Yadda APC ke nuna damuwa kan ihun 'Ba ma yi' a wajen kamfe

APC
    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ihun rashin goyon baya da ake yi wa ƴansiyasa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke tunzura su da ƙara fargaba a zukatansu a duk lokacin da suka fuskanci ana yi musu ihun.

A baya-bayan nan an ga bidiyoyi da hotunan ƴansiyasar Najeriya da ake yi wa ihun 'Ba ma yi' a lokacin da suka halarci wani taron jama'a.

Ɗaya daga cikin bidiyoyin ihun 'ba ma yi' da suka ɗauki hankali shi ne wanda aka yi wa Shugaba Tinubu a wani masallacin Juma'a a Abuja a makon da ya gabata.

Bayan faruwa lamarin ne jami;'an tsaroi suka kama fiye da mutum 70 bisa zarginsu da yin ihun a lokacin da Shugaba Tinubu ke fita daga masallacin, kodayake a farkon makon nan Shugaba Tinubu ya umarci jami'an tsaro su saki mutanen.

A lokuta da dama ƴansiyasa kan zargi juna da kitsa ko shirya musu ihun domin daƙile farin cikinsu a lokacin yaƙin neman zaɓe.

A baya-bayan nan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zargi jam'iyyun ADC da NDC masu hamayya a ƙasar da kitsa musu irin wannan ihun.

Cikin wata sanarwa da mai magana da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar, Dele Alake ya fitar ya zargi jam'iyyun hamayyar da ɗaukar nauyin masu yi mata ihun a gangamin yaƙin neman zaɓukanta.

Alake ya kuma yi kira ga jagororin jam'iyyun hamayyar su dakatar da abin da ya kira jefa rayukan matasa cikin hatsari.

Mene ne 'Ba ma yi'?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

'Ba ma yi' jimla ce da ke nuna rashin goyon baya ga wanda aka faɗa wa ita.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa na Jami'ar Bayero da ke Kano, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasar Najeriya ya ce jimla ce ta Hausa mai ɗauke da ma'anar ''ba ma goyon bayanka a siyasance''.

Ya ara da cewa a siyasance, "Ba ma yi" na nufin wata dabara ko matsayar siyasa da mutum ko ƙungiyar siyasa ke amfani da ita wajen nuna cewa masu faɗarta ba za su goyi bayan wanda suke faɗawa ba.

''Idan mutane suka riƙa ihu suna cewa 'Ba ma yi! Ba ma yi!' ga ɗan siyasa a lokacin taro ko gangamin siyasa, wannan yana iya zama wata alama ta rashin amincewa da ɗan siyasa ko manufofinsa a bainar jama'a'', in ji masanin siyasar.

Farfesa Kamilu ya ce a nazarin siyasa wannan shi ake kira boren masu zaɓe.

''Alama ce da ke nuna cewa masu zabe ba sa tare da wanda suka yi wa ihun'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa ba tun yanzu aka fara amfani da irin wannan salo ba wajen nuna rashin goyon bayan ɗansiyasa a Najeriya.

''An yi wa ƴanssiyasa a jamhuriya ta farko da ta biyu don haka ba yanzu ne aka fara amfani da wannan salo ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Martanin ADC da NDC

Tuni dai jam'iyyun ADC da NDC suka musanta wannan zargi tare da nesanta kansu da kitsa ihun da Shugaba Tinubu na APC.

Jam'iyyun sun danganta masu yin ihun da mutanen da suka ce ba sa jin dadin matakan da gwamnatin TInubu ke ɗauka.

Ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ADC, Faisal Kabir ya ce masu ihun na yi ne saboda wahalar da suke sha daga manufofin gwamnatin Tinubu da APC.

A hirarsa da BBC, Faisa Kabir ya ce yunwa da talauci da ƙuncin rayuwa da jama'a ke ciki ne ya sa suke yin irin wannan ihun.

''Mutane ba sa su juri rayuwa cikin irin wannan yanayi ba, don haka suke yi, amma ba mu da hannu a cikin wannan lamari'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa ''babu ruwanmu da ihun da mutane ke yi musu'', in ji shi.

Ita jam'iyyar NDC mai hamayya ta nesanta kanta da wannan lamari, ta bakin daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓenta na shugaban ƙasa, Ibrahim Hussaini Abdulkarim.

''Babu hannun jam'iyyun hamayya a cikin wannan sabga, mutane ne da shan wahalar mulkin APC, in da sun yi abin da ya kamata ko wani ya ce a hyi musu ihun ba za a yi musu ba'', in ji shi.

Ya zargin gwamnatin Tinubu da ɗaukar matakan da suka haifar da wahalwalu ga ƴan ƙasa, lamarin da ya ce shi ne dalilin da ya sa suke yi masa ihun.

''Babu abin da ya haɗa jam'iyyun hamayya da ihun da ake yi wa Tinubu da APC, tsakaninsu ne da talakawan da suke zaɓe su,'' in ji shi.

Wane tasiri ihun 'Ba ma yi' ke yi wa ƴansiyasa?

Farfesa Fagge ya ce ko shakka babu wannan salo na yin tasiri ga wanda aka yi wa.

"Ƴansiyasa kan ɗauki wannan salo a matsayin wata alama da ke nuna cewa ba a tare da su'', in ji shi

Ya ƙara da cewa a duk lokacin da aka yi wa wani ɗansiyasa wannan ihun kamata ya yi ya zauna ya yi nazarin dalilin da ya sa aka yi masa hakan domin ya gyara.

''Hakan kuma na nuna wa ɗansiyasa cewa ba lallai ya kai ga nasara a zaɓe ba, musamman a wannan yanki da ake yi masa ihun'', in ji Farfesa Fagge.

Masanin siyasar ya ce duk ɗan siyasar da aka yi wa irin wannan yana da kyau ya ɗauki darasi, ya gyara abubuwan da masu ihun ke zarginsa da shi domin kauce wa faɗawa tarkonsu a ranar zaɓe.