Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wani fasinja ya yi 'yunƙurin buɗe ƙofar jirgi' kafin saukarsa a Legas
Kamfanin jiragen sama na Kenya Airways ya tabbatar da mutuwar wani fasinja a cikin jirginsa da ke kan hanyarsa daga Nairobi zuwa Legas jim kaɗan kafin jirgin ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, kamfanin ya ce lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 9:20 na dare agogon Najeriya.
Kamfanin ya ce fasinjan ya fita daga hayyacinsa kusan mintuna 20 kafin lokacin da aka shirya jirgin zai sauka, inda ma'aikatan jirgin suka ba shi agajin gaggawa tare da bin duk matakan da aka tanada domin tunkarar irin wannan yanayi.
Sai dai wasu rahotanni da fasinjojin da ke cikin jirgin suka wallafa a kafafen sada zumunta sun ce mutumin ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgin yayin da yake sararin samaniya.
Wata 'yar Najeriya da ta kasance cikin jirgin, Adekunbi Ewaola, ta bayyana a shafinta na Instagram cewa fasinjojin sun yi gaggawar ɗaure mutumin domin hana shi buɗe ƙofar jirgin.
Wani fasinja kuma ya yi iƙirarin cewa mutumin ya fara nuna halayen tayar da hankali tun kafin ya hau jirgin.
BBC News Pidgin ta nemi ƙarin bayani daga Kenya Airways game da yadda lamarin ya faru da kuma musabbabin mutuwar mutumin, amma kamfanin bai mayar da martani ba kafin ya fitar da sanarwarsa. Haka kuma sanarwar ba ta yi magana kan zarge-zargen da fasinjojin suka yi ba.
Kamfanin ya ce bayan da jirgin ya sauka a Legas, jami'an lafiya da ke filin jirgin sun tabbatar da cewa fasinjan ya rasu.
Kenya Airways ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin da abokansa tare da cewa yana aiki tare da iyalansa, hukumomin da abin ya shafa da kuma masu kula da harkokin sufurin jiragen sama wajen gudanar da bincike da ɗaukar matakan da suka dace.
"An ce yana fama da matsalar tabin hankali"
Wata 'yar Najeriya fitacciya a kafafen sada zumunta, wadda aka bayyana da suna Lola , ta ce tana cikin jirgin lokacin da lamarin ya faru, kuma ta yi imanin da abubuwa sun iya lalacewa matuƙa da ba don Allah ya tsare rayukansu ba.
Ta bayyana abin da ya faru a shafinta na Instagram mai suna @the_neene a ranar Laraba, 7 ga Oktoba.
"Wani fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a jirgin da nake ciki zuwa Legas jiya. Ya ce yana da matsalar taɓin hankali, kuma ni dai na yi tunanin cewa duk wanda zai yi tafiya ta jirgin sama ana tantance shi tun kafin ya hau jirgi. Ban san yadda za a yi hakan ba, amma ina ganin ya kamata a fara yi saboda da lamarin ya iya zama mummuna ƙwarai. Amma godiya ta tabbata ga Allah da ya tsare rayukanmu," in ji ta.
Lola ta ce da farko ta yi zaton fada ne ya ɓarke a cikin jirgin, yayin da mutumin ke kai-komo a tsakanin kujeru kuma mutane suna ta roƙonsa ya kwantar da hankalinsa.
Ta ce mutumin ya yi iƙirarin cewa yana son ganin matukin jirgin, kuma idan ba a kai shi wurinsa ba zai buɗe ƙofar jirgin domin ya mutu.
"A wannan lokacin ne kowa ya tasar masa. Maza suka yi amfani da bargo suka riƙe shi, ma'aikatan jirgin kuma suka kawo bel ɗin kujera suka daure shi. A wannan lokacin za ka iya ganin tsoro a idanunsa yayin da yake ta cewa, 'Ba zan buɗe ƙofar ba kuma, ba zan buɗe ƙofar ba kuma.' Ina ganin daga nan ne ya fara suma.
"Daga baya, lokacin da jirgin ke gab da sauka, ma'aikatan jirgin suna shirya fasinjoji domin saukar jirgi sai suka fahimci cewa ba ya cikin hayyacinsa. Daga nan suka yi ƙoƙarin farfaɗo da shi, suka yi masa CPR, suka kuma yi amfani da na'urar farfaɗo da bugun zuciya amma bai farfaɗo ba.
"Har ma muna tunanin yana yin dabarar ne domin a kwance shi, amma daga baya sai muka gane cewa ba ƙarya ya yi ba," in ji Lola.