ina zan samu kuɗi?

Ga mutane da dama a Afirka, musamman a Gabashin Afirka, wannan ba wani yanayi ne na ɗan lokaci ba. Wani ɓangare ne na rayuwarsu ta yau da kullum.

Sai dai wani sabon bincike ya nuna cewa matsin tattalin arziki na dogon lokaci ba ya shafar lalitar mutum kawai. Haka kuma yana iya yin tasiri ga lafiyar kwakwalwa.

Wani bincike da masana kimiyya na Birtaniya suka gudanar ya gano cewa mutanen da ke fuskantar matsalolin kuɗi na tsawon lokaci na da yiwuwar samun kansu cikin larurar ƙwaƙwalwa da raguwar ƙarfin tunani da sarrafa bayanai yayin da suka kai matsakaitan shekaru.

Masu binciken sun bibiyi rayuwar sama da mutum 2,700 da aka haifa a watan Maris na shekarar 1946, suna nazarin yadda halin kuɗinsu ya shafi lafiyar kwakwalwarsu yayin da suka kai matsakaicin shekaru.

Wasu daga cikin manyan illolin da za su iya faruwa sun haɗa da:

Raguwar haddar ƙwaƙwalwa da iya tuna abubuwa.

Wahalar mayar da hankali da tattara tunani waje daya.

Raguwar saurin fahimta da sarrafa bayanai.

Ƙarancin iya warware matsaloli da yanke shawara.

Ƙaruwa a haɗarin matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa yayin tsufa.

Illolin damuwa mai tsawo ga aikin ƙwaƙwalwa gaba ɗaya.

Binciken ya nuna cewa talauci da ke ci gaba na shekaru na iya yin mummunan tasiri ga lafiyar ƙwaƙwalwa, kamar yadda yake shafar sauran ɓangarorin rayuwar mutum.

Mece ce alaƙar talauci da matsalar ƙwaƙwalwa?

Sakamakon binciken ya nuna cewa mutanen da suka shafe mafi yawan rayuwarsu ta balaga, daga shekarunsu na ashirin zuwa farkon shekarunsu na hamsin, a cikin rukunin masu ƙaramin ƙarfi, sun fi samun sakamako mara kyau a gwaje-gwajen ƙwaƙwalwa da ƙarfin tunani.

Binciken ya kuma gano cewa mutanen da suka fuskanci matsala ta kasa biyan kuɗaɗensu sau biyu ko fiye da haka a lokacin da suke cikin shekarunsu na talatin da arba'in, sun fi kasancewa cikin haɗarin samun matsalolin ƙwaƙwalwa da raguwar saurin sarrafa bayanai lokacin da suka kai matsakaitan shekaru.

Ko bayan da masu binciken suka yi la'akari da wasu abubuwa kamar yanayin rayuwar yara, matakin ilimi da kuma ƙwarewar tunani da mutum yake da su tun yana ƙarami, sun gano cewa alaƙar da ke tsakanin matsin tattalin arziki da matsalolin lafiyar kwakwalwa ta ci gaba da kasancewa a fili.

A cewar masu binciken, matsananciyar damuwar kuɗi ta dogon lokaci na iya yin tasiri har ma a kan wasu alamomin halittar kwakwalwa.

Gwaje-gwajen karatu, da lissafi da kuma hotunan binciken kwakwalwa sun nuna sauye-sauyen da ake dangantawa da shekaru na matsin tattalin arziki.

Ɗaya daga cikin marubutan binciken, Jacques Wels, ya ce hujjojin da suka tattara sun nuna cewa matsalolin kuɗi na iya yin tasiri kai tsaye ga lafiyar kwakwalwa.

Ya ce:

"Mun gano akwai dangantaka kai tsaye tsakanin matsin tattalin arziki da lafiyar kwakwalwa. Alamomi kamar saurin karatu, da ƙwarewar lissafi da kuma hotunan binciken kwakwalwa sun nuna cewa damuwar kuɗi ta dogon lokaci na iya tasiri na tsawon lokaci a kan mutum."

Sai dai binciken ya kuma gano wani abin mamaki. Mutanen da suka fuskanci matsananciyar damuwar kuɗi a rayuwarsu sun nuna raguwar ƙarfin tunani a hankali yayin da suke tsufa idan aka kwatanta da wasu.

Amma masu binciken sun yi hasashen cewa hakan na iya kasancewa ne saboda yawancin illolin sun riga sun faru tun a farkon rayuwarsu, kafin su kai shekaru masu yawa.

Yadda bashi ke rikita ƙwaƙwalwar mutane

Masana sun bayyana cewa matsalolin kuɗi da matsalolin lafiyar kwakwalwa na iya shiga wani mummunan mataki da ke ci gaba da sa matsalolin kara girma.

Lokacin da mutum yake fama da damuwa ko baƙin ciki, ƙarfinsa na yanke shawarar da ta shafi kuɗi kan ragu. Wasu kan fara guje wa buɗe wasiƙun bashi, da duba asusun bankinsu ko amsa wayar masu bin su bashi.

Sakamakon haka, kuɗaɗen kan taru su yi yawa - saboda jinkirin biyan bashi da ribar bashin kan ƙaru, lamarin da ke ƙara tsananta damuwa da matsin tattalin arziki.

Masana sun yi gargaɗin cewa idan ba a shawo kan matsananciyar damuwar kuɗi ba, tana iya haifar da:

Yawan damuwa a kai-a kai game da bashi, kuɗin bukatun yau da kullum da sauran nauye-nauyen rayuwa.

Baƙin ciki da rashin fata na samun mafita ga matsalolin kuɗi.

Rashin barci ko barcin da ba ya gamsarwa.

Rikice-rikice tsakanin ma'aurata, da sauran wadanda ake da dangantaka da su.

Matsalolin lafiyar jiki kamar ciwon kai, matsewar tsokoki da kuma hawan jini.

Binciken ya nuna cewa matsin tattalin arziki ba yana shafar harkar kuɗin mutum ba ne kawai.

Haka kuma yana iya yin tasiri ga lafiyar kwakwalwa, dangantakar iyali da kuma lafiyar jiki gaba ɗaya. Don haka masana na jaddada muhimmancin samun hanyoyin rage damuwar kuɗi da kuma neman taimako tun da wuri idan matsalar ta fara shafar rayuwar yau da kullum.

Me ya sa kuɗi ke iya shafar lafiyar ƙwaƙwalwa?

Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce jikin ɗan'Adam ba a tsara shi ya kasance cikin yanayin fargaba da damuwa na dogon lokaci ba.

Lokacin da mutum ke fama kullum da tunanin yadda zai biya haraji, samun abinci, kuɗin jinya ko na karatun yara, jiki kan fara fitar da sinadaran damuwa irin su cortisol a matakai masu yawa.

A ɗan gajeren lokaci, wannan sinadari na taimaka wa jiki wajen fuskantar ƙalubale da matsaloli.

Amma idan damuwar ta ci gaba har tsawon watanni ko ma shekaru, yawan sinadarin (cortisol) a jiki na iya fara shafar sassan ƙwaƙwalwa da ke da alhakin koyo da kuma yanke shawara.

Wannan na iya sa mutum ya rika samun matsala wajen mayar da hankali na dogon lokaci, ya rika mantuwa da abubuwa cikin sauƙi, ko kuma ya kasa yanke muhimman shawarwari.

Saboda haka ne masana ke cewa matsalolin kuɗi da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa sukan kasance suna ƙarfafa juna.

Misali, mutumin da yake fama da tarin bashi na iya fara gujewa buɗe takardun banki ko kuma wasiƙun bashi saboda tsoro. Yayin da yake ci gaba da jinkirtawa, bashin kan ƙaru, ribar bashi ta taru, kuma damuwarsa ta ƙara tsananta.

Matakan da za su iya rage matsalar rashin kuɗi

1. Nazarin halin da kake ciki na kudi

Masana sun ce tsoro da damuwa kan fi tsananta idan mutum bai san hakikanin yanayin kuɗinsa ba.

Saboda haka suna ba da shawarar a fara da rubuta:

Dukkan hanyoyin samun kuɗin shiga.

Kuɗaɗen da ake kashewa a kowane wata.

Duk wani bashi da ake bi.

Kason ribar da ake biya a kan bashi.

Ranakun biyan bashi ko sauran kuɗaɗe.

Wannan mataki na iya taimaka wa mutum ya fahimci ainihin matsayinsa na kuɗi, maimakon dogaro da zato ko tsoro.

Haka kuma, zai ba shi damar tsara yadda zai magance matsalolinsa a hankali, tare da gano wuraren da zai rage kashe kuɗi ko yadda zai fifita biyan bashin da ya fi muhimmanci.

2. Ka yi kasafi

Masana sun ce tsara kasafin kuɗi na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin da za su taimaka wa mutum wajen sarrafa kashe kuɗinsa da kuma rage matsin tattalin arziki.

Ɗaya daga cikin ƙa'idojin da aka fi ba da shawara ita ce ta 50-30-20, wadda ta tanadi cewa:

  • Kashi 50 cikin 100 na kuɗin shiga a ware shi domin muhimman buƙatu kamar abinci, haya, sufuri da biyan kuɗaɗen lantarki da ruwa.
  • Kashi 30 cikin 100 a kashe shi kan buƙatu na zaɓi, kamar nishaɗi da wasu abubuwan jin daɗin rayuwa.
  • Kashi 20 cikin 100 a ware shi domin ajiya da kuma biyan basussuka.

Sai dai idan mutum na fama da manyan basussuka, masana suna ba da shawarar a rage kuɗin da ake kashewa kan abubuwan da ba su da matuƙar muhimmanci, sannan a ƙara yawan kuɗin da ake warewa wajen biyan bashi har sai an daidaita halin da ake ciki.

Sun ce bin tsari mai kyau na kasafin kuɗi na iya taimakawa wajen samun iko a kan harkokin kuɗi, rage damuwa da kuma gina ingantacciyar makoma ta tattalin arziki.

3. Ka tsara yadda za ka biya bashi

Debt is one of the biggest sources of financial stress.

Some experts advise starting with the smallest debt first to gain motivation to keep going, while others recommend starting with the highest-interest debt to reduce costs in the long run.

The important thing is to have a workable plan.

Bashi na daga cikin manyan abubuwan da ke jefa mutane cikin matsin tattalin arziki

Masana sun ce basussuka na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa damuwa da rashin kwanciyar hankali a rayuwar mutane.

Wasu ƙwararru kan ba da shawarar a fara biyan ƙaramin bashi da farko. Sun ce hakan na taimaka wa mutum ganin sakamako cikin sauri, wanda ke ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da biyan sauran basussuka.

Wasu kuma suna ganin ya fi dacewa a fara biyan bashin da ke da mafi girman ruwa, domin rage kuɗin ribar da za a biya a nan gaba da kuma rage nauyin bashi cikin sauri.

Duk da bambancin ra'ayoyin, masana sun ce abin da ya fi muhimmanci shi ne mutum ya kasance da tsarin da zai iya aiwatarwa kuma ya ci gaba da bin sa.

Samun ingantaccen shiri na biyan bashi na iya taimakawa wajen rage damuwar kuɗi, inganta lafiyar kwakwalwa da kuma ba mutum damar sake samun iko kan harkokinsa na kuɗi.

4. A ware kuɗin gaggawa

Masana sun ce samun wani ƙaramin asusun ajiyar kuɗin tunkarar bukatu na gaggawa na iya taimakawa matuƙa wajen rage matsin tattalin arziki da damuwar da ke tattare da shi.

Ko da kuwa mutum ba zai iya ajiye kuɗi masu yawa ba, sanya ɗan abin da ya samu a gefe akai-akai na iya taimakawa wajen fuskantar abubuwan da ba a yi wa tsammani ba, kamar rashin lafiya, gyaran gida ko mota, ko kuma rasa aikin yi.

Samun irin wannan ajiya na gaggawa na rage yiwuwar komawa karɓar sabon bashi a duk lokacin da wata matsala ta taso.

Masana sun ba da shawarar a rika ware wani kaso na kuɗin shiga a kai a kai, ko da kuwa kaɗan ne, domin gina wannan asusu sannu a hankali.

A cewarsu, ajiyar kuɗin gaggawa ba wai kawai tana taimakawa harkokin kuɗi ba ne, har ma tana ba mutum kwanciyar hankali da rage damuwar da ke tattare da rashin tabbas a rayuwa.

5. A daina kashe kuɗi ba gaira ba dalili

Ƙananan sauye-sauye na iya kawo babban sauyi

Masana sun ce ƙananan canje-canje a yadda mutum ke kashe kuɗinsa na iya taimakawa sosai wajen rage matsin tattalin arziki, ba tare da sun yi tasiri mai yawa ga ingancin rayuwarsa ba.

Daga cikin matakan da suke ba da shawara akwai:

  • Dafa abinci a gida maimakon yawan sayen abinci a gidajen abinci ko wuraren sayar da abinci.
  • Soke kuɗin biyan wasu ayyuka ko manhajoji da ba a amfani da su akai-akai.
  • Amfani da sufuri na haɗin gwiwa ko na jama'a idan hakan ya yiwu.
  • Sayen kayayyaki a lokacin da suke araha ko sauki.

Masana sun ce duk da cewa waɗannan matakai na iya zama ƙanana, idan aka ci gaba da aiwatar da su akai-akai za su iya rage kashe kuɗi, ƙara yawan ajiya da kuma taimakawa wajen inganta yanayin kuɗin mutum a dogon lokaci.

6. Nemi taimako lokacin da kake bukata.

Masana sun ce babu abin kunya a neman taimako lokacin da mutum ke fuskantar matsalolin kuɗi.

A ƙasashe da dama, gwamnatoci da ƙungiyoyi masu zaman kansu suna samar da shirye-shiryen tallafa wa iyalan da ke fama da ƙalubalen tattalin arziki. Waɗannan tallafe-tallafen na iya haɗawa da:

Taimakon abinci.

Tallafin kuɗin haya ko matsuguni.

Taimakawa wajen biyan kuɗin lantarki, ruwa da sauran muhimman buƙatu.

Ba da shawara kan yadda za a gudanar da basussuka da tsara kuɗi.

Haka kuma a ƙasashen Gabashin Afirka, wasu hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin al'umma da cibiyoyin kuɗi na samar da shirye-shiryen ba da shawarwari kan harkokin kuɗi da kuma taimaka wa mutanen da ke fuskantar matsalolin tattalin arziki.

Masana sun jaddada cewa neman shawara ko taimako da wuri na iya hana matsalolin kuɗi tsananta, tare da rage damuwa da kuma kare lafiyar kwakwalwa.

7. Kare lafiyar ƙwaƙwalwa

Kula da lafiyar kwakwalwa na da muhimmanci kamar kula da harkokin kuɗi

Masana sun jaddada cewa lafiyar kwakwalwa na da muhimmanci kamar lafiyar tattalin arziki, domin ɗaya na iya yin tasiri kai tsaye ga ɗayan.

Sun ce rage damuwa ta hanyoyi kamar:

  • Yin motsa jiki a kai a kai.
  • Samun isasshen barci.
  • Tattaunawa da mutanen da ake yarda da su.

Neman shawarar ƙwararrun masu kula da lafiyar kwakwalwa idan buƙata ta taso.

na iya taimakawa wajen inganta ikon mutum na yanke shawara mai kyau kan kuɗinsa da kuma fuskantar ƙalubalen rayuwa cikin nagarta.

A cewar masana, idan damuwa ta ragu, mutum kan fi samun damar tsara harkokinsa na kuɗi, guje wa yanke shawara cikin gaggawa, da kuma nemo hanyoyin magance matsalolinsa cikin natsuwa.

Sun ƙara da cewa ƙananan matakan da mutum ya ɗauka a yau na iya taimakawa wajen karya mummunan zagayen tsoro da damuwar kuɗi, tare da ba shi damar sake gina kwanciyar hankali a harkokin tattalin arziki da kuma inganta rayuwarsa gaba ɗaya.

Ko da matsalar kuɗi na da girma, masana sun ce mataki ɗaya bayan ɗaya na iya kawo canji mai ma'ana, kuma waɗanda suke neman taimako ne suke samunshi.

Matakin talauci a Afirka

Talauci na ci gaba da ƙaruwa a yankin hamadar Sahara ta Afirka

Yayin da aka samu gagarumar raguwar talauci a ƙasashe irin su China da Indiya, inda yawan mutane kusan biliyan ɗaya suka fita daga kangin talauci, a yankin hamadar Sahara ta Afirka, yawan mutanen da ke fama da matsanancin talauci ya fi na shekaru 25 da suka gabata yawa.

Daraktar kula da ayyukan yaƙi da talauci da inganta daidaito ta Bankin Duniya, Carolina Sánchez-Páramo, ta ce:

"A cikin shekaru goma da suka gabata, mun ga duniya tana tafiya cikin sauri nau'i biyu daban-daban."

Ta ce yayin da wasu yankuna na duniya suka samu ci gaba mai yawa wajen rage talauci, wasu kuwa, musamman a Afirka, na ci gaba da fuskantar ƙalubale.

A cewar Bankin Duniya, fiye da mutum miliyan 460 a Afirka na kudu da hamadar Sahara har yanzu suna rayuwa cikin matsanancin talauci, wato suna samun ƙasa da dala 2.15 a rana.

Rahoton ya nuna cewa duk da bunƙasar tattalin arziki da aka samu a wasu ƙasashen yankin, adadin mutanen da ke fama da matsanancin talauci ya fi yadda yake shekaru 15 da suka gabata, abin da ke nuna cewa ci gaban tattalin arzikin bai kai ga rayuwar talakawa yadda ya kamata ba.