Jagororin Taliban huɗu da Kotun ICC ta bayar da sammacin kama su

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta fitar da ƙarin bayanai kan sammacin kama wasu manyan shugabannin Taliban da ta bayar a bara, ciki har da jagoran ƙungiyar, Haibatullah Akhundzada, da kuma shugaban Kotun Koli ta gwamnatin Taliban, Abdul Hakim Haqqani.

Cikakken bayanin sammacin ya kasance cikin sirri tun lokacin da aka bayar da shi, sai dai a ranar Litinin kotun ta bayyana sakamakon binciken alƙalan da suka amince da fitar da sammacin.

A gefe guda kuma, kakakin gwamnatin Taliban a Afghanistan, Zabihullah Mujahid, ya yi Allah wadai da matakin ta hanyar shafin sada zumunta na X, yana mai cewa gwamnatin Taliban ba ta amince da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ba, kuma ba ta ɗauki matsayinta da muhimmanci.

Mujahid ya ce: "Alhamdulillahi, shugabannin Daular Musulunci ta Afghanistan ba su aikata wani abu da ya cancanci kamawa ko hukunci ba. Wani muhimmin batu kuma shi ne mu bi dokokin Shari'ar Musulunci, ba waɗanda hukumomin leƙen asiri ko abin da ake kira kotuna suke ƙaƙaba mana ba."

A cikin sabuwar sanarwar da ta fitar, ICC ta ce Sashe na biyu na kotun wanda ke kula da matakin gabatar da ƙara kafin fara shari'a, ya yanke shawarar wallafa sammacin kama mutane huɗu da aka bayar a ranakun 8 ga Yuli da 9 ga Satumban 2025 dangane da shari'ar Afghanistan.

Kotun ta ce sammacin ya shafi

  • Haibatullah Akhundzada
  • Abdul Hakim Haqqani
  • Habibullah Agha da
  • Nida Mohammad Nadeem

Kotun ta ƙara da cewa an riga an sanar da wanzuwar sammacin farko biyu tun ranar 8 ga Yulin 2025.

Kotun ICC ta sanar a watan Yulin 2025 cewa ta gurfanar da wasu manyan jami'an Taliban biyu bisa zargin aikata "laifukan cin zarafin bil adama, ciki har da cin zarafi da danniyar jinsi kan 'yan mata da mata da sauran jama'a."

A cewar kotun, an aikata waɗannan laifuka ne tsakanin 15 ga Agustan 2021, lokacin da Taliban ta karɓi mulki a Afghanistan, zuwa aƙalla ranar 20 ga Janairun 2025.

Kotun ta kuma ce Taliban ta sanya masu rajin kare haƙƙin mata cikin jerin "abokan gaba na siyasa," tare da ƙaƙaba musu takunkumi da matakan danniya.

Alƙalan kotun sun kammala cewa waɗanda ake zargin sun aiwatar da wata manufar gwamnati da ta haifar da munanan take hakkokin al'ummar fararen hula na Afghanistan, ciki har da kashe-kashe da tsarewa a kurkuku da azabtarwa da fyade da kuma ɓatar da mutane.

Har ila yau, alƙalan sun ce duk da cewa Taliban ta kakaba tsauraran dokoki da takunkumai kan dukkan ƴan Afghanistan da matan da 'yan mata ne suka fi fuskantar waɗannan matakan.

A cewar alƙalan, an hana mata da ƴan mata haƙƙoƙinsu na samun ilimi, 'yancin faɗar albarkacin baki da kuma 'yancin zirga-zirga.

Kungiyar ta ce takunkuman da aka ƙaƙaba wa mata da ƴan mata kan harkokin ilimi da aiki da kuma shiga cikin al'amuran zamantakewa ba wai kawai sun tauye musu muhimman haƙƙoƙinsu ba ne, har ma suna yin mummunar illa ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Afghanistan.

Shin za a iya aiwatar da sammacin?

Idan har jagoran Taliban, Haibatullah Akhundzada, da shugaban Kotun Kolin gwamnatin Taliban, Abdul Hakim Haqqani, suka gurfana a gaban Kotun ta ICC, za a gurfanar da su bisa zarge-zargen da ake musu.

Idan kotun ta same su da laifi, za a yanke musu hukuncin ɗauri a wasu ƙasashen da ke cikin membobin ICC waɗanda suka amince da karɓar fursunonin kotun.

Bisa tanadin sashe na 77 na Yarjejeniyar Roma, kotun na iya yanke hukuncin ɗaurin shekaru har 30, ko kuma ɗaurin rai da rai a wasu lokuta.

Baya ga hakan, kotun na iya umartar a biya waɗanda abin ya shafa diyyar asara ko a mayar musu da haƙƙoƙinsu.

Zuwa yanzu, ICC ta fitar da sammacin kama mutum 61 da ake zargi da aikata manyan laifuka.

Daga cikinsu, an kama mutum 22 kuma an gurfanar da su a gaban kotun, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 30.

Kotun ICC tana da ƙasashe mambobi 124, waɗanda ke da alhakin aiwatar da umarni da hukuncin kotun bisa wajibcin da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa suka ɗora musu.

Saboda haka, idan wanda ake nema ya shiga ƙasar da ke cikin membobin kotun, ana sa ran a kama shi tare da miƙa shi ga kotun da ke birnin Hague na ƙasar Netherlands.

Sai dai a wasu lokuta, matsin lambar siyasa da diflomasiyya kan hana cikakken aiwatar da wasu sammacin kama, musamman waɗanda suka shafi shugabanni masu ƙarfi kamar Vladimir Putin da Benjamin Netanyahu.

Wasu ƙasashe kuma kan ƙi aiwatar da irin waɗannan umarni, yayin da ƙasashen da ba mambobin kotun ba ba su da wajibcin yin hakan.

Duk da waɗannan ƙalubale, ICC ta samu nasarar kama tare da gurfanar da wasu mutane da ake zargi da aikata manyan laifuka na ƙasa da ƙasa tare da haɗin kan ƙasashe mambobinta.

Abin da ke nuna cewa har yanzu kotun na da ikon hukunta masu aikata irin waɗannan laifuka a wasu lokuta.