Yadda za a gudanar da zaɓen gwaji a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta ce za ta gudanar da wani zaɓen gwaji domin tantance ingancin na'urar BVAS da kuma gano matsalolin da ka iya tasowa kafin babban zaɓen shekarar 2027.
Mai magana da yawun hukumar, Zainab Aminu Abubakar, ta ce manufar gwajin ita ce gano duk wata matsala da ka iya shafar aikin na'urar domin a samu damar gyara ta kafin lokacin zaɓe.
Na'urar Bimodal Voter Accreditation System (BVAS) ita ce INEC ke amfani da ita wajen tantance masu kaɗa ƙuri'a da kuma ɗaukar hoton sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓe domin ɗora su a intenet.
A cewarta, za a gudanar da gwajin ne a rumfunan zaɓe biyu a kowace gundumar zaɓe daga cikin gundumomi 8,838 da ke faɗin ƙasar.
Zainab ta bayyana cewa hukumar ta wallafa lambobin rumfunan zaɓen da aka zaɓa domin gwajin a shafinta na yanar gizo, tare da buƙatar masu kaɗa ƙuri'ar da abin ya shafa su duba ko rumfarsu tana cikin waɗanda aka zaɓa.
INEC ta kuma yi kira ga masu kaɗa ƙuri'ar da rumfunansu suka shiga cikin gwajin da su fito yau Asabar tare da katin zaɓensu.
Zainab Aminu Abubakar ta ce dukkan masu kaɗa ƙuri'ar da suka yi rajista a rumfunan da aka zaɓa za su iya shiga cikin gwajin.
'Ba za a yi amfani da sunayen jam'iyyu ba'
Hukumar ta ce ba za a yi amfani da takardar zaɓe mai ɗauke da sunayen jam'iyyun siyasa, tambarinsu ko sunayen ƴan takara ba, kasancewar gwaji ne.
Maimakon haka, za a yi amfani da wata takarda ta musamman da aka tsara domin bai wa masu kaɗa ƙuri'a damar zaɓar abubuwan da aka gabatar musu, da nufin gwada yadda na'urar ke aiki.
Ta ƙara da cewa manufar ita ce a tantance yadda na'urar BVAS ke gudanar da aikin tantance masu zaɓe da kuma yadda take ɗaukar hoton takardar zaɓe tare da ɗora shi a yanar gizo.
A cewar hukumar, za a gudanar da gwajin ne daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana.
INEC ta sake yin kira ga masu kaɗa ƙuri'a da rumfunansu suka shiga cikin shirin da su fito da katin zaɓensu domin ba da gudunmawa wajen gwada tsarin kafin babban zaɓen 2027.


























