Manyan biranen Afrika na nutsewa ƙasa cikin sauri - Bincike

Asalin hoton, Getty Images
Wani sabon bincike da aka yi amfani da bayanan tauraron ɗan'adam ya nuna cewa wasu daga cikin manyan biranen Afirka na nutsewa cikin ƙasa, cikin sauri fiye da yadda aka yi zato a baya.
Daga cikin biranen akwai Lagos a Najeriya da kuma Alexandria a Masar.
Binciken ya ce wasu daga cikin abubuwan da ke haddasa wannan matsala na faruwa ne a ɗabi'an ce.
Sai dai wasu da dama daga cikinsu na da alaƙa da wasu ayyukan bil'adama musamman yawan gina rami domin haƙo ruwa da gina madatsun ruwa.

