Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Motsa jiki 5 da za su kare ku daga samun matsala a wuyanku
- Marubuci, David Cox
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Yana da kyau lokaci zuwa lokaci a dinga duba irin nauyin da ke kan ɗan'adam.
A lokacin da kake zaune ko tsaye, nauyin da kan ka ke dauka ya kai sama da kilogiram 5, kamar yadda kwararren likitan tiyatar kwaƙwalwa Anthony Ghosh ya bayyana, wanda ke aiki ma'aikatar lafiya da asibitin Queen's Hospital a birnin Landan. Wannan ba wata matsala ce da za a ɗaga hankali akai ba.
Sai dai biliyoyin mutane a faɗin duniya na shafe tsahon ra na cikin yanayin da ka iya cutar da lafiyarsu.
Misali sunkuyar da kai domin amfani da na'ura mai ƙwaƙwalwa da latsa wayar salula, a hankali mu na karawa wuyanmu nauyin da ya wuce ƙima.
Yanayin da muke zama ta hanyar lanƙwasa wuyan mu, nauyin da ke karuwa a wuyanmu ya kai sama da kilogiram 27, kuma Ghosh ya kara da cewa "Yanayin ya sanya dole ƙwanwar naki wuya ya ɗauki abin da ya samu komai wuyar shi."
A takaice dai, dabi'un da zamani ya zo da su da muka runguma na ɗaya daga cikin matsalolin da ke kassara lafiyar wuyan mu.
Amma aƙwai sauƙakan hanyoyi biyar da za ka iya yi domin inganta lafiyar wuyanka da kare shi daga samun matsala nan gaba, kuma hanyoyin babu ruwansu da yawan shekarun ka ko ƙarancinsu.
1. Jujjuya wuya
Idan ka na fama da ciwon wuya, Hukumar Lafiya ta Birtaniya ta bada shawarar sassauƙar hanyar motsa jiki domin samun sauki.
Ya yin da ka ke a zaune ko kwance, ka juya kan ka zuwa ɓangaren dama, ka tsaya a haka na aƙalla sakan biyu, daga nan sai ka juya angaren hagu ka yi yadda ka yi wa dama.
Ka ci gaba da yin haka kamar sau biyu ko uku, ko adadin da za ka iya a tsahon rana.
2. Ka yi zaman da ba za ka gaji ba
Tabbatar da cewa ka na zaune a yanayin da ba zai cutar da wuyan ka ba ya na da matuƙar muhimmanci, saboda zaman da zai sanya wuyanka ya lankwasa baya ko sunkuyar da kai na taka rawa wajen sanya jijiyoyin wuyan su yi tauri.
Allah ya halicci wuyanmu domin ya juya ta kowanne ɓangare, dan haka ana ba da shawarar a dinga juya shi a kai-a-kai a tsahon rana.
Sai dai hanyar da za a tabbatar da wuya na cikin koshin lafiya shi ne zaman da za ka miƙe bayan ka ta yadda wuyan ka zai tsaya wuri guda ya yin da Lakkar bayanka za ta kasance ita ma a tsaye.
Ka kaucewa sunkuyar da kai ta yadda habarka za ta yi kasa sosai, ko lanƙwasa kan ka yadda zai ƙwanta a kafaɗunka na tsayon lokaci, kar kuma ka yi baya da kan ka na dogon lokaci.
Ya na da ƙyau a duk lokacin da za ka zauna a kujera ya kasance bayan ka a miƙe ya ke, wuyan ka a miƙe, idon ka akan abin da ke gaban ka musamman idan ka na latsa na.ura mai ƙwakwalwa, ko kallon talbijin ko tukin mota.
3. Motsa wuya da sunkuyar da haɓa
Ƙwashe shekaru zaune gaban allon na'ura mai kwakwalwa na taka mihimmiyar rawar haddasa ciwon wuya, inda kan ka a ko wanne lokci ya ke sunkuye maimakon tsayawa daidai da kafadarka.
Amma wannan ba wata gagarumar matsala ce da ba za a iya magancewa ba, kawai za ka sauya yadda ka ke zama da kuma amfani da sauƙaƙan hanyoyin motsa jiki.
Cikin tsanaki za ka iya miƙar da wuyan ka sama, da juya ci ɓangaren dama da hagu a hankali, za ka iya sanya dan karamin lemo ko kwallo tsakanin haɓarka da sai ka yi kasa da shi ya ɗan taɓo haɓarka kaɗan ka tsaya a hakan na ɗan lokaci amma kar ka matse sosai, sai ka yi bayan da wuyanka a hankali.
4. Motsa wuya dama da hagu
Yadda muke ɗaukar sa'o'i da dama a zaune gaban allon kwamfiyuta ko talbijin, Gosh ya bayyana cewa indai mun yi zaman da ya dace wato bayan mu mike a kujera kan mu kuma ya na kallon abin da ke gabanmu ba tare da mun lankwasa wuyanmu ba, to wannan na taimakawa jijiyoyin mu d aiki yadda ya dace.
Idan ka na son motsa jijiyoyin wuyan ka a sauƙaƙe, ka ƙwanta akan gado, ka miƙe samɓal a hankali sai ka dago ta yadda habarka za ta taba kirjinka.
A karon farko ka dan tsaya a hakan na aƙalla sakan 30.
Ka sanya hannun ka a bayan wuyan ka, ka tallafe shi, sai ka yi gaba kadan da kan na ka amma hannun na tallafe da wuyan ya kasance kan na ka ya bar gadon.
A hankali ka cire hannun ka daga tallafar wuyan ka tsaya haka iya adadin sakannin da za ka iya. Amma a karon farko ka yi kokarin rikewa na sakan 30, ko fiye da haka.
5. Sabawa da matse naman wuyanku
Wata hanyar da za ka tabbatar wuyan ka na cikin koshin lafiya, shi ne amfani da kujera mai tebur.
Ka zauna an kujerar a miƙe ka na kallon gaban ka, daga nan sai ka sunkuyar da kan ka a hankali haɓarka ta taba ƙirjinka, ka tsaya haka na ɗan Lokaci, sai kuma ka sake juyawa yadda ka fara.
Ka maimaita hakan sau adadin da za ka iya.
Idan ka na yin hakan akai-akai za ka saukakawa wuyan ka da samun cikakkiyar lafiya.