Yadda sabon jirgin saman shugaban Ghana da ya kai dala miliyan 60 ya tayar da ƙura

Jirgin shugaban ƙasar Ghana, mai ɗauke da launukan tutar ƙasar
Bayanan hoto, Jami'ai sun ce jirgin ƙirar Falcon 6X da aka kera a Faransa ya maye gurbin jirgin saman shugaban kasa da ya tsufa
    • Marubuci, Wycliffe Muia
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Gwamnatin Ghana ta kare matakin da ta ɗauka na sayen sabon jirgin saman shugaban ƙasa, matakin da ya janyo muhawara mai zafi, musamman kan kuɗin da aka kashe wajen sayensa, a daidai lokacin da 'yan ƙasar da dama ke ci gaba da fama da tsadar rayuwa.

Jirgin ƙirar Falcon 6X, wanda aka ƙera a Faransa kuma aka saya kan dala miliyan 60 (£46m), ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasa, inda 'yan adawa suka zargi gwamnatin Shugaba John Mahama da fifita sayen jirgin a kan buƙatun al'umma.

Sai dai gwamnatin ta ce babu laifi a matakin da ta ɗauka, tana mai cewa ingantuwar tattalin arzikin ƙasar ta ba ta damar sayen jirgin, wanda kuma ya zama wajibi domin maye gurbin tsohon jirgin saman shugaban ƙasa.

Wannan muhawara ta barke ne a daidai lokacin da gwamnatin Mahama ke ƙoƙarin nuna alamun farfaɗowar tattalin arzikin Ghana, bayan shafe shekaru tana fama da matsalolin kuɗi da suka kai ga neman tallafin Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF).

Kamfanin kera jiragen sama na Faransa, Dassault Aviation, ne ya ƙera jirgin, wanda aka miƙa wa rundunar sojin saman Ghana a ranar Litinin kan kuɗin dala miliyan 61.

Majalisar Dokokin Ghana ta amince da sayen jirgin a watan Disamban bara, a matsayin wani ɓangare na babban shirin zamanantar da rundunar sojin saman ƙasar. Shirin ya kuma ƙunshi sayen jiragen sama masu saukar ungulu guda huɗu daga kamfanin Airbus.

An yi wa jirgin maraba da gaisuwa a ranar Litinin, amma isowarsa ta janyo suka a kafafen sada zumunta da kuma tsakanin 'yan siyasa na adawa, musamman kan kuɗin da aka kashe wajen sayensa da kuma lokacin da aka gudanar da sayen.

A lokacin da yake jam'iyyar adawa, Shugaba John Mahama da kansa ya nuna rashin amincewa da sayen sabon jirgin saman shugaban ƙasa. Hakan ya sa ake tambayar dalilin da ya sa gwamnatinsa ta sauya matsaya tare da amincewa da sayen jirgin.

Ɗan majalisar dokoki na jam'iyyar adawa, Samuel Abu Jinapor, ya yi tambaya kan irin abubuwan da gwamnati ta sa a gaba, yana mai cewa kashe waɗannan kuɗaɗe ya zo ne a lokacin da al'ummar Ghana da dama ke fama da tsadar rayuwa, yayin da matasa da dama ke fuskantar rashin aikin yi.

"Abin da ba za a amince da shi ba lokacin da ake adawa, ba zai zama abin amincewa ba kwatsam saboda kawai an sauya waɗanda ke kan mulki," in ji Jinapor.

Ya zargi jam'iyyar National Democratic Congress (NDC) mai mulki da munafunci, yana mai tunatar da ita yadda ta yi adawa da batun sayen sabon jirgin saman shugaban ƙasa lokacin da ba ta kan mulki.

Jinapor ya kuma buƙaci gwamnati da ta ƙara bayyana gaskiya game da tsarin sayen jirgin, inda aka samo kuɗaɗen da aka kashe wajen sayensa, da kuma dalilan da suka sa ta ga ya dace a kashe irin waɗannan kuɗaɗe a wannan lokaci.

Kenneth Adjei sanye da riga mai launin shuɗi a cikin jirgin sama mai tsada
Bayanan hoto, Ministan Tsaro Kenneth Adjei ya yi maraba da kuma duba sabon jirgin a ranar Litinin
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sayen jirgin ya kuma janyo suka mai zafi a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin cewa da an yi amfani da kuɗin wajen biyan wasu buƙatun jama'a masu muhimmanci.

"Wannan kuɗin zai iya ɗaukar ma'aikatan jinya sama da 100,000 da malamai 200,000 aiki," kamar yadda wani mai amfani da kafar X ya wallafa.

Sai dai gwamnati ta yi watsi da sukar, tana mai cewa yanayin tattalin arzikin Ghana ya sauya matuƙa tun lokacin da jam'iyyar NDC ke adawa da irin wannan saye.

Peter Lanchene Toobu, shugaban kwamitin tsaro na majalisar dokokin ƙasar, ya ce jam'iyyar ba ta taɓa adawa da sayen sabon jirgin saman shugaban ƙasa a ƙa'ida ba.

Ya ce abin da suka yi adawa da shi shi ne lokacin da aka nemi sayen jirgin, kasancewar Ghana na fuskantar matsanancin ƙalubalen tattalin arziki a lokacin.

"Mun amince tun da farko cewa muna buƙatar sayen sabon jirgin saman shugaban ƙasa," in ji shi.

Sai dai ya ce a wancan lokacin, Ghana ba ta cikin halin da zai ba ta damar kare kashe irin waɗannan kuɗaɗe, musamman ganin cewa tana neman tallafin dala biliyan uku daga Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF).

Ya ƙara da cewa: "Ƙarfin tattalin arzikin ƙasar da kuma daidaituwar yanayinsa a yanzu sun ba mu damar sayen kayayyaki daga ƙasashen waje cikin sauƙi, don haka wannan shi ne lokacin da ya dace."

Toobu ya ce gwamnati ta sayi jirgin ne ba tare da karɓar bashi ba, yana mai danganta hakan da ƙarfafa darajar kuɗin Ghana da kuma ingantuwar tattalin arzikin ƙasar.

Kakakin gwamnatin Ghana, Kwakye Ofosu, shi ma ya yi watsi da sukar da ake yi wa sayen jirgin, yana mai cewa masu sukar ba su yi la'akari da sauyin da tattalin arzikin ƙasar ya samu ba.

Ya yi nuni da raguwar farashin kayan gini da kuma kuɗin ruwa kan rance a matsayin wasu daga cikin alamomin ingantuwar tattalin arzikin ƙasar.

"Lokacin da nake yaƙin neman zaɓe a shekarar 2024, ina bayar da gudummawar siminti, farashin buhu ɗaya ya kai cedi 115 (£7.50). Amma a yau, ana iya samun buhun siminti kan cedi 80," kamar yadda ya shaida wa tashar JoyNews.

Muhawarar ta kuma shafi abubuwan more rayuwa da ke cikin jirgin, bayan da aka yi ikirarin cewa yana da ɗakin kwana da bandaki na musamman.

Sai dai Ofosu ya musanta waɗannan ikirari, yana mai cewa jirgin ba shi da irin waɗannan abubuwa.

"Tabbas babu bandaki. Shugaba Mahama ba shi da niyyar yin wanka a sararin samaniya," in ji shi.