Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/8/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 20 ga watan Agustan 2026.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello, Haruna Kakangi

  1. Majalisar dokokin Bangladesh ta zaɓi Fakhrul Islam a matsayin shugaban ƙasa

    Majalisar dokokin Bangladesh ta zaɓi Mirza Fakhrul Islam Alamgir a matsayin shugaban ƙasar, a zaɓen shugaban ƙasa na farko da aka yi takara a kai cikin shekaru talatin da biyar.

    Mista Alamgir, wanda ya fito daga jam'iyya mai mulki ta Bangladesh Nationalist Party (BNP), ya kasance fitaccen mai adawa da tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina, wadda aka hambarar a 2024 sakamakon zanga-zangar ɗalibai.

    Ya taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar jam'iyyar ta BNP a cikin wasu shekaru masu cike da ƙalubale, kuma an kama shi sau da dama.

    Zabensa na zuwa ne yayin da Tarique Rahman ke cika watanni shida a matsayin Firaminista.

    Matsayin shugaban ƙasa a Bangladesh dai na da ƙarancin iko, sai dai a ƙarƙashin sauye-sauyen da ake shirin yi, Bangladesh na iya ƙara wa ofishin ƙarin iko domin samar da daidaito tsakanin manyan shugabannin ƙasar.

  2. Yadda za ku kauce wa kamuwa daga ciwon idon Apollo

    Yayin da ake samun rahotonnin ɓarkewar cutar ciwon ido ta Apollo, likitoci sun fara gargaɗin ɗaukar matakan kauce wa ciwon.

    Apollo na haddasa kumburi da jajayen idanu tare da saurin yaɗuwa tsakanin mutane.

    Ciwon na haifar da damuwa musamman a wuraren taruwar jama'a kamar makarantu, kasuwanni da ofisoshi, inda mutane ke yawan mu'amala da juna.

    Apollo, wadda aka fi sani da ciwon ido mai saurin yaɗuwa, na iya shafar mutane ba tare da la'akari da shekaru ko jinsi ba.

    Masana lafiya na cewa ko da yake ba kasafai cutar ke haifar da matsaloli masu tsanani ba, tana iya janyo rashin jin daɗi da kuma katse harkokin yau da kullum na masu kamuwa da ita.

  3. Mutane 40 sun mutu a kifewar kwale-kwale a Sokoto - Reuters

    Wani kwale-kwale da ya kife a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ya haifar da mutuwar aƙalla mutum 40 yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

    "Zan iya tabbatar muku cewa ya zuwa yanzu an gano gawarwakin yara kimanin 40," a cewar wani jami'in hukumar sufurin jiragen ruwa ta Najeriya Abubakar Yusuf, a wani bayani da ya tura wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Lamarin ya faru ne a safiyar jiya Laraba sa'ilin da mutane ke kan hanya zuwa gona a yankin karamar hukumar Goronyo, in ji wani basaraken yankin mai suna Sarkin Daji.

    "Masuntanmu sun zaƙulo gawarwaki sannan har yanzu ana ci gaba da nema," a cewar Nasiru Gurau, wani mazaunin yankin.

    Najeriya na fama da yawaitar kifewar kwale-kwale, inda ake gudanar da irin wannan sufuri cikin yanayi mai hatsari.

  4. Za a fara gwajin allurar rigakafin cutar Ebola a Kwango

    An tura alluran rigakafi dubu saba’in zuwa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango domin taimakawa wajen dakile ɓarkewar cutar Ebola.

    Ƙungiyar ƙasa da ƙasa da ke kula da samar da alluran rigakafi, ta ce kunshin ya haɗa da allurai dubu hamsin da za a bai wa ma’aikatan jinya da ke kan gaba wajen yaƙi da wannan annobar, wadda ake ganin ita ce mafi saurin yaɗuwa a tarihin cutar.

    Sauran alluran kuma za a yi amfani da su ne domin yin gwaji.

    An amince da wannan rigakafi ne domin kare mutane daga nau’in Ebola na Zaire, wanda shi aka fi samu, sai dai har yanzu ba a tabbatar ko yana da tasiri kan nau’in Bundibugyo ba, wanda ake dangantawa da ɓarkewar cutar ta yanzu.

    Nan gaba kadan za a soma yin gwajin allurar rigakafi biyu da aka haɗa domin nau'in Bundibugyo a kan mutane karon farko.

  5. An yi wa samari da ƴanmata bulala ɗari-ɗari bisa laifin zina

    An yi wa wasu maza biyu da ƴanmata biyu bulala a bainar jama'a bayan kama su da laifin yin zina a yankin Aceh na ƙasar Indonesia.

    Kowannensu an masa bulala 100.

    Akwai kuma wasu matasan 7 waɗanda aka yi wa bulalar da ba ta kai 100 ba bisa aikata laifukan da ba su kai girman zina ba, wanda ya ƙunshi keɓewa, sai kuma wani mutum ɗaya da aka yi wa bulala 20 bisa laifin shan barasa.

    Aceh ne lardi ɗaya tilo a Indonesia da ke zartar da hukuncin shari'ar Musulunci sau da ƙafa.

    Kasar wadda take a kudu maso gabashin nahiyar Asiya, ita ce mafi yawan al'ummar Musulmi a duniya.

  6. Najeriya za ta daina hukunta waɗanda suka yi yunƙurin kashe kansu

    Gwamnatin Najeriya ta amince da shirin daina hukunta mutanen da suka yi yunƙurin kashe kansu.

    Wannan sauyi wani muhimmin ci gaba ne a ƙoƙarin da ake yi na kawo sauyi a harkar kula da lafiyar ƙwaƙwalwa a Najeriya, inda a yanzu haka ake iya yanke wa wanda aka kama da yunƙurin kashe kansa hukuncin ɗauri da zai iya kai na tsawon shekara ɗaya.

    A wata ganawa da manema labarai, ministan lafiya na Najeriya ya ce yunƙurin kashe kai babbar matsala ce a Najeriya, inda ake samun kimanin mutum 300,000 da ke yunƙurin kashe kansu a ƙasar cikin shekara guda, kuma ana samun kimanin mutum 7,000 da ke samun nasarar kashe kan nasu.

    Farfesa Ali Pate ya ce a yanzu za a maye hukuncin da ake yankewa, da kula da lafiya, nuna kulawa da bayar da taimako.

    Masu yunƙurin kashe kai na fuskantar tsangwama a Najeriya sannan ana fama da mummunan ƙarancin masu kula da lafiya ƙwaƙwalwa.

    Ƙungiyar likitocin lafiyar ƙwaƙwalwa ta Najeriya ta ce akwai ƙasa da likitan lafiyar ƙwaƙwalwa ɗaya da ake sa ran zai kula da masu lalura sama da 200.

  7. An ƙwace shari'o'i daga hannun alƙalin da ke ta yanke wa mutane hukuncin kisa

    Hukumomi a arewacin ƙasar Indiya sun ƙwace shari'o'i kimanin 100 daga wani alƙali bayan ya yanke wa mutum daban-daban har 22 hukuncin kisa cikin kwana ɗaya.

    Gwamnatin jihar Uttar Pradesh ta ƙwace shari'o'in daga mai shari'a Ravi Kumar Diwakar wanda ke jagorantar kotun bayan da ƙungiyar lauyoyin yankin ta nuna tababa game da shi.

    A ƙarƙashin dokokin Indiya, za a iya zartar da hukuncin kisa ne kawai idan manyan kotunan jiha ko kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin.

    Har yanzu aiwatar da hukuncin kisa halas ne a dokokin Indiya, sai dai Kotun Ƙolin ƙasar ta ce za a iya zartar da hukuncin ne kawai idan abin ya munana.

    An aiwatar da hukuncin kisa na ƙarshe a baya-bayan nan a Indiya ne a shekarar 2020 lokacin da aka rataye wasu maza huɗu waɗanda aka kama da laifin fyaɗe da kisan wata mata a birnin Delhi.

  8. Zan mayar da tallafin man fetur idan na ci zaɓe - Atiku

    Ɗan takarar shugabancin Najeriya na babbar jam'iyyar hamayya ta ADC a zaɓen ƙasar mai zuwa, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa zai mayar da tallafin man fetur a ƙasar idan ya hau kan mulki a shekarar ta 2027.

    Cire tallafin man fetur na daga cikin manyan matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka waɗanda suka kawo gagarumin sauyi a tattalin arziƙin ƙasar.

    A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Tinubu ya sanar a cikin jawabinsa na karɓar mulki cewa "tallafi ya ƙare", lamarin da ya taka rawa wajen tashin farashin litar man fetur da hauhawar farashi a kusan kowane fanni na ƙasar.

    Sai dai an yi ta cece-ku-ce kan rashin ganin alfanun hakan bayan da aka samu ƙarin tsadar rayuwa a ƙasar.

    A tattaunawar da ya yi da kafafen yaɗa labarai a jiya Laraba, Atiku ya ce cire tallafin bai yi amfani ba kasancewar "ba a ga abin da aka yi da kuɗin ba".

    "Ina kuɗin suke? Ya kamata a ce an yi amfani da su wajen maganin talauci da rashin zuwa makaranta, da sauran su".

    A lokacin da aka tambaye shi ko zai mayar da tallafin man fetur ɗin idan ya ci zaɓe a 2027, sai ya ce: "Zan mayar, kuma duk wani wanda ya saci kudin zai dawo da su".

    Gabanin babban zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya taɓa yin alƙawarin cewa zai sayar da matatun man fetur na ƙasar

  9. Sheikh Bashir zai jagoranci majalisar hada-hadar banki babu kuɗin ruwa ta Ghana

    Babban Bankin Ghana ya ƙaddamar da Majalisar Bayar da Shawarwari kan harkokin banki da babu kuɗin ruwa ta ƙasar (NIFAC) domin taimakawa wajen tsarawa da samarwa da kuma sanya ido kan harkokin banki da sauran hada-hadar kuɗi da babu kuɗin ruwa a ƙasar.

    A wani saƙo da bankin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Majalisar za ta riƙa bai wa Babban Bankin shawarwari kan tafiyarwa da lura da kuma sanya ido kan bankuna da ba su amfani da tsarin riba.

    Lokacin da ya ƙaddamar da majalisar cikin wannan mako, gwamnan babban bankin Ghana Dr Johnson Asiama ya jaddada muhimmancin samar da tsarin tafiyarwa mai kyawu, kare masu amfani da tsarin da kuma ƙoƙarin ganin mutane sun samu kwanciyar hankali da tsarin.

    Sanannen malamain addinin Musulunci na Najeriya Farfesa Bashir Aliyu ne zai jagoranci majalisar.

    Sheikh Bashir farfesa ne a Jami'ar Bayero da ke Kano kuma shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Shari'a a Najeriya (SCSN).

    Sauran mambobin majalisar su ne Dr. Yussuf Adany Al-Badani, da Dr. George Baah-Danquah, da Adishetu Hamidu Naabo da kuma Samuel Gameli Gadzo.

  10. Iran ta yi watsi da 'barazanar' Amurka

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Aragchi ya bayyana barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na ƙaƙaba ƙarin takunkuman tattalin arziƙi kan ƙasar a matsayin ci gaba da fito da sabbin shawarwarin da ba za su je ko ina ba.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X, ya bayyana cewa: “Abin da aka bayyana da ranar ƙarshe ta tattalin arziƙi wani yunƙuri ne na kawar da hankula daga abin da ke faruwa; kamar tarin bashi da kuma hauhwar kuɗin ruwa na bashi da Amurka ke fama da shi”.

    Ya ƙara da cewa “dagewa wajen kawo tsare-tsare waɗanda ba za su yi nasara ba, ba za su haifar da komai ba sai ƙarin rashin nasara da kuma janyo wa kansa ƙiyayya daga Iraniyawa.

    “Ta’addancin Amurka barazana ce ga tattalin arziƙin duniya da ƴancin cin gashin kai na ƙasashe a faɗin duniya,” a cewar saƙon.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta, shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai ƙaƙaba “matakin tattalin arziki mafi tsanani da aka taɓa gani a tarihi a kan kowace ƙasa”.

    Bai yi ƙarin bayan kan saƙon nasa ba sai dai ya ƙara da cewa “wannan zai zama ware ƙasar ɗungurungum a harkar tattalin arziƙi”.

  11. An ta haramta haƙar ma'adanai a inda zaftarewar ƙasa ta kashe mutum 107

    Gwamnatin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta dakatar da duk wasu ayyukan haƙar ma'adanai a yankin Zamboi, inda zaftarewar ƙasa ta kashe aƙalla mutum 107.

    Ministan haƙar ma'adanai da nazarin ƙasa da duwatsu na ƙasar Rufin Benam ne ya sanar da haka bayan ya ziyarci wurin da lamarin ya faru a ranar Laraba.

    Hukumomi ba su bayyana a hukumance adadin mutanen da suka salwanta ba sanadiyyar lamarin.

    Wani jami'i a garin Garou-Boulai na kan iyaka ya shaida wa BBC cewa an zaƙulo aƙalla gawarwaki 107 daga cikin ƙasa.

    A ɓangare ɗaya ƙasar Kamaru mai maƙwaftaka ta ce lamarin ya rutsa da ƴan ƙasarta, inda gwamnan yankin gabashin ƙasar ya ce ƴan Kamaru aƙalla uku ne suka rasa rayukansu.

  12. Ƙarin ƴan Najeriya 83 sun koma gida daga Afirka ta Kudu

    Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce ƴan ƙasar 83 sun isa birnin Legas daga Johannesburg a yammacin jiya Laraba, a ci gaba da kwashe ƴan ƙasashen waje daga Afirka ta Kudu sanadiyyar zanga-zangar ƙyamar baƙi.

    Ma’aikatar harkokin wajen ta ce wasu mutane ne suka ɗauki nauyin kwaso mutanen na wannan karo bayan da gwamnatin ƙasar ta rufe ƙofar kwaso ƴan ƙasar da ke zaune a Afirka ta Kudun a cikin watan Yuni.

    Gwamnati ta ɗauki nauyin mayar da ƴan ƙasar gida sau biyar tun bayan ƙazancewar zanga-zangar ƙyamar baƙi a ƙasar ta Kudancin Afirka, lamarin da ya tursasa wa ƙasashe da dama kwashe mutanensu.

    Wasu ƙungiyoyi ne a ƙasar suka tsananta matsin-lambba kan duk wasu baƙi, wadanda ba su da halastattun takardun zama su fice daga ƙasar kafin 30 ga watan Satumba.

    Wannan lamari ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin ƙasar da sauran ƙasashen nahiyar Afirka.

    Sai dai gwamnatin ƙasar ta yi tir da hare-haren da ake kai wa baƙin, inda ta ce tana ƙara ƙaimi wajen tabbatar da aiki da dokokin shige da fice, da kuma magance kwarar baƙin haure.

    Afrka ta Kudu ta ce ya zuwa yanzu an kwashe baƙi marasa takardu sama da 80,000 daga ƙasar.

  13. Harin Rasha ya kashe mutum 13 a babban birnin Ukraine

    Hukumomin Ukraine sun ce harin makami mai linzami da Rasha ta kai Kyiv, babban birnin ƙasar ya kashe aƙalla mutum 13 tare da jikkata sama da 40.

    Rahotanni sun ce makamai masu linzami 20 ne na Rasha ta yi amfani da su wajen kai harin kan gidaje da wuraren ajiye kaya da wani asibitin yara.

    Yayin da hukumomin ke ci gaba da yin ƙoƙarin ganin an mayar da wutar lantarki a wasu sassan birnin inda wasu mutane da dama suka maƙale a wurin da suke fakewa a birnin.

  14. Zan ƙaƙaba takunkumai kan Iran da masu taimaka mata - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai kaddamar da sabbin takunkuman tattalin arziki kan Iran da duk wata ƙasa da ke taimaka mata ko yin kasuwanci da ita.

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Trump ya ce zai dauki matakin ne saboda Iran ta kasa cimma yarjejeniya da Amurka.

    Sai dai bai bayar da cikakken bayani kan matakan ko sunan wata ƙasa da abin zai shafa ba.

    A ranar Litinin ne yarjejeiyar tsagaita wuta ta kwana 60 ta kare ba tare da wata alama da ke nuna za a kawo ƙarshen yaƙin da ake fafatwa tsakanin Iran da Amurkar ba.

  15. Bashin da ake bin Amurka ya zarce dala tiriliyan 40

    Bashin da ake bin Amurka ya zarce dala tiriliyan arba'in, adadi mafi girma na bashin da aka taɓa bin ƙasar.

    Bashin ya nunninka a cikin shekara 10 yayin da ya riƙa ƙaruwa da dala tiriliyan ɗaya duk wata biyar tun daga shekarar 2020.

    Ƙaruwar kashe kudaden gwamnati ciki har da yaƙi da kuma rage haraji na daga cikin dalilan da suka haifar da haka.

    Sai dai shugaba Trump ya ɗora alhakin hakan kan karin kudin ruwa. Ya ce idan ƙasarmu na samun nasara da ci gaba ya kamata kudin ruwa suyi ƙasa saboda hakan zai ƙara tabbatar da munada jajirtacciyar ƙasa.

    Sai dai masana sun fara nuna damuwa kan yadda bashin ke ƙaruwa cikin sauri.

  16. Barka da warhaka!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis a wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku muhimman labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya, maƙwaftanta da kuma sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook, instagram da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.