Yadda mata ke amfani da wayayinsu wajen fallasa maza masu cin zarafi

Sarah Jassim ta ce bidiyoyin da take wallafawa na taimakawa wajen tattara hujjojin cin zarafi.
Bayanan hoto, Sarah Jassim ta ce bidiyoyin da take wallafawa na taimakawa wajen tattara hujjojin cin zarafi.
    • Marubuci, Sally Nabil
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabe
    • Aiko rahoto daga, Bagdad
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 8

"Fito daga cikin motar!" wata mata ta yi ihu tana zargin direban da nuna tsiraicinsa da kuma yi mata kalaman batsa yayin da take wucewa a mota.

Matar ta ɗauki bidiyon lamarin da wayarta a wani titin Bagadaza mai cike da jama'a, inda aka ga direban na ƙin buɗe ƙofar motarsa yayin da take ci gaba da tona asirinsa.

Ana iya kallon wannan bidiyon da wasu makamantansa a shafin Instagram na Sarah Jassim, wata mai fafutukar kare haƙƙin mata a Iraq. Tana wallafa bidiyoyin ne a madadin matan da ke zargin maza da samari da cin zarafinsu ko kuma yi musu neman lalata.

Ta shaida wa BBC cewa: "Kyamar wayarki ita ce makaminki." Ta ce: "Hanya ce ta tattara hujjoji idan mace ta yanke shawarar shigar da ƙara a kan wanda ya ci zarafinta, ko aƙalla wata hanya ce ta tona masa asiri da kunyata shi."

A cewarta, ɗaya daga cikin bidiyoyin da ta wallafa ya taimaka wajen kama wanda ake zargi da laifin, wani ɗan sanda da ake zargi da cin zarafin ɗalibai mata.

Wani bidiyon da Jassim ta wallafa ya nuna wata mata tana yi wa wani mutum ihu bayan ta zarge shi da nuna tsiraicinsa a bainar jama'a, kafin daga bisani ta yi ƙoƙarin buɗe ƙofar motarsa.
Bayanan hoto, Wani bidiyon da Jassim ta wallafa ya nuna wata mata tana yi wa wani mutum ihu bayan ta zarge shi da nuna tsiraicinsa a bainar jama'a, kafin daga bisani ta yi ƙoƙarin buɗe ƙofar motarsa.

Jassim ta ce wallafa irin waɗannan bidiyoyi na jefa ita da matan da abin ya shafa cikin haɗari.

Mun tattauna da mata da dama da suka fuskanci cin zarafi a Iraƙi, inda suka ce al'umma kan ɗora musu laifin abin da ya same su.

Jassim ta ce: "An sha yi mi barazanar kisa, sannan an yi mini barazanar watsa mini ruwan sinadarin acid."

Ta ƙara da cewa: "An zarge ni da ƙarfafa rashin ɗa'a a bainar jama'a saboda ina ƙarfafa mata su fito su yi magana a cikin al'ummar da ke tsammanin mu yi shiru."

Yanzu dai, saboda dalilan tsaro, da wuya ta fita daga gida. Maimakon haka, tana shafe sa'o'i tana wasa da karenta.

A ganinta, akwai buƙatar tsaurara dokoki, ciki har da samar da tanade-tanaden da ke ayyana tsangwama da cin zarafin jinsi ake yi wa mata matsayin babban laifi, kalmomin da har yanzu ba su cikin kundin dokokin laifuka na ƙasar.

Ta ce: "Amincewa da cewa akwai matsalar shi ne mataki na farko wajen magance ta."

"Muna buƙatar kariya, kuma dole ne a hana masu aikata irin waɗannan laifuka ci gaba da yin su."

"Babu wanda zai sani idan na kashe ki"

Mata da dama a Iraki sun shaida wa BBC cewa suna jin cewa tsaretsaren shari'a da na 'yan sanda sun ci amanarsu.

A cewar masu fafutuka da lauyoyi da dama da BBC ta zanta da su, ɗaukar matakin shari'a a kan wanda ake zargi da cin zarafi ko fyaɗe a Iraki abu ne mai ɗaukar lokaci, mai cike da sarƙaƙiya, kuma sakamakonsa ba ya da tabbas.

Wani rahoto da kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar a watan Mayu ya bayyana cewa cin zarafin da ake yi wa mata da 'yan mata a Iraƙi ya zama ruwan dare, amma ba kasafai ake kai rahotonsa ba. Rahoton ya kuma yi kira da a tsaurara dokokin da suka shafi irin waɗannan laifuka.

Daga cikin shawarwarin da ya bayar, ya buƙaci hukumomi su soke dokokin da ya bayyana a matsayin masu nuna wariya, ciki har da waɗanda ke wanke mai laifin fyade idan ya auri wadda ya yi wa fyaden, da kuma waɗanda ke ba da damar rage hukunci ga masu kisan kai a lokutan da ake kiran laifin da sunan "kisan kare mutunci".

Amal (ba sunanta na ainihi ba) ta shafe kusan shekara biyar tana fafutukar neman adalci a kotu. Ta zargi tsohon mijinta da yi wa 'yarta, wadda ba ta kai shekara 18 a lokacin ba, fyaɗe sau da dama yana mata barazana da bindiga.

Har yanzu tana tuna bayanin da 'yarta ta yi cikin alhini game da abin da ya faru. A cewarta, mahaifin yarinyar ya shiga ɗakinta tare da ajiye bindigarsa a kan gado.

Amal ta ce mutumin ya yi wa yarinyar barazana da cewa:

"Idan na kashe ki, babu wanda zai sani."

Amal ta zargi tsohon mijinta da yi wa ‘yarta, wadda ke ƙasa da shekara 18 a lokacin, fyade sau da dama.
Bayanan hoto, Amal ta zargi tsohon mijinta da yi wa 'yarta, wadda ke ƙasa da shekara 18 a lokacin, fyade sau da dama.

Batun cin zarafin jima'i dai ya daɗe yana kasancewa abin da ba kasafai ake magana a kai ba a Iraq.

Na gana da mutane da dama da suka tsira daga irin wannan cin zarafi, inda suka ce sun fi son yin shiru saboda tsoron martanin iyalansu. Wasu kuma sun shaida mana cewa suna tsoron zuwa wurin 'yan sanda saboda gudun fuskantar tsangwama da tozarci daga al'umma, da kuma yiwuwar fuskantar matsaloli sakamakon kai ƙara.

Sai dai Amal ta ƙuduri aniyar neman adalci, kuma cikin gaggawa ta kai rahoton abin da ya faru ga hukumomi.

Amal ta ce: "Tana da raunuka da dama a wuyan hannuwanta saboda yadda ya matse su da ƙarfi. Duk lokacin da ta yi ƙoƙarin yin ihu, sai ya toshe mata baki da hannunsa."

Amal ta nuna mini takardun likitoci, ciki har da sakamakon gwajin kwayoyin halitta (DNA), waɗanda ta ce sun tabbatar da bayaninta kan abin da ya faru.

Ta kuma ba da wani misali da take ganin ya nuna rashin tausayi da muguntar tsohon mijinta. A cewarta, ta taɓa jin shi yana cewa wani ɗan uwa a "wanke abin kunya" idan har aka kama shi.

A Iraki, ana amfani da wannan furuci ne wajen nuni da abin da ake kira kisan kare mutunci, wato kashe mace bisa zargin cewa ta jawo wa iyali abin kunya ko zubar da martabarsu.

Amal ta ce tana ganin tsohon mijin nata ya yi barazanar kashe 'yarsa ne domin:

"Kada a bayyana rahoton likitanci kuma kada a tabbatar da cewa an aikata mata wannan ta'asa."

Ta ce har yanzu tsohon mijin nata na ɓoye, yayin da shari'ar ke ci gaba da gudana.

Cikin kuka, Amal ta ce: "Ni kaɗai na yi wannan gwagwarmayar." Ta bayyana cewa tsohon mijin nata ya ɗauki lauyoyi da dama domin kare kansa, yayin da ita ba ta da kuɗin ɗaukar lauyan kare muradunta, kuma iyalanta sun yi biris da halin da take ciki.

Yanzu ta ce ta kusa rasa fatan samun hukuncin da zai tabbatar mata da adalci.

"Abin da nake so kawai shi ne ya nisance ni har abada," in ji ta cikin yanayin takaici da cire tsammani.

An kashe 'yar fafutuka

Mata da dama da suka tsira daga cin zarafi ba su da wata hanyar samun kuɗaɗen shiga ko kuma wurin da za su fake. Haka kuma, cibiyoyin da ke ba mata masu fuskantar tashin hankali mafaka ba su da yawa a Iraq.

Ɗaya daga cikin mutanen da suka yi fice wajen samar da irin waɗannan mafaka ita ce Yanar Mohammed, fitacciyar mai rajin kare haƙƙin mata da aka sani a duniya.

A watan Maris da ya gabata, wasu mahara ɗauke da makamai sun kashe ta a gaban gidanta da ke Bagadaza. Har zuwa yanzu dai ba a gano waɗanda suka aikata kisan ba.

A watan Afrilu kuma, wasu ƙwararru masu aiki da Majalisar Ɗinkin Duniya ta Kare Haƙƙin Bil Adama sun bayyana cewa shekaru da dama ana yi wa Mohammed barazanar kisa tare da kai mata hare-hare ta intanet.

Sun ce akwai "yiwuwar waɗannan barazanar da hare-haren sun samo asali ne daga ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addini."

Hanaa Edwar(hagu) ta wallafa wani hotonta tare da Yanar Mohammed, wanda ta ce an ɗauke shi ne kwana biyu kacal kafin a kashe fitacciyar mai fafutukar kare haƙƙin matan.
Bayanan hoto, Hanaa Edwar(hagu) ta wallafa wani hotonta tare da Yanar Mohammed, wanda ta ce an ɗauke shi ne kwana biyu kacal kafin a kashe fitacciyar mai fafutukar kare haƙƙin matan.

Masu fafutukar kare haƙƙin mata sun shaida mana sau da dama cewa hare-haren da ake kai wa takwarorinsu kai tsaye sun ƙaru a cikin 'yan shekarun nan.

Hanaa Edwar, wata fitacciyar mai rajin kare haƙƙin mata, ta ce ta ga Yanar Mohammed kwanaki biyu kacal kafin a kashe ta. Ta kuma ce ita ma ta fuskanci barazana.

Ta shaida wa BBC cewa: "A Iraq babu dokoki da suka isa kare mata, babu kariya, kuma babu adalci ga mata."

Daraktan Cibiyar Sa-ido kan Haƙƙin Bil Adama ta Iraki, Mustafa Saadoon, ya bayyana wa BBC cewa: "Matsalar Iraq ba wai ta rashin magana daga ɓangaren mata ba ne. Matsalar ita ce idan suka yi magana, tsarin da ake da shi ba a shirye yake ya saurare su ba."

Ya ƙara da cewa: "Mace da ta kai rahoton cin zarafin jima'i sai ta fara bi ta hannun iyalanta, sannan ta je ofishin 'yan sanda, daga bisani kuma kotu. A kowane ɗayan waɗannan matakai, akwai yiwuwar wani ya buƙace ta ta sasanta lamarin a ɓoye maimakon a bi hanyar shari'a."

"Biyo ni aka yi a wata mota."

Ɗaya daga cikin matan Iraq da suka ce ba su gamsu da yadda hukumomi ke tafiyar da irin waɗannan batutuwa ba ita ce Samira (wanda ba sunanta na ainihi ba).

Ta shaida wa BBC cewa yanzu tana jin tsoron tafiya a kan titi bayan ta sha fuskantar cin zarafi a lokuta daban-daban.

Ta bayar da misalin wani lamari da ya same ta a cikin motar haya, inda ta ce:

"Wani mutum yana kallon bidiyon batsa a wayarsa, sannan ya nuna mini shi kai tsaye."

Samira ta ce ta fuskanci cin zarafi a cikin motocin haya, sannan wani mutum ya riƙa binta da motarsa yayin da take kan hanyarta ta zuwa wurin aiki.
Bayanan hoto, Samira ta ce ta fuskanci cin zarafi a cikin motocin haya, sannan wani mutum ya riƙa binta da motarsa yayin da take kan hanyarta ta zuwa wurin aiki.

A wani lokaci daban a Bagadaza, Samira ta ce wani mutum ya bi ta da motarsa na fiye da minti 10.

Ta ce: "Abin ya ba ni tsoro sosai. Daga baya na hango wasu jami'an 'yan sanda, sai na nufe su na ba su labarin abin da ke faruwa. Amma suka ce ba su da hurumin shiga cikin lamarin."

Ko da yake mahaifiyarta na ƙaunarta kuma tana ba ta goyon baya, Samira ta ce ba ta saba gaya mata abubuwan cin zarafin da take fuskanta ba.

Ta ce: "Idan na gaya wa iyalina, abu na farko da za su ce shi ne kada na riƙa fita daga gida domin kare kaina."

Samira ta ce ta fidda tsammani da hukumomin da ya kamata su kare mata.

"Maza da yawa, har da wasu jami'an 'yan sanda, ba sa ganin cin zarafi a matsayin laifi. A ganinsu, idan ba ka tsangwamar mata, to ba kai namiji ba ne," in ji ta.

Mata da dama da BBC ta tattauna da su a Iraq sun kuma zargi wasu jami'an 'yan sanda da aikata cin zarafi.

BBC ta gabatar da wannan zargi ga Muqdad Miri, kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Iraki.

Sai dai Miri ya ce: "Ana samun lokutan da wasu jami'an 'yan sanda ke aikata cin zarafi, amma hakan ba ruwan dare ba ne. Duk jami'in da aka tabbatar da laifinsa na fuskantar hukunci mai tsauri, wanda zai iya kai wa ɗaurin shekaru 10 a gidan yari, sannan a sallame shi daga aiki."