Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu 5 da ya kamata ku sani kan zaɓen gwamnan jihar Osun
Al'ummar jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya na shirin fita rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri'ar zaɓen gwamnan da zai jagorancin jihar tsawon shekaru huɗu masu zuwa.
Hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta ce mutum 2,339,233 ne a cikin rijistar masu zaɓe, inda 1,906,390 suke da katin zaɓe wato kimanin kaso 81.5 na waɗanda suka yi rijistar.
Ƴantakara 15 ne ke takarar kujerar gwamnan jihar da zaɓenta ya kasance a koyaushe mai cike da taƙaddama.
BBC ta tsamo wasu batutuwa masu ɗaukar hankali dangane da zaɓen.
Sunayen ƴantakara 15 da jam'iyyunsu
A farko dai, INEC ta fitar da sunayen 'yan takara 14, amma bayan hukuncin kotu da ya umarci a saka ɗan takarar SDP a takardar kaɗa ƙuri'a, adadin ya kai 15 yanzu haka.
- Ademola Adeleke - AP
- Bola Oyebamiji - APC
- Najeem Salaam - ADC
- Farinloye Olarenwaju – AA
- Esan Olajide – AAC
- Adeagbo Opawoye – ADP
- Mustapha Adeniyi – SDP
- Adesina Aseyemi-Doro – APGA
- Adewale Adebayo – APM
- Clement Adesuyi – APP
- Masilo Adeleke – BP
- Taofeek Adeleke – NNPP
- Saliu Oyelami – PRP
- Ogunsakin Olalekan – YPP
- Adefemi Adesuyi - ZLP
Takarar za ta fi zafi tsakanin mutum 3
Duk da cewa ƴan takarar 15 ne ke fafatawa a zaɓen gwamnan jihar ta Osun amma bisa abin da ke faruwa a jihar ana ganin takarar za ta fi zafi tsakanin ƴan takara guda uku.
- Ademole Adeleke - AP: Ademola Adeleke shi ne gwamnan jihar Osun mai ci. Kuma ya samu nasarar zama gwamnan ne a zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2022, a ƙarƙashin jam'iyyar PDP bayan kayar da gwamna mai ci na lokacin Gboyega Oyetola.
- Bola Oyebamiji - APC: Bola Oyebamiji wanda ke takara a ƙarƙashin jam'iyyar APC, na ɗaya daga cikin manyan 'yan adawar da ke ƙalubalantar gwamna mai ci, Ademola Adeleke, a zaɓen gwamnan jihar Osun. Tsohon ma'aikacin banki ne wanda ya yi kwamishinan kuɗi na jihar lokacin Ra'uf Aregbesola da Gboyega Oyetola.
- Najeem Salaam - ADC: Ya kasance tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Osun karo biyu a 2011 da 2015.
Dantakarar PDP ya ce a zaɓi Ademola Adeleke
Ɗan takarar gwamnan Jihar Osun a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Adedamola Adebayo, ya sanar da cewa ya janye daga takarar kujerar gwamna.
Adebayo, wanda aka fi sani da Fryo, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Osogbo ranar Juma'a.
Fryo ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa tsarin zaɓen ya gudana cikin lumana da tsari, tare da ba Gwamna Ademola Adeleke damar kammala ayyukan ci gaba da suka tsaya cik.
Ya bayyana cewa ya janye daga takarar ne saboda muradinsa shi ne mara wa Adeleke baya.
Sannan ya yi kira ga dukkan magoya bayansa da masu sha'awar siyasa da su goyi bayan Ademola Adeleke domin ya samu damar komawa kan mulki wa'adi na biyu.
Ƴansanda 15,000 da kwamishinoni 30
Rundunar ƴansanda Najeriya a ranar Alhamis ta ce kwamishinonin ƴansanda 30 ne ta tura zuwa jihar Osun domin kula da tsaro a zaɓen da za a yi na gwamna a jihar.
Kakakin rundunar ƴansandan ƙasar, CSP Anietie Iniedu ne ya fadi hakan a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a birnin Osogbo na jihar.
CSP Anietie ya ƙara da cewa rundunar ƴansandan sun fara tura dakarunsu 15,000 tare da kwamishinonin ƴansandan tun mako biyu da suka gabata.
Bugu da ƙari, rundunar ƴansanda ta kuma gargaɗi dukkannin wasu ƙungiyoyin tsaro da suka haɗa da Amotekun da sauran ƙungiyoyin sintiri.
Har wayau, rundunar ta ce za kuma ta yi amfani da jami'an tsaron farin kaya da sojoji da jami'an gidan yari da na kiyaye haɗurra duka a lokacin zaɓen.
Akpabio da gwamnoni sun hallara a Osun
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya isa Jihar Osun gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a wannan ƙarshen mako.
Sanata Akpabio ya jagoranci wata tawaga da ta haɗa da shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jam'iyyar APC kuma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma da gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo; da gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo.
Hakazalika, gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ikeja a Jihar Legas, James Faleke, su ma sun isa Jihar Osun domin nuna goyon baya ga ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Bola Oyebamiji.