United na harin Bassey da Collins, AC Milan na zawarcin Endrick

Bassey
Bayanan hoto, Bassey
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Fulham da Najeriya Calvin Bassey, na cikin ƴan wasan da ake hasashen cewar Mauricio Pochettino zai iya ɗaukowa zuwa Manchester United a kakar siyar da ƴan wasa a watan Janairu. (Telegraph - subscription)

Ɗan wasan Brentford Nathan Collins, na cikin waɗan da Manchester United ke son ɗauka baya ga Liverpool da Tottenham da su ma ke zawarcin ɗan wasan. (Football Insider)

Manchester United na harin Noussair Mazraoui, da ke jan hankalin AC Milan, da Juventus da wasu ƙungiyoyi da ke Saudiya. (Caught Offside)

Ɗan wasan Juventus Weston McKennie, an cikin waɗan da Pochettino, ke son ɗauka, kasancewar ya horar da ɗan wasan ƙasar Amurka. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

AC Milan na da ƙwarin gwaiwa cewar dangantakar da ke tsakaninsu da Kaka na iya taimaka mata wajen ɗauko aro Endrick, daga Real Madrid. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Paris St-Germain, Arsenal, da Chelsea, da Manchester United na kan aniyarsu na ɗauko ɗan wasan Como Nico Paz, sai dai Real Madrid ta dage kan wata kwataragi na sake daukarsa idan ta yanke shawarar yin haka, a nan gaba. (Fichajes - in Spanish)

Everton na zawarcin Samuel Lino, da ya zura ƙwallaye 21daga wasannin 33 da ya bugawa Flamengo a wannan kaka. (Liverpool Echo)

Stuttgart ba ta da wani shiri na siyar da Bilal El Khannouss, duk da harin ɗan wasan da Leeds United ke yi. (Football Insider)

Ɗan wasan Manchester United Joshua Zirkzee, da takwaransa na Chelsea Jamie Gittens, na cikin yan wasan da Napoli ke zawarci a watan Janairu. (Tuttomercato)