Fitattun ƴan gwagwarmar asali na arewacin Najeriya

Gwagwarmaya
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Najeriya ta samu ƴancin kai daga hannun Turawan mulkin mallaka na Burtaniya a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, bayan gumurzu da fafutuka na tsawon shekaru da jagororin siyasa da masu kishin ƙasa suka yi domin ganin an bai wa 'yan Najeriya damar tafiyar da al'amuransu da kansu.

Wannan nasara ba ta zo cikin sauƙi ba, domin ta biyo bayan tattaunawa, gangami, wayar da kai da kuma matsin lamba da aka riƙa yi wa gwamnatin mulkin mallaka.

A arewacin Najeriya kuwa, an samu wasu fitattun ƴan kishin ƙasa da suka sadaukar da lokacinsu da ƙarfinsu wajen wayar da kan al'umma da kuma fafutukar tabbatar da cewa Najeriya ta samu makomar Najeriya.

Ta hanyar jagoranci, ilimi da siyasa, waɗannan mutane sun taimaka wajen haɗa kan jama'a da kuma kare muradun yankinsu a matakin ƙasa.

Wasu daga cikin waɗannan gwarazan sun yi fice wajen kafa ƙungiyoyi, shiga tarurrukan tsarin mulki da kuma tattauna batutuwan da suka shafi miƙa mulki ga ƴan Najeriya.

Duk da cewa gudunmawar wasu daga cikinsu ba ta samu cikakken haske a rubuce-rubucen tarihi ba, tasirinsu ya kasance mai zurfi wajen samar da yanayin da ya ba Najeriya damar samun ƴanci.

A daidai lokacin da ake tattaunawa kan makomar gwagwarmaya musamman a arewacin Najeriya, BBC ta yi waiwaye tare da rairayo wasu fitattun ƴan gwagwarmaya da suka taka rawa wajen ciyar da yankin gaba.

Malam Sa'adu Zungur (1914-1958)

Zungur

Malam Sa'adu Zungur na ɗaya daga cikin matasan da suka yi adawa mai ƙarfi ga Turawan mulkin mallaka, wanda aka haifa a shekarar 1914, sannan ya rasu a shekarar 1958, shekara biyu kafin Najeriya ta samu ƴancin kai.

Tare da Abubakar Tafawa Ɓalewa da Aminu Kano da wasu gogaggun ƴan arewacin Najeriya sun kafa ƙungiyar Bauchi General Improvement Union, BGIU, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka zama jam'iyyun siyasa na farko a arewacin ƙasar da Bauchi Discussion Circle.

Malam Sa'adu Zungur ya yi amfani da ƙungiyoyin biyu wurin bayyana ra'ayoyinsa masu kaushi.

A shekarar 1946 ne Nnamdi Azikiwe ya aike wa da Zungur gayyatar kasancewa da jaridarsa ta West African Pilot wadda aka kafa domin gwagwarmayar ƙwato ƴanci daga hannun Turawan mulkin mallaka.

Arewa Jumhuniya ko Mulkiya littafin waƙoƙi ne da ya rubuta a shekarar 1950.

Malam Aminu Kano (1920 — 1983)

Aminu Kano
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Malam Aminu Kano wanda ya kafa fitacciyar jam'iyyar NEPU, ya kasance malamin makaranta ne a 1940, bayan kammala Kwalejin Kaduna, inda kuma aikin koyarwar ya kai shi zama a birane kamar Bauchi da Zaria da ma taƙaitaccen lokaci a kudancin Najeriya.

A 1942 ne ra'ayinsa na riƙau kan sarakuna da rajin kare Talakawa ya fara bayyana. A lokacin ne ya fara rubuce-rubuce a jaridu da mujallu kamar Gaskiya Ta Fi Kwabo da West African Pilot ta Nnamdi Azikiwe.

Bayanai sun nuna cewa haɗuwar Malam Aminu Kano da Malam Sa'adu Zungur a kwalejin Kaduna College ce ta ƙara masa ƙaimin samun ra'ayin mazan jiya.

A shekarar 1948 ne Malam Aminu Kano ya ja gorar wasu ƴan arewacin ƙasar masu irin ra'ayinsa suka kafa Jam'iyyar Mutanen Arewa ko kuma Northern Peoples Congress, NPC, kuma an ƙaddamar da ita a 1949.

To sai dai kuma Malam Aminu ya ajiye muƙaminsa a jam'iyyar a 1950, inda kuma ya kafa Northern Progressive Union, NEPU da manufar ƙwata wa Talakawa ƴanci.

Hajiya Gambo Sawaba (1933-2001)

Gambo Sawaba

An haifi Gambo Sawaba ranar 15 Fabrairun 1933 a jihar Neja sai dai ta yi rayuwarta a garin Zariya da ke jihar Kaduna, a cewar Dokta Shu'aibu Aliyu.

Ta fara karatu a makarantar furamare ta NA, kodayake karatun nata ya samu tsaiko bayan rasuwar mahaifinta.

''Duk da cewa ta yi aure tun tana ƙarama, (shekara13), bayan rasuwar iyayenta, hakan bai sanyaya mata gwiwa a fannin gwagwarmaya ba''.

Tsohon shugaban gidan tarihin ya ce an tsare Hajiya Gambo Sawaba a kurkuku aƙalla sau 16 saboda gwagwarmayarta na neman yanci.

''Ta kasance ƙusa a siyasar arewacin Najeriya, inda ta kai matsayin mataimakiyar shugaban jam'iyyar GNPP, kafin daga baya ta koma jam'iyyar NEPU inda ta zama shugabar mata na jam'iyyar''.

Gambo Sawaba ta riƙa sukar manufofin turawan mulkin mallaka a tarukan yaƙin neman zaɓen NEPU.

Ta kasance ɗaya daga cikin matan da aka riƙa jin muryoyinsu a fagen fafutikar neman yancin kan Najeriya, in ji masanin tarihin.

A ƙarshe ta rasu cikin watan Oktoban 2001.

Dokta Yusuf Bala Usman (1945 - 2005)

Yusuf Bala

Dokta Yusuf Bala Usman an haife shi a garin Musawa da ke Jihar Katsina a shekarar 1945, kuma ya rasu a watan Satumban 2005. Ya yi aiki a Sashen Tarihi na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga shekarar 1970 har zuwa rasuwarsa kamar yadda shafin intanet na cibiyar Yusufu Bala Usman ta wallafa.

Yana daga cikin fitattun masana tarihi da suka sauya yadda ake nazarin tarihin Afirka. Maimakon kallon al'ummomi ta fuskar ƙabilanci kawai, ya nuna cewa asali da tsarin zamantakewa suna canzawa ne ta hanyar abubuwan da suka faru a tarihi.

Ya rubuta littattafai da dama kan tarihin Najeriya, siyasa, tattalin arziki da addini, kuma ya taimaka wajen gyara fahimtar tarihin Arewacin Najeriya da Daular Sakkwato.

Baya ga aikin ilimi, Yusuf Bala Usman ya kasance fitaccen ɗan gwagwarmaya ta siyasa da zamantakewa. Ya yi ƙoƙari wajen wayar da kan jama'a kan yaƙi da mulkin mallaka, danniya da zalunci, tare da tallafa wa manufofin da ke kare muradun talakawa a Najeriya da Afirka baki ɗaya.

Sai dai ya riƙe muƙamai da dama na gwamnati da na jama'a, ciki har da kasancewa mamba a Kwamitin Tsara Kundin Tsarin Mulki, mai ba da shawara ga tawagogin Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna tsakanin 1979 zuwa 1982.

Balarabe Musa (1936 - 2020)

Alhaji Balarabe Musa na cikin manyan ƴan siyasar Najeriya masu ra'ayin sauyi da suka taka rawa wajen tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya ta hanyar nuna rashin amincewa ta zahiri da mulkin soja.

An haife shi ne a watan Agustan shekarar 1936 a garin Kaya na jihar Kaduna, ya yi karatu a cibiyar nazarin harkokin mulki da gudanarwa da ke Zaria da kuma wasu makarantu da ke birnin London.

An zaɓe shi gwamnan jihar ta Kaduna ne a 1979 a ƙarƙashin jam'iyyar PRP, mai rajin ceto talaka daga mulkin danniya. Ko da yake an tsige shi a 1981 kafin ya kammala wa'adinsa.

Amma duk da haka ya ci gaba da taka rawa a harkokin siyasa da bayyana ra'ayoyinsa kan yadda ake tafiyar da Najeriya inda har ya jagoranci wata tafiya ta ƙalubalantar gwamnatin soji ta Marigayi Janar Sani Abacha da zummar ganin an mayar da ƙasar kan tafarkin dimokuraɗiyya.

Bayan komawar ƙasar kan tafarkin dimokuraɗiyya a 1999, Marigayi Abdulƙadir Balarabe Musa ya zama shugaban CNPP, wata gamayyar jam'iyyun adawar ƙasar na jamhuriyya ta huɗu.

A shekarar 2018, marigayin ya bar harkokin siyasa gadan-gadan saboda dalilai na rashin lafiya inda har ya sauka muƙaminsa na shugaban jam'iyyarsa ta PRP.

Amma duk da haka ya ci gaba da bayyana ra'ayinsa kan yadda ake gudanar mulkin kasar musamman kan batutuwan suka shafi cin hanci da kuma facaka da dukiyar talaka da ya yi fice wajen nuna adawa da su.

Alhaji Balarabe Musa ya rasu yana da shekara 84, inda ya bar ƴaƴa tara, mata uku da maza shida.

Mudi Spikin

Mudi

An haifi Alhaji Mudi Spikin a ranar 1 ga watan Oktoba 1930, a unguwar Darma da ke birnin Kano. Yayi karatun Qur'ani a hannun Malam Umaru Badamagare.

Bai taba zuwa makarantar boko ba, amma duk da haka, ya zauna jarrabawar GCE Ordinary level, ta hanyar yin rijista da wata kwaleji a Ingila, acikin 1960 kamar yadda shafin intanet na Al'ummar Hausa ya ruwaito.

Ya samu illimin zamani ne a hannun abokansa na gwagwarmayar siyasa irinsu; Malam Sa'adu Zungur, Malam Aminu Kano, da kuma Alhaji Yusuf Maitama Sule. BuyMaps

Yana cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar ƙwato yancin talaka wato NEPU a 1950. Ya fara rubuta waƙoƙinsa tun a 1948, ya fara da waƙarsa ta "Rasha Abokan Tafiya", da kuma wani raddi da ya yi wa malaminsa, wato malam Sa'adu Zungur mai taken "Arewa Jamhuriya Kawai".

Alhaji Mudi Spikin, ya rasu ne a shekarar 2013 a gidansa da ke unguwar Fagge a Jihar Kano.

A tsawon rayuwarsa, an ɗaure shi sau da dama saboda fafutukarsa ta siyasa da gwagwarmayarsa wajen kare haƙƙin talakawa, musamman ta hanyar amfani da rubuce-rubucensa.