Firaministan Kurdistan na Iraq ya yi allawadai da harin Iran kan ofishinsa
Firaministan yankin Kurdistan na Iraq, Masrour Barzani, ya yi allawadai da abin da ya bayyana a matsayin harin jiragen yaƙi marasa matuƙi na Iran kan ofishinsa da kuma gidan shugaban hukumar leƙen asirin yankin.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, Barzani ya ce bayanan da binciken Hukumar Yaki da Ta'addanci ta gwamnatin Kurdistan suka tattara sun tabbatar da cewa Iran ce ta kai harin.
Ya bayyana lamarin a matsayin "aikin da ba za a amince da shi ba" tare da yin tir da shi."
Firaministan ya ce harin wani mataki ne mai haɗari na ƙara tashin hankali, kuma barazana ce kai tsaye ga tsaro da zaman lafiyar yankin.
Tun da farko, Hukumar Yaki da Ta'addanci ta Kurdistan ta ce babu wanda ya mutu ko ya jikkata a harin, tana mai cewa an harba jiragen Hadid 110 guda biyu masu ɗauke da abubuwan fashewa daga wajen iyakar Iran.