Yadda Boko Haram ke bautar da mutane a yankunan da take iko da su a Najeriya

Asalin hoton, BOKO HARAM
Yanke tallafin jin-ƙai da Amurka ta yi, ya jefa dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu cikin matsananciyar yunwa, lamarin da ke tilasta wa wasu komawa yankunan da mayaƙan ke riƙe da su domin neman abin da za su ci.
A duk wata, wani masunci mai suna Musa mai shekara 46 daga garin Doron Baga da ke jihar Borno, kan yi tafiya tare da wasu masunta da dama zuwa tsibiran da ke ƙarƙashin ikon mayakan Boko Haram domin kamun kifi.
Tafiya ce ba mai sauƙi ba, amma Musa ya ce ba shi da wani zaɓi idan yana son ciyar da matansa biyu da yaransa tara.
Bayan shafe sama da shekaru goma yana dogaro da tallafin abinci daga ƙungiyoyin agaji, rayuwarsa ta sauya bayan da Amurka ta rage tallafin kuɗin da take bai wa ƙungiyoyin jinƙai a shekarar da ta gabata.
Rage tallafin ya shafi ayyukan agaji da ke taimaka wa dubban mutanen da rikicin Boko Haram na tsawon shekara 17 ya raba da muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya.
Binciken kamfanin dillancin labarai na AFP, wanda ya tattauna da manoma, da ƙungiyoyin agaji da majiyoyin tsaro, ya nuna cewa yunwa ta sa wasu masunta shiga hulɗa da mayakan Boko Haram domin samun abin da za su rayu da shi.
'Ba mu da wani zaɓi'
Musa ya shaida wa AFP ta wayar tarho cewa shi da sauran masunta kan biya kuɗin haraji kafin mayakan Boko Haram su ɗauke su a kan manyan kwale-kwale masu inji daga gabar tafkin Chadi kusa da Baga zuwa tsibiran Shuwa da Dan-Katsina.
Waɗannan tsibirai na da yawan kifaye, lamarin da ke jan hankalin masunta daga yankunan da ke kewaye.
"Da zarar mun shiga yankinsu, muna zama kamar kayansu ne, kuma muna yin abin da suka ce saboda ba mu da wani zaɓi," in ji Musa, wanda ya nemi a yi amfani da sunansa na farko kawai saboda dalilan tsaro.
Kamar dubban sauran mutanen da rikicin ya raba da muhallansu, Musa ya taɓa zama a wani sansanin ƴan gudun hijira na wucin gadi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Asalin hoton, Getty Images
Yadda yunwa ke ƙara ƙarfin Boko Haram
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masuntan da ke zuwa yankunan da Boko Haram ke iko da su ba kamun kifi kawai suke yi ba.
A cewar rahoton, wasu kan yi wa mayakan ayyukan kai musu kayayyaki tare da sanar da su halin da ake ciki a yankunan da ba sa ƙarƙashin ikonsu.
Wannan na sanya masuntan cikin haɗarin faɗawa tsakanin mayakan da jami'an tsaro, domin ɓangarorin biyu kan zargi wasu al'ummomi da taimaka wa abokan gabansu.
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ta ce rage tallafin agaji da kuma ƙaruwar rashin tsaro sun jefa wasu yankunan arewa maso gabashin Najeriya cikin matsanancin yunwa da ba a gani ba tsawon kusan shekaru goma.
A jihar Borno kaɗai, adadin mutanen da ke fuskantar matsanancin ƙarancin abinci ya haura miliyan uku daga miliyan 1.6, a cewar hukumar.
WFP ta ƙara da cewa sama da mutane miliyan 17 a jihohi tara da rikici ya shafa a arewacin Najeriya na fuskantar matsalar ƙarancin abinci mai tsanani, matakin gaggawa ko kuma yunwa mai tsananin muni.
Arjun Jain, wakilin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) a Najeriya, ya shaida wa AFP cewa:
"Kuɗin tallafin da ake da su sun yi matuƙar raguwa."
Ya ce ƙungiyoyin agaji na samun kuɗin da bai kai abin da ake buƙata ba, yayin da wasu ma suka tilasta rufe ayyukansu.
A cewarsa, raguwar tallafin ta zo daidai da tabarbarewar yanayin tsaro a wasu yankuna.
Yadda Boko Haram ke samun kuɗi a tafkin Chadi

Asalin hoton, Getty Images
Tafkin Chadi, wanda ya haɗa iyakokin Najeriya, da Nijar, da Kamaru da Chadi, ya kasance ɗaya daga cikin manyan wuraren da Boko Haram ke da tasiri.
Ƙungiyar ta mayar da wasu tsibirai da ke cikin tafkin mafaka, inda masunta, da manoma, da makiyaya da masu sare itatuwa ke biyan kuɗin haraji domin gudanar da ayyukansu.
Rahoton ya ce wannan tsarin karɓar haraji ya bai wa Boko Haram damar samun kuɗaɗen shiga da kuma ƙara ƙarfin ɗaukar sababbin mambobi.
Hakan ya bambanta da ƙungiyar ISWAP, wadda ke da alaƙa da ƙungiyar ISWAP, kuma ita ma ke karɓar haraji daga makiyaya, masunta da manoma.
ISWAP ta rasa yawancin wuraren da take iko da su a tafkin Chadi bayan fafatawa da Boko Haram.
Wata majiya mai masaniya kan ayyukan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ta shaida wa AFP cewa wasu shugabannin ISWAP sun gudanar da taro a sansanoninsu tare da mayakan jihadi shida daga ƙasashen Maghreb, ciki har da Morocco.
A cewarta, taron ya mayar da hankali kan hanyoyin ƙara kuɗaɗen shiga da kuma dakile ficewar mayaka daga ƙungiyar.
A gefe guda, Boko Haram na samun kuɗi ta hanyoyi daban-daban, ciki har da harajin da take karɓa daga masunta, makiyaya, da manoma da masu sare itatuwa, da kuma kasuwancin fatun dabbobi, ƙumushin Larabawa da kuɗin fansar mutanen da take garkuwa da su.
Rahoton ya ambaci bayanan kamfanin bincike na SBM Intelligence da ke Legas, wanda ya ce ƙungiyoyin masu aikata laifuka sun samu kusan dala miliyan shida daga kuɗin fansa tsakanin Yulin 2025 da Yunin 2026.
A cewar kamfanin, kashi 90 cikin 100 na kuɗin ya tafi ga Boko Haram, bayan sace ɗalibai 260 daga makarantar St Mary's Catholic School a jihar Neja da kuma mutane sama da 400 a Ngoshe, jihar Borno.
Gwamnatin Najeriya ta musanta cewa ta biya kuɗin fansar.
Babakura Kolo, wani jagoran mayaƙan sa-kai da ke taimaka wa sojojin Najeriya wajen yaƙar Boko Haram, ya ce ƙungiyar na da kuɗaɗen da take amfani da su wajen jawo hankalin matasan da ke cikin mawuyacin hali.
'Matasa masu ƙoshin lafiya'

Asalin hoton, Getty Images
Kuɗaɗen da Boko Haram ke samu daga karɓar haraji a yankin tafkin Chadi na taimaka mata wajen ɗaukar ƙarin matasa da ke neman mafita daga matsin rayuwa.
Wata majiya mai masaniya kan ayyukan ƙungiyar ta shaida wa AFP cewa a watan Fabrairu, Boko Haram ta ƙaddamar da shirin ɗaukar mayaka 1,500 a wani daji da ke tsakanin jihohin Yobe da Borno, kusa da iyakar Nijar.
Majiyar ta ce cikin ƙasa da mako guda, sama da mutane 5,000 ne suka fito neman shiga ƙungiyar, wasu ma daga nesa kamar ƙasar Chadi.
Sani Abdullahi da Babakura Kolo sun tabbatar da cewa ana samun matasa da dama da ke sha'awar shiga ƙungiyar.
"Matasa ne dukkansu, masu ƙoshin lafiya," in ji Kolo.
Sai dai Abdulaziz Mala na Swift Relief ya yi gargaɗin cewa hulɗa da Boko Haram na iya jefa rayuwar masunta cikin haɗari matuƙa.
Ya ce masuntan da ke aiki a yankunan na iya fuskantar harin sojoji bisa kuskuren ɗaukar su a matsayin mayakan Boko Haram.
A watan Mayu, an kashe masunta ƴan Najeriya da dama lokacin da jiragen yaƙin Chadi suka kai hari a tsibirin Shuwa, a cewar ƙungiyar masunta da mayaƙan sa-kai.
Harin ya biyo bayan hare-haren da mayakan suka kai, inda suka kashe kusan sojojin Chadi 30, ciki har da manyan hafsoshi biyu.
Sani Abdullahi ya ce da an ci gaba da bai wa mutanen tallafin abinci, da yawa daga cikin masuntan ba za su shiga irin wannan haɗari ba.
"Da mutane na samun tallafin abinci, me zai sa su shiga wannan haɗari su jefa rayukansu cikin barazana?" in ji shi.



























