Mai kungiyar Andorra ya ce bai kamata a dakatar da Owono wasa 12 ba, Jesus Owono
Asalin hoton, Getty Images
Mai kungiyar
FC Andorra, Gerard Pique, ya ce mai tsaron raga Jesus Owono bai cancanci
dakatarwar wasa 12 da aka yi masa ba, - bayan taho mu gana da ta kai ga mutuwar
ɗan wasan Tenerife, Jesus de Miguel.
Lamarin ya
faru a wani wasan rukuni na biyu a gasar Spain a ranar 2 ga Nuwamba. An kai De
Miguel dakin kulawa na musamman daga baya ya rasu washegari.
Kwamitin
ladabtarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Spain ne ya dakatar da Owono da c ewar ya
yi amfani da karfi fiye da kima da ya haddasa mummunan raunin.
An hukuntan wani dan kallo da ya ci zarafin Kylian Mbappe, Kylian Mbappe
Asalin hoton, Getty Images
Wani mai
goyon bayan Real Oviedo da ya yi cin zarafin ɗan wasan gaba na Real Madrid,
Kylian Mbappe ta hanyar kalaman wariyar launin fata a bara, an same shi da
laifi, kamar yadda Real Madrid ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata.
An ci tarar
mutumin da ba a bayyana sunansa ba, an kuma hana shi shiga filayen wasa na
tsawon shekaru biyu, sannan an yanke masa hukuncin ɗaurin watanni 11 amma ba
zai je gidan yari ba sai idan ya karya dokar hana shi shiga filayen wasanni nan
gaba.
Lamarin ya
faru ne a lokacin nasarar da Real Madrid ta yi da ci 3-0 a kan Real Oviedo a
watan Agustan 2025.
Dokar Spain
ta tanadi cewa hukuncin da bai kai shekara guda ba yawanci ana dakatar da
aiwatar da shi ga wanda ya yi laifi a karon farko.
Wannan shi
ne hukunci kan samun magoyin baya da kalaman wariya da cin zarafi na 12 da ya
shafi wasannin LaLiga tun daga watan Yunin 2024.
Watakila Ingila ta karbi bakuncin wasan karshe a Nations League, Nations League
Asalin hoton, Getty Images
Watakila
Ingila ta karbi bakuncin wasan ƙarshe na Nations League na wannan kakar bayan
da Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta nuna sha'awar hakan.
Za a gudanar
da wasannin kusa da na ƙarshe da na ƙarshe a kasa daya a cikin watan Yuni, amma
ba a fayyace kowacce ba.
Baya ga
Ingila, an fahimci cewa Spain da Faransa ma suna son shirya wasa hudu da za su
rage a karkare kakar bana daga 9 zuwa 13 ga wayan Yuni.
Tun bayan
ƙaddamar da gasar a shekarar 2019, Ingila ba ta taɓa karɓar bakuncin wasan
ƙarshe ba, kamar yadda Portugal, Italiya, Netherlands da Jamus suka yi kawo
yanzu.
Ranar Juma'a
za a raba jadawalin kwata finals, domin tantance yan hudun karshe - watakila a
hada tawagar Ingila da ta Belgium, Netherlands, Denmark ko Norway da za a barje
gumi a cikin watan Maris - kafin wasan karshe a cikin watan Yuni a 2027.
Faransa ta amince Diallo ya yi takarar shugan Fifa, Fifa
Asalin hoton, Getty Images
An amince da
takarar Philippe Diallo ta neman shugabancin FIFA daga Hukumar Kwallon Kafa ta
Faransa.
UEFA ta
sanar a ranar Litinin cewa mai shekara 63 ya samu goyon bayan wakilan
mambobinta da ke cikin kwamitin zartarwa da kuma Majalisar FIFA domin ya tsaya
takara karbe kujerar Gianni Infantino.
Hukumar
ƙwallon ƙafa ta Faransa ma ta ba shi goyon baya a jiya Talata, inda kwamitin
zartarwa na FFF ya amince baki ɗaya da takararsa.
UEFA ta dawo
daga rakiyar Infantino sakamakon shirinsa da ya jawo ce-ce-ku-ce na sayar da
hannun jari a wani kamfanin da zai ke kula da harkokin Gasar Kofin Duniya ga
masu zuba jari masu zaman kansu,
Hakan ya sa
aka fara kiraye kirayen shugaban ya yi murabus, yayin da Uefa ta yi alkawarin
fito da wani sahihin ɗan takara da zai fafata da shi.
Romario ya bukaci a kori Ancelotti, yayin ce-ce-ku-ce a tsakaninsu, Brazil
Asalin hoton, Getty Images
Babu wanda zai yi hasashen cewa Carlo Ancelotti zai fara fuskantar suka daga wani gwarzon
Brazil watanni 18 kacal bayan ya zama kocin tawagar ƙasar.
Amma
Romario, wanda shi ne na huɗu cikin waɗanda suka fi yawan cin ƙwallaye a
tarihin Brazil, bayan Neymar da Pele da Ronaldo, ya fito fili ya nemi a sauke
fitaccen kocin daga aiki a cikin makon da ya gabata.
Hakan ya biyu bayan da Brazil ta sha kashi da ci 3-2 a wasan sada zumunta a hannun Japan
ranar Juma’a.
An ba
Ancelotti jan kati saboda nuna rashin gamsuwa bayan wasan, wanda shi ne karo na
farko da aka kore shi a aikinsa na horas da tawagar ƙasa, yayin da ɗan wasan Barcelona, Raphinha, shi ma ya ga jan kati.
Bayan rashin
nasarar da Brazil ta yi, Romario ya shiga shafukan sada zumunta domin bayyana
fushinsa kan tsohon kocin Real Madrid.
"Ancelotti,
ya isa haka! Ka tattara kayanka ka tafi!" ya rubuta a Instagram.
"Babu
wanda ke musanta tarihin da ka yi. Kana ɗaya daga cikin manyan masu horarwa da
duniyar ƙwallon ƙafa ta taɓa gani, amma hakan ya kasance ne a matakin
kungiya."
An fitar da
Brazil daga Gasar Kofin Duniya ta 2026 a zagayen 'yan wasa 16 a
hannun Norway, lamarin da ya sa ta kasa kai wa wasan kwata-fainal karo na farko
tun shekarar 1990.
Romario ya
yi nuni da wannan ma, inda ya ce ƙasar "ba za ta iya ɗaukar haɗarin sake
jefa kasar cikin hadari a wata Gasar Kofin Duniya ba - lokacin ɗaukar mataki shi ne
yanzu!"
Rafael Camara zai kara wakiltar Haas a Las Vegas Grand Prix, Formula 1
Asalin hoton, Getty Images
A Formula One, ɗan kasar Brazil, Rafael Camara, zai yi wa tawagar Amurka ta Haas tsere karo na biyu a gasar Las Vegas Grand Prix ta ƙarshen mako.
Matashin mai shekaru 21 ya yi wasansa na farko tare da Haas a gasar Sao Paulo Grand Prix da ta gabata tare da takwaransa, Oliver Bearman.
Andreeva ta lashe WTA Final bayan doke Svitolina, Kwallon tennis
Asalin hoton, Getty Images
Matashiyar 'yar wasan Rasha, Mirra Andreeva, ta doke Elina Svitolina ta Ukraine da ci 7-5, 6-3 ranar Lahadi ta lashe WTA Final - gasar kakar karshe da yan wasa takwas dake kan gaba a tennis a duniya suka halarta Indian Wells.
Andreeva ta jefa raket ɗinta sama sannan ta yi tsallen murna lokacin da Svitolina ta bugo ƙwallo cikin raga a maki na ƙarshe, kafin daga bisani ta rungumi kocinta Conchita Martinez da sauran tawagarta.
Klopp ya ce Infantino ya fi Blatter muni kan tafiyar da Fifa, Jurgen Klopp
Asalin hoton, Getty Images
Kociyan tawagar Jamus, Jurgen Klopp, ya ce "ban yi tunanin
abubuwa za su iya ƙara muni bayan Sepp Blatter ba, amma wani ya yi nasarar kai
su wannan matakin", yayin da ya yi kira da a maye gurbin shugaban Fifa,
Gianni Infantino.
Blatter ya yi murabus daga shugabancin FIFA a shekarar 2015, bayan badakalar cin hanci da rashawa, kuma Infantino ne ya gaje shi a
watan Fabrairun 2016.
Infantino na shirin sake tsayawa takara a watan Maris, amma
yana fuskantar matsin lamba tun bayan da ya yi watsi da shirin Fifa Forward
Enterprise (FFE), wanda ya haɗa da sayar da hannun jarin Gasar Kofin Duniya da
sauran wasannin FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu.
Infantino ya nemi afuwa ga Majalisar FIFA kan wannan shiri,
amma an gaya masa cewa bai dace ya ci gaba da jagorantar hukumar ƙwallon ƙafa
ta duniya ba, har sai ya fitar da dukkan takardun da suka shafi lamarin tare da
bayar da amsoshin muhimman tambayoyin da za a yi masa.
An bayyana shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa,
Philippe Diallo, a matsayin ɗan takarar Uefa domin kalubalantar Infantino.
Diallo zai tsaya takara bayan amincewar da Hukumar Kwallon
Kafa ta Faransa (FFF) za ta bayar a hukumance ranar Talata, bayan ya samu
cikakken goyon bayan kwamitin zartarwa na Uefa.
Lukaku ya yi ritaya daga buga wa Belgium tamaula, Romelu Lukaku
Asalin hoton, Getty Images
Romelu
Lukaku ya yi ritaya daga buga wa Belgium wasanni, yana mai cewa ya "ji
daɗin kowane lokaci" da ya shafe yana wakiltar kasar.
Dan wasan mai taka leda a Fenerbahce mai shekara 33 ya fara buga wa Belgium wasa a shekarar 2010,
kuma shi ne wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin tawagar ƙasar da 94 a raga a wasa135.
Shi ne na
biyar cikin masu yawan cin ƙwallaye a wasannin ƙasa da ƙasa a duniya a tarihi,
bayan Sunil Chhetri, Ali Daei, Lionel Messi da kuma jagora Cristiano Ronaldo,
wanda ya ci ƙwallaye 146.
Lukaku ya ci
ƙwallaye takwas a gasar kofin duniya guda huɗu da ya halarta, ciki har da lokacin
da Belgium ta kai wasan kwata-fainal a gasar bana, sannan ya ci jimillar
ƙwallaye shida a gasar European Championship guda uku.
Jama'a barkanmu da wannan lokacin na labarin wasanni daga BBC Hausa da za muke sanar da ku irin wainar da ake toyawa a fagen wasanni a fadin duniya.
Za ku iya bayar da gudunmuwarku a BBC Hausa Facebook a lokacin da muke gabatar muku da filin a bbchausa.com.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skipper zan gabatar muku da shirin daga ranar 16 zuwa 22 ga watan Nuwambar 2026.