BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Sai an cika sharuɗɗanmu bakwai kafin mu buɗe mashigar Hormuz - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Lahadi 4 ga watan Oktoban 2026
‘Yadda muke kwana a dazuka saboda rashin tsaro’
Jama'ar Wasagu da sauran wasu garuruwa kimanin bakwai na yankin karamar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, na ci gaba da kokawa kan yadda matsalar hare-haren 'yan bindiga ke ta addabar su, har ma wasu magidanta sun kwashe wata biyar ba sa iya kwana a gidajensu ba
Jihohin Najeriya da suke da arzikin man fetur
A yau, jihohi da dama ne ke samar da ɗanyen mai, musamman a yankin Neja Delta, wanda ya kasance cibiyar harkokin man fetur a ƙasar.
A shekara nawa ya kamata matasa su yi aure?
Ana cewa idan mutum ya kai wasu shekaru bai yi aure ba, zai iya fara yin wasu "ɗabi'u da ba a gane musu ba" ko kuma lafiyar ƙwaƙwalwarsa ta iya fuskantar matsala.
Mene ne sakamakon yiwuwar haramta fitar da dizel daga Amurka?
Yaƙin da ke gudana tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran da kuma takurawar wadatar mai a kasuwar duniya na daga cikin abubuwan da suka haddasa tashin farashin.
Wataƙila a kawo ƙarshen yaƙin Iran zuwa bayan zaɓe - Trump
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Asabar 3 ga watan Oktoban 2026
Hanyoyi 4 da abinci zai iya sa ku farin ciki
Daga shan isasshen ruwa zuwa cin ganyayyaki, ƙwararru sun bayyana ƙananan canje-canje a cikin abinci waɗanda za su iya taimakawa wajen tallafawa yanayi da walwalar ƙwaƙwalwa.
Mene ne Ruwan Zamzam kuma daga ina ya samo asali?
A ƴan kwanakin nan kusan za a iya cewa ƴan soshiyal midiya da dama daga arewacin Najeriya suna birnin Makka ko Madina a ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umra.
’Mutumin da aka yi wa gwajin rashin haihuwa, amma aka gano yana da mahaifa’
Bayan da aka gano wannan yanayin, wasu tambayoyi sun taso, kamar ko mara lafiyan zai iya ɗaukar ciki, ko yana iya yin al'ada, ko kuma ko kamanninsa na waje yana kama da na mace.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 5 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurara Kai Tsaye, Shirin Yamma, 19:29, 4 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 4 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 4 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
Me ya shiga tsakanin Ronaldo da kocin Portugal?
Magoya bayan Portugal sun fara ganin yadda tawagar ta buga wasa ba tare da Cristiano Ronaldo ba, bayan da ƙasar ta doke Denmark da ci 4-2 a gasar Nations League ranar Alhamis.
Spurs ba ta da niyyar sayar da van de Ven, ƙungiyoyin Premier na neman Matanovic
Tottenham ba ta da niyyar cefanar da ɗan wasan baya Micky van de Ven, ƙungiyoyin Premier uku na zawarcin ɗan wasan Freiburg Igor Matanovic yayin da Juventus ke son ɗan wasan bayan Liverpool Giovanni Leoni.
Chiesa na shirin barin Liverpool, Haaland zai iya komawa Barcelona
Ƙungiyoyi uku na gasar Serie A na zawarcin ɗan wasan gaban Liverpool Federico Chiesa, akwai yiwuwar ɗan wasan gaban Man City Erling Haaland zai so komawa Barcelona, yayin da Juventus ke son ɗaukar Michael Kayode daga Brentford.
KAI TSAYE, Man City ta shigar da kara kan samunta da laifin karya dokar Premier
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin kai tsaye a BBC Hausa daga 28 ga Satumbar zuwa 4 ga Oktoban 2026.
Me ya sa Ronaldo ya bar sansanin horar da Portugal 'rana tsaka'?
Cristiano Ronaldo ya ce ya bar sansanin ƴanwasan Portugal kuma zai yi bayani kan dalilin "a lokacin da ya dace", sa'o'i bayan kocin kungiyar Jorge Jesus ya musanta cewa akwai wata takaddama tsakaninsa da ɗanwasan.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Kamfanoni 21 da kotu ta ce suna harkoki ba bisa ƙa'ida ba a Najeriya
EFCC ta gurfanar da kamfanonin ne kan tuhume-tuhume da suka shafi gudanar da harkokin hada-hadar kuɗi ba tare da lasisin da doka ta tanada ba
Matsaloli 5 da suka hana Najeriya zama giwar Afirka
Tsaro, talauci, rashawa, sauyin yanayi da rashin aikin yi na daga cikin manyan matsalolin da suka daɗe suna taɗiye ƙafafun ƙasar.
Amurka ta sake tura babban jirgin yaƙi Gabas ta Tsakiya
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 2 ga watan Oktoban 2026
Mece ce hujjar Trump kan iƙirarin haɗa miyagun ƙwayoyi a cibiyoyin nukiliyar Iran?
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin a karon farko a wani jawabin yaƙin neman zaɓensa da ya gabatar a Durant, jihar Oklahoma, cewa cibiyoyin nukiliyar Iran da jiragen saman B-2 na Amurka suka kai wa hari ana amfani da su ma wajen haɗa miyagun ƙwayoyi. Sai dai bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da wannan ikirari ba.
Shin sanya albasa a ƙafafu na maganin mura?
Iƙirarin da ake yi game da cewa albasa na warkarwa na ci gaba da jan hankali a shafukan sada zumunta.
Abin da ƴansanda suka ce kan hawan doki a Kano
Kwamishinan ya ce duk wanda ke da buƙatar hawa a Kano sai ya sanar da jami'an tsaro tun da farko.
Yadda Kanawa ke murnar samun ruwan famfo bayan shekara 20
Yanzu dai fatan da Kanawa ke yi shi ne na ɗorewar ruwan da kuma kai wa ga wasu unguwoyi da garuruwan da ba su da wannan ruwa domin rage musu raɗaɗin wahalar rashin ruwa ta shekaru aru-aru.
Mutum 10 da suka yi rawar gani wajen samun ƴancin Najeriya
BBC ta yi bincike daga ɓangarori daban-daban dangane da mutanen da suka fi taka rawa wajen fafutukar nema wa Najeriya 'yanci.
Dabarun yaƙi 9 da sojoji suka ƙirƙira a tarihi
Tun daga lokacin da mutum ya fara amfani da sandar itace wajen kai wa maƙiyinsa hari, ɗan Adam ya ci gaba da neman sabbin hanyoyi da dabarun yaƙi domin kayar da abokan gaba.
Wane ne Dujjal da yadda ake gane shi?
A cikin hadisai, Dujjal ba wata alama ce kawai ko wata falsafa ba; an bayyana shi a matsayin mutum wanda zai fito a ƙarshen zamani. Fitinarsa za ta kasance babba sosai, har Annabi ya yi gargadi akai-akai game da ita.
Abu huɗu da suka sauƙaƙa rayuwar ƴan Najeriya bayan ƴancin kai
A yanzu, bayan fiye da shekara 60 da samun ƴancin kai, fasaha ta kawo sauye-sauye da dama da suka sa rayuwa ta yi sauƙi.
Real Madrid ta dage kan Quansah, Liverpool na sa ido kan Mora
Real Madrid nta dage wajen ɗauko ɗan wasan Bayer Leverkusen Jarell Quansah, yayin da Liverpool ke sa ido kan Gilberto Mora, sai Roma da ke harin ɗan wasan Real Madrid striker Endrick. Da ƙarin wasu wasannin.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































