Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya janyo ambaliya a wasu sassan Abuja?
A ƙarshen makon nan ne wasu sassan Abuja, babban birnin Najeriya, suka fuskanci wata mummunar ambaliya da ta haddasa tsaikon zirga-zirga, lalata kadarori, tare da haifar da damuwa ga mazauna yankunan da abin ya shafa.
Lamarin ya sake jawo hankalin jama'a kan yadda birnin ke fama da matsalar ambaliya duk da kasancewarsa ɗaya daga cikin biranen da aka tsara bisa tanadin hukumomi.
Kodayake ruwan sama mai ƙarfi na daga cikin abubuwan da ke haddasa ambaliya, masana da dama na ganin matsalar ta wuce yawan ruwan sama.
A cewarsu, yadda ake ci gaba da gina gidaje da wuraren kasuwanci a wuraren da aka tanada domin hanyoyin ruwa da kwazazzabai na daga cikin manyan abubuwan da ke kara tsananta matsalar.
Wasu kuma na ɗora alhakin ambaliyar kan gazawar tsare-tsaren birane da kuma yadda aka ba da izinin gine-gine a wasu wuraren da a baya aka ware domin kare muhalli da saukar ruwan sama.
A cewarsu, ƙarin gine-gine a wuraren da ba a saba gani ba a birnin na rage wuraren da ruwa ke iya bi ta cikinsa kasa, lamarin da ke sa ruwan ya sauya hanya zuwa kan tituna da unguwanni.
Ina ambaliyar ta fi shafa?
Rahotanni kan ambaliyar da aka samu a Abuja a ƙarshen mako sun nuna cewa wasu daga cikin yankunan da abin ya fi shafa sun haɗa da:
- Katampe Main, inda mazauna suka ce ambaliyar ta lalata katangu da motoci, tare da sake tayar da hankali kan wadatar magudanan ruwa a yankin.
- Utako, musamman kusa da Dan Suleiman Street, inda aka ruwaito cewa wasu motoci sun nutse a ruwa
- Wuse 2, musamman kan Adetokunbo Ademola Crescent, wanda ya fuskanci ambaliya mai tsanani, inda hotunan bidiyo suka nuna motoci na yawo a saman ruwa.
- Maitama, Fitacciyar unguwa mai tarin ofisoshin jakadanci da gidajen manyan jami'an gwamnati a Abuja.
- Gudu, ciki har da yankin da ke kusa da Delight Event Centre da kuma hanyar Ebeano-Gudu Road.
- Lokogoma, musamman Efab Estate, inda ruwa ya mamaye wasu hanyoyi da kadarori.
- Gaduwa da Durumi, inda gadar da ke haɗa yankunan biyu ta cika da ruwa, lamarin da ya katse zirga-zirga na ɗan lokaci.
Me ya janyo ambaliyar?
Mutane da dama sun yi mamakin abin da ya haddasa ambaliyar a birnin da ya fi kowane tsari da bin ƙa'ida a Najeriya.
To amma Timothy David Bono, ƙwararren mai bayar da shawara kan tsara birane da ke zaune a Abuja, ya ce abubuwa da dama ne suka haddasa ambaliyar na Abuja.
- Sauka daga ainihin tsarin ginin birnin
Ɗaya daga cikin dalilan a cewar Dr Timothy shi ne sauka da hukumomin birnin suka daga ainihin tsarin ginin birnin.
''A ainihin tsarin ginin Abuja, akwai tanadin bai wa ruwa damar wucewa da wuraren da za a gina magunan ruwa, amma a yanzu ba a bin tsarin'', in ji shi.
Masanin ya ce a tsarin ginin Abuja akwai ƙa'idar bayar da tazara tsakanin gine-gine, wanda a yanzu ba a fiya bin tsarin ba.
- Gina wuraren hutawa da shaƙatawa:
Ɗaya daga cikin dalilan shi ne gine wuraren hutawa da shaƙatawa na birnin.
A baya-bayan nan ana zargin hukumomin birnin da sayar da wasu daga cikin wuraren hutawar ga masu gine-gine a birnin.
Masanin tsarin biranen ya ce su wuraren hutawar ba kawai amfaninsu hutu ko shaƙatawar ba.
''Suna taimaka wajen tsose ruwa idan ya sauka, to idan aka gine su, da zarar ruwan ya sauka sai ya fara gudu, saboda babu abin da tsotse shin'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
- Toshe magudanan ruwa
Wani dalilin da ya ahifar da ambaliyar a birnin an Abuja shi ne toshewar magudanar ruwa.
''Shi ruwa ba a toshe masa hanya, in ma aka toshe zai samar wa kansa hanyar da zai wuce, a wannan dalili ne ruwan ke haifar da ambaliya'', in ji shi.
Galibi wasu magunan ruwa a wasu unguwannin Abuja kan kasance a toshe saboda yadda mutane ke zuba shara a cikinsu.
Me ya kamata hukumomi su yi?
Dr Timothy ya ce akwai matakan da ya kamata hukumomin birnin da mazauna birnin su ɗauka domin magance matsalar.
''Na farko shi ne a koma amfani da ainihin tsaron ginin birnin wanda ya tanadi matakan kauce wa samun ambaliyar'', in ji shi.
Masanin tsarin biranen ya ci gaba da cewa ya kamata hukumomin Abuja su daina sayar da da wuraren hutawa da na shaƙatawa ga masu gine.
''Waɗannan wuraren suna da matuƙatr muhimmanci wajen hana aukuwar ambaliya, ba hutawar ba ne kawai amfaninsu'', in ji shi.
Dr Timothy ya kuma yi kira ga mazauna birnin su daina zuba shara a magunan ruwa na unguwanninsu.
''Ɗaukar matakin ba na gwamnati ce kaɗai ba, su ma mazauna birnin na da rawar da za su taka wajen taƙaita aukuwar hakan'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa dole ne mazauna birnin su guji toshe magunar ruwa na unguwanninsu ta hanyar zuba shara a cikinsu.