Yarjejeniyar da Tinubu ya cimma da ƴan ƙabilar Igbo kan zaɓen 2027

Asalin hoton, Tinubu/fb
- Marubuci, Abdulrazzaq Kumo
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Wani bidiyon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayin ganawa da wasu jagororin ƴan ƙabilar Igbo na jihar Legas, na ci gaba da jan hankali a shafukan sada zumunta, bayan da aka jiyo shugaban na ƙulla yarjejeniya ta fatar baka da su, don su taimaka masa wajen samun nasara a zaɓen 2027.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nazari kan yadda Kudu maso Gabas, wanda mafi yawan al'ummarsa ƴan kabilar Igbo ne, ya kasance ɗaya daga cikin yankunan da Shugaba Tinubu ya fi fuskantar ƙalubalen samun ƙuri'u a zaɓen 2023.
Mafi yawan masu kaɗa ƙuri'a a yankin sun karkata ga ɗan takarar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, kuma hasashe na nuna cewa har yanzu Obin, wanda a yanzu yana jam'iyyar NDC, na da karfi a yankin.
A jihar Legas ɗin ma wato jihar Shugaba Tinubu, Peter Obi ne ya fi samun ƙuri'u zaɓen na 2023 kuma ana ganin ƴan ƙabilar Igbo mazauna jihar sun taka muhimmiyar rawa wajen kayar da shi a zaɓen da ya gabata.
Hakan ya sa masu sharhi ke kallon ganawar da kuma kalaman shugaban a matsayin wani yunƙuri na ƙara kusanci da yankin gabanin na Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.
''Idan kuka ba ni gishiri zan ba ku manda''

Asalin hoton, Tinubu/FB
A cikin bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana fada wa jagororin al'ummar Igbon cewa "As you do for me, I do for you", kalaman da ke nufin "Idan kuka ba ni gishiri zan ba ku manda''.
Wasu na ganin kalaman a matsayin wani yunƙuri na ƙulla sabuwar alaƙa tsakanin shugaban da ƴan ƙabilar Igbo, waɗanda suka bai wa Peter Obi gagarumin rinjaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
A jihohin Abia da Anambra da Ebonyi da Enugu da Imo, Obi ne ya lashe zaɓen da tazarar da ta nuna irin goyon bayan da yake da shi a yankin.
Don haka ake ganin kalaman shugaban ba wai kawai wata raha ce ta neman ƙuri'u ba, suna nuna yadda siyasar 2027 ke ɗaukar salo, inda yankin Igbo ke ƙara zama muhimmin filin fafatawa ga jam'iyyun siyasa.
Bayan da ya kasa samun karɓuwa sosai a wurin al'ummar Igbo a zaɓen da ya gabata musamman saboda takarar Obi, ganawar da shugaba Tinubu ya yi da jagororin al'ummar Igbo na nuni da ƙoƙarin sake gina gada tsakanin ɓangarorin biyu.
Haka kuma ya tunatar da mahalarta taron cewa da yawa daga cikinsu ba su zaɓe shi a 2023 ba, amma yanzu lokaci ya yi da za a ci gaba tare, lamarin da wasu ke fassarawa a matsayin wani nau'in yarjejeniyar siyasa.
Tinubu ya yi ganawar ne da jagororin al'ummar Igbo a wurin taro na Wole Soyinka Centre for Culture and Creative Arts da ke Iganmu a jihar Legas.
"Ban ji daɗin rashin nasara ba a Legas a zaɓen 2023"

Asalin hoton, Bola Tinubu/FB
A yayin taron, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana fushinsa kan rashin nasara a jihar Legas a 2023, jihar da yake ganin jam'iyyarsa ta APC ya kamata ta fi rinjaye, amma yanzu abin ya wuce.
Tinubu ya ce: "Wasu daga cikin ku ba su zaɓe ni a 2023 ba kuma na yi fushi amma yanzu mun sasanta. Ku je ku yanki katin zaɓe."
Ya ƙara da cewa: "A ranar 16 ga watan Janairu za ku fita ku kaɗa ƙuri'a, kar ku manta mun ƙulla yarjejeniya fa."
Ya tambayi mahalarta taron idan za su kaɗa masa ƙuri'a inda mafi yawansu suka amsa da 'e'.
Shugaba Tinubu ya kuma bayyana yadda yake da goyon bayan gwamnonin yankin Kudu maso Gabas.
Alƙawuran da Tinubu ya yi a taron

Asalin hoton, Bola Tinubu/fb
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaban Najeriya ya gargaɗi mutane a taron da su bi 'wanda ya san hanya' wato shi ke nan, inda ya bayyana wasu ayyuka da yake ƙoƙarin yi.
Tinubu ya nemi haɗin kan ƙasa da kuma ɗaukar nauyin gina ƙasa tare, yana mai buƙatar 'yan Najeriya su ɗauki kan su a matsayin al'umma guda mai makoma ɗaya domin ci gaban kasar.
"Dole ne ku bi wanda ya san hanya. Ni kuma dole ne in yi aiki tuƙuru domin tabbatar da tattalin arziki ya inganta, yara suna makaranta, a kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke addabar jami'o'i, sannan a gina hanyoyi masu kyau da za su taimaka wajen kiyaye motocinmu."
Ya ƙara da cewa: "Makomarmu tana hannunmu. Dole ne yaranmu su samu ilimi. Kasancewarmu talakawa ba yana nufin kada su shiga jami'a ba."
Har ila yau, Tinubu ya ce dole ne Najeriya ta rufe babin bambance-bambancen da ke tsakaninta, domin ci gaban kasar ya dogara ne da gudunmawa da jajircewar dukkan al'ummominta
Duk da cewa shugaban ƙasar ya buƙaci al'ummar Igbo a Legas su mara masa baya a zaɓen 2027 tare da alƙawarin ci gaba da inganta tattalin arziki, ilimi da ababen more rayuwa, lokaci ne zai nuna ko wannan kira na haɗin kai da sulhu zai iya shawo kan al'ummar ƙabilar Igbo, musamman a Legas inda sakamakon zaɓen 2023 ya nuna irin tasirin kuri'un al'ummar Igbo a siyasar jihar.






























