Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihohin Najeriya 5 da kowane ɗantakarar shugaban ƙasa ke son lashewa
A hukumance an fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki na 2027 a ranar Laraba, 19 ga Agusta 2026, abin da ke nufin an fara shirin yaɗa manufofin da za su kai ga babban zaɓen da ke tafe.
A ranar Talata, Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa ya gayyaci dukkan jam'iyyun siyasar da ke da ƴan takarar shugaban ƙasa domin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, wadda ke ƙunshe da alƙawarin gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.
A shekarun da aka yi ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, akwai wasu muhimman jihohi da ƴan siyasa ke mayar wa da hankali na musamman, saboda ganin cewa nasara a irin waɗannan jihohi na iya ƙara musu damar lashe zaɓen ƙasa baki ɗaya.
BBC ta yi nazari kan waɗannan muhimman jihohi, dalilin da ya sa suke da muhimmanci da kuma yadda 'yan siyasa ke ƙoƙarin samun nasara.
Jihar Kano
Jihar Kano ita ce jihar da ta fi yawan jama'a a Najeriya ba, har ila yau tana da mafi yawan masu rajistar zaɓe, sama da miliyan takwas. Alkaluman zaɓukan baya kuma na nuna cewa masu zaɓe a Kano na yawan fitowa sosai domin kaɗa ƙuri'a.
A zaɓen 2023, Shugaba Tinubu ya sha kaye a Kano, inda ya samu ƙuri'u 517,341, yayin da Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP ya samu ƙuri'u 997,279.
Yanzu Kwankwaso ya haɗa kai da Peter Obi a jam'iyyar NDC, inda ya zama abokin takararsa na mataimakin shugaban ƙasa. A gefe guda kuma, gwamnan Kano na yanzu, Abba Yusuf, ya fice daga NNPP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Saboda haka, ana sa ran za a samu fafatawa mai zafi a Kano a zaɓen 2027, musamman wajen ganin wanda ya fi samun goyon bayan jama'a tsakanin Kwankwaso da Gwamna Yusuf.
Duka jam'iyyun NDC da APC sun fara gudanar da ƙananan taruka domin ƙara yawan magoya bayansu. Yanzu da yaƙin neman zaɓe ya fara sosai, Kano na daga cikin jihohin da za a sanya ido a kansu.
Jihar Legas
Legas ita ce jiha ta biyu mafi yawan jama'a a Najeriya, duk da cewa tana cikin jihohin da ke da ƙaramin faɗin ƙasa.
Bayanan hukumomi na watan Yunin 2025 sun nuna cewa Legas na da jimillar masu rajistar zaɓe 7,060,195, sai dai ana sa ran adadin zai ƙaru kafin zaɓen 2027.
Zaɓen da ke tafe zai ƙara sanya Legas cikin manyan wuraren da za a mayar da hankali, saboda Shugaba Bola Tinubu, wanda ke neman wa'adin mulki na biyu, ya fito ne daga Legas. Ya taɓa zama gwamnan jihar daga 1999 zuwa 2007.
Sai dai abin ya ba mutane mamaki lokacin da Tinubu ya sha kaye a Legas a zaɓen 2023. Ya samu ƙuri'u 572,606, yayin da Peter Obi na Labour Party ya samu 582,454.
A wannan karon ma ana ganin za a iya samun fafatawa mai zafi, saboda jam'iyyar APC mai mulki ba za ta so sake shan kaye a jihar da ake kallonta a matsayin sansaninta ba.
Tuni jam'iyyar mai mulki ta fara gudanar da ayyuka da gangamin ƙara wayar da kan magoya bayanta kafin kamfen ya ɗauki zafi sosai.
A bangaren manyan jam'iyyun adawa biyu, ADC da NDC, har yanzu ba a ga wani gagarumin shiri daga wurinsu ba. Sai dai ADC a Legas ta zargi ƴan baranda masu goyon bayan APC da tarwatsa wasu daga cikin tarukan da take son gudanarwa.
Jihar Rivers
Rivers na cikin jihohin da suka zama masu matuƙar muhimmanci a zaɓen 2023, inda sakamakon da INEC ta sanar ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya yi nasara a jihar, duk da cewa a lokacin jihar tana ƙarƙashin ikon jam'iyyar PDP da Nyesom Wike ke jagoranta.
Sai dai wani binciken BBC daga baya ya gano cewa sakamakon da INEC ta sanar a Rivers na iya kasancewa da wasu kura-kurai.
A halin yanzu, Nyesom Wike har yanzu yana ikirarin cewa shi ɗan jam'iyyar PDP ne, amma yana cikin gwamnatin Tinubu a matsayin ministan Abuja, kuma har yanzu yana da babban tasiri a siyasar jihar Rivers.
Rivers na cikin jihohin goma mafi yawan jama'a a Najeriya, kuma tana daga cikin jihohin da suka fi arziki a ƙasar.
Waɗannan abubuwa sun sa Rivers ta zama tana muhimmanci ga duk wani ɗansiyasar da ke neman nasara a zaɓen shugaban ƙasa.
A halin yanzu, APC ce jam'iyyar da aka fi ganin tasirinta a jihar, musamman saboda kasancewar Wike a gwamnatin tarayya. Duk da cewa har yanzu yana cikin PDP, ya bayyana goyon bayansa ga neman wa'adin mulki na biyu na Tinubu.
Wike ya kuma kafa abin da ya kira "Rainbow Coalition", wanda ya ƙunshi ƴan siyasa daga jam'iyyu daban-daban da suka haɗu da manufa guda ta goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu.
Kaduna da Katsina
Kaduna da Katsina na daga cikin jihohin da 'yan siyasa ke fafutukar samun ƙuri'u masu yawa daga can, saboda yadda masu zaɓe ke yin zaɓe bisa alaƙarsu da wata ƙungiya ko jam'iyya da kuma yawan masu fitowa zaɓe.
A zaɓen 2023, shugaba Tinubu ya sha kaye a jihohin biyu a hannun Atiku Abubakar na PDP, duk da cewa APC ta samu nasara a zaɓen gwamnonin jihohin makonni biyu bayan na shugaban ƙasa.
A wannan karon, Atiku yana takara ne ƙarƙashin ADC, yayin da ake ganin APC ta ƙara samun karfi a jihohin.
Sai dai jihohin biyu na daga cikin wuraren da matsalar tsaro ta fi muni a Najeriya, abin da masana harkokin siyasa ke ganin zai iya sa wasu masu zaɓe su yi amfani da ƙuri'unsu wajen nuna rashin gamsuwa da jam'iyyar da ke mulki.
Haka kuma, tasirin Kwankwaso na iya taimaka wa NDC wajen samun ƙarin goyon baya a wannan yanki.
A bayyane yake cewa fafatawar za ta yi zafi ga duk wanda ke son lashe jihohin, da ma sauran jihohin Arewa maso Yamma.
A yi siyasa ba tare da ɓatanci ba - INEC
A wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar Talata, 18 ga Agusta 2026, hukumar zaɓe ta INEC, ta buƙaci ƴan siyasa su mutunta juna a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Hukumar ta kuma jaddada cewa ba ta goyon bayan wani ɗan takara ko wata jam'iyya.
Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya ce: "INEC ba ta da wata sha'awa kan wanda zai yi nasara ko ya sha kaye a kowane zaɓe. Hukumar ba ta da ɗan takara, kuma ba ta fifita wata jam'iyyar siyasa ba."
Ya ƙara da cewa: "Ya kamata yaƙin neman zaɓen 2027 ya zama damar bayyana ra'ayoyi, ba filin yaƙi ba. 'Yan Najeriya ba sa son zagi, suna neman mafita ne. Suna son jin manufofi da tsare-tsare masu ma'ana da za a iya auna sakamakonsu."