Hotunan Afirka na mako 23-29 Agustan 2019: Tsalle-tsalle da sa albarka

An wallafa

Wasu zababbun hotunan Afirka da aka tattaro daga fadin nahiyar a wannan makon.

Alkafira
Bayanan hoto, Wannan yarinyar tana yin alkafira a birnin Alexandra na Afirka Ta Kudu bayan ta tashi daga makaranta ranar Talata...
Trampoline
Bayanan hoto, Fitacciyar mai tsalle-tsalle tana nuna wa jama'a yadda ake tsalle da malkwadar jiki
Masu kokawa
Bayanan hoto, A ranar Asabar a birnin Johannesburg, 'yan wasan kokawa sun yi wani wasa don masoyansu su gani...
Wrestlers
Bayanan hoto, Kungiyar wasan dambe ta Afirka Ta Kudu da ake kira South African Pro Wrestling
Iman
Bayanan hoto, Iman - wata jaruma 'yar kasar Somaliya a bikin fina-finan Venice International Film Festival da aka gudanar a Italiya ranar Laraba...
Presentational white space
Candice Swanepoel
Bayanan hoto, Yadda fitacciyar jarumar kasar Afirka ta Kudu Candice Swanepoel ta ke daukar hoto a bayan wani ruwa
D'banj
Bayanan hoto, Shahararren mawakin Afrobeats a Najeriya, D'banj ya mamaye manyan labaran kwalejin Brixton Academy da ke birnin London a ranar Lahadi. Kafin nan ya shaida wa BBC cewa mai dakinsa za ta sake haifa masa da shekara daya bayan mutuwar dansu.
Ivory Coast
Bayanan hoto, Wani bangare na mutanen da suka bikin "Fatchue" ranar Alhamis a Abidjan babban birnin Ivory Coast...
Ivory Coast
Bayanan hoto, Ana gudanar da bikin ne domin shirya kananan yara fara shirin zaman shugabannin gobe
Bobi Wine
Bayanan hoto, Limaman coci ne ke yi wa mawaki kuma dan siyasa na kasar Uganda, Bobi Wine ranar Lahadi a lokacin wani gangamin kamfe na neman kuri'ar jama'a a takararsa da Yoweri Museveni
Ethiopia
Bayanan hoto, Wani kwarangwal din kai mai kama da na mutum mai darajar kudi har dala miliyan 3.8 da aka gano a Ethiopia wanda kuma a baje-kolinsa a
Kenya
Bayanan hoto, A Kenya nan inda jami'an tsaron daji rike da makamai ke yi wa wasu karkanda irinsu da suka rage rakiya domin samun wurin da za su tsuguna su kyankyashe kwayayensu, ranar Juma'a.
Liberia
Bayanan hoto, Dalibai na faretin bikin tuna wa da ranar tutar kasar Laberiya a birnin Monrovia ranar Asabar.
Slave trade
Bayanan hoto, Yadda ake bikin tuna wa da mutanen da suka mutu a ruwa lokacin cinikin bayi a Amurka, a Virginia.

An tattaro hotunan ne daga Reuters da EPA da Getty Images da AFP da Redferns da kuma SOPA Images.