Gwamnatin jihar Katsina ta dakatar da Sarkin Daura

Sarkin Daura
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, daga dukkan ayyukan masarautar da wasu tafiye-tafiyen biyo bayan zargin cin zarafin da wata baƙuwa mai yawon buɗe ido ta yi a kansa.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu na jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar 24 ga Nuwamba, 2026, gwamnatin ta ce ta kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa Sarkin.

Sanarwar ta ce Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya bayar da umarnin kafa kwamitin domin gudanar da bincike kan lamarin tare da ba gwamnati shawarwari kan matakin da ya kamata ta ɗauka.

Gwamnatin ta bayyana damuwa kan zargin cin zarafin mata da ake yi wa Sarkin, wanda ya bazu a kafafen sada zumunta.

Ta kuma tabbatar wa al'umma cewa za ta tabbatar da an yi adalci, tare da aiwatar da dukkan shawarwarin da sakamakon binciken kwamitin ya fito da su.

Gwamnatin ta buƙaci jama'a su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bin doka da oda, tare da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Tun gayan zargin muhawara ta kaure bayan ɓullar wani bidiyo da a cikinsa ake zargin cewa ɗaya daga cikin sarakuna masu daraja ne na ƙasar Hausa tare da wata baturiya ƴar yawon buɗe ido.

Abin da muka sani kan bidiyon baturiya da 'Sarkin Daura'

Xxx

A cikin bidiyon an ga wata baturiya a cikin fada irin ta masarautun ƙasar Hausa tare da wani da ake kyautata zaton Sarkin Daura ne Alhaji Faruk Umar Faruk.

A cikin bidiyon an ji yadda matar, wadda ta bayyana kanta da suna Beduina a shafin instagram ke cewa : "ɗaya daga cikin abin da ya burge ni shi ne jin tarihin Daura, kasancewar a baya mata ne suke mulkin Daura".

A ƙarƙashin bidiyon da ta wallafa, matar ta ce ta naɗi bidiyon ne ta amfani da tabarau ɗin da take sanye da shi mai kyamarar ɗaukan hoto, wanda ake kira Meta glasses a Ingilishi.

Ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a cikin wannan wata na Nuwamba sa'ilin da take Najeriya.

Ta ƙara da cewa ba ta wallafa bidiyon ba har sai bayan da ta bar Najeriya domin gudun kada a cutar da ita.

Wannan lamari ya haifar da muhawara a fili da kuma shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke ta kiraye-kirayen a yi bincike kan lamarin.

Ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bayyana lamarin a matsayin "abin damuwa".

Sannan ƙungiyar ta buƙaci da a gaggauta yin bincike.

A arewacin Najeriya ana yi wa sarakuna kallon martaba da mutunci da kuma girmamawa, a matsayinsu na ginshiƙan adana al'ada, sannan suna da matuƙar faɗa-a-ji a cikin al'umma.

Daura gari ne mai matuƙar tarihi a ƙasar Hausa.

Wace ce Beduinqa?

Bayanan da ta wallafa a shafinta na Instagram sun nuna cewa Beduinqa wata baturiya ce ƴar ƙasar Poland wadda ta ƙudiri aniyar karaɗe ƙasashen duniya 197.

Ta bayyana kanta a matsayin mai son tallafa wa al'umma sannan tana sha'awar ninƙaya zuwa ƙasan ruwa da kuma yawon duniya.

Daga hotunan da ta wallafa, ta ziyarci ƙasashe daban-daban a duniya, daga nahiyar Turai, zuwa Amurka ta Arewa da Amurka ta Kudu da Australia da Afirka da ma wasu ƙasashen duniya da dama.

Hotunan sun kuma nuna yadda ta yi yawace-yawace a kudanci da arewacin Najeriya har ma da ziyartar fadojin sarakunan gargajiya.

Hotuna sun nuna yadda ta halarci bukukuwa da gidajen tarihi a jihar Kano da ke Najeriya tare da ɗaukan hoto da al'ummar Hausawa.

Ta ɗauki hoto da sarkin Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya da kuma na Kagara a jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.

Birnin Daura

Garin yana cikin jihar Katsina ne a arewa maso yammacin Najeriya, kuma ya yi iyaka da Jamahuriyar Nijar ta wajen Damagaram daga arewa.

Babu yadda za a yi tarihin kasar Hausa ya kammala ba tare da an sako na Daura a ciki ba.

Rubuce-rubucen masana tarihi da dama sun nuna cewa Daura ita ce tushen Hausa da Hausawa, duk da cewa dai akwai masana da dama da ba su yarda da wannan hasashe ba.

Tana daga cikin manyan masarautun kasar Hausa da aka fi sani da Hausa Bakwai.

Daura na da hamshakiyar masarauta wacce sarakuna daban-daban suka mulke ta tun daga zamanin Sarauniya Daurama har zuwa yau. An kuma san garin da tarihin kofofi da ganuwar gari da yawancin garuruwan kasar Hausa ke da shi.

Tarihi ya nuna cewa Daurama ita ce take sarauta a lokacin da Bayajidda ya iso garin ya kuma kashe macijiya sarki, sai ta aure shi saboda bajintarsa.

Daurama ita ce uwarsu Bawo wato ita ce uwar sarakunan Hausa Bakwai na Biram da Kano da Katsina da Zazzau da Gobir da kuma Rano.

Hakika duk wanda zai karanci tarihin kasar Hausa dole zai ci karo da na Sarauniya Daurama.