Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sabbin hanyoyi 4 da Tinubu 'zai rage raɗaɗin' cire tallafin mai
Fiye da shekara uku bayan cire tallafin mai a Najeriya, tsadar fetur na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar gidaje, masu sana'o'i da masu harkokin sufuri.
Duk lokacin da farashin fetur ya tashi, farashin abinci, sufuri da sauran kayayyaki ma kan yi tashin gwauron zabi.
A cikin makonnin baya-bayan nan, hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya sake haifar da fargabar yiwuwar ƙarin farashin fetur a Najeriya.
Wannan ne ya sa Gwamnatin Tarayya ta fito da wasu sababbin matakai da ta ce za su taimaka wajen rage wa jama'a raɗaɗin tsadar mai ba tare da dawo da tallafin fetur da aka soke a watan Mayun 2023 ba.
A cewar Ministan Kudi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, a wata sanarwa da mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, gwamnati na son kare masu ƙaramin karfi daga matsin tattalin arziki, amma ba tare da komawa tsarin tallafin da ta ce ya jawo asarar biliyoyin naira ga kasar ba.
Rage farashin fetur na wata 1
Mataki na farko kuma wanda ya fi ɗaukar hankali shi ne wanda kamfanin NNPCL ya ɗauka na haƙura da ribar da yake samu daga sayar da fetur a gidajen mansa.
A ƙarƙashin sabon tsarin, idan kuɗin sauke ko samar da litar fetur ya kasance Naira 1,300, NNPCL za ta sayar wa jama'a da fetur kan wannan farashin ko kusa da shi ba tare da ƙara nata ribar kasuwanci ba.
Gwamnati ta ce wannan rangwamen zai fara aiki na tsawon kwana 30, kuma masu motocin haya za su kasance daga cikin waɗanda ake sa ran za su fi cin gajiyar tsarin.
A cewar gwamnatin, wannan ba tallafin mai ba ne saboda babu kuɗi daga baitul malin gwamnati da za a kashe wajen rage farashin. Maimakon haka, NNPCL ce ta rage wani ɓangare na ribar da take samu domin taimakawa masu amfani da fetur.
Dalilin wannan mataki shi ne rage matsin da tsadar fetur ke yi wa direbobi da masu safarar jama'a.
Idan direbobi sun samu mai a dan rahusa, gwamnati na fatan hakan zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri ko kuma aƙalla hana ƙarin kuɗin sufuri a lokacin da farashin ɗanyen mai ke tashi a kasuwannin duniya.
Kafa manyan ma'adinan fetur
Wani sabon tsari da gwamnati ta sanar shi ne kafa abin da ta kira National Strategic Fuel Reserve, wato manyan ma'adinan fetur na kasa.
A baya, Najeriya ta sha fuskantar ƙarancin fetur saboda matsalolin samar da shi ko kuma saboda wasu ƴan kasuwa sun ɓoye man domin ƙara farashi. Irin waɗannan yanayi kan janyo dogayen layuka a gidajen mai tare da hauhawar farashi.
Don magance wannan matsala, gwamnati na shirin tara wani adadin man fetur da za a riƙa ajiyewa domin amfani da shi a lokacin da aka samu wata matsala a kasuwannin duniya ko kuma lokacin da ake fuskantar karancin fetur a cikin gida.
A cewar gwamnatin, idan aka samu rikici a ƙasashen da ke samar da mai ko matsalolin kasuwanci da suka sa fetur ya yi ƙaranci, za a iya sakin wani ɓangare na wannan ajiyar zuwa kasuwa domin tabbatar da wadatar mai.
Gwamnati ta ce wannan tsarin ba zai ƙayyade farashi ba kuma ba tallafi ba ne. Manufarsa ita ce tabbatar da wadatar fetur, hana ƙirƙirar ƙaranci ta bogi da kuma rage yawan tashin farashin da ba dole ba.
Masana tattalin arziki sun dade suna ganin cewa ƙasashen da ke da manyan ma'adinan makamashi sun fi samun kariya daga matsalolin kasuwannin duniya fiye da waɗanda ba su da irin wannan tanadi.
Haɓaka aika saƙonni ta Post Office
Ko da yake mutane da yawa ba sa danganta cunkoson hanya da farashin fetur, gwamnati na ganin cewa akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu.
A manyan biranen Najeriya kamar Legas, Abuja, Kano da Fatakwal, motoci na iya ɗaukar sa'o'i suna tsaye a cunkoson ababen hawa. A irin wannan lokaci kuwa, motoci na ci gaba da amfani da fetur ba tare da yin tafiya mai nisa ba.
Saboda haka, gwamnati ta ce hukumomin kula da zirga-zirga za su ƙara ƙaimi wajen rage cunkoso domin rage yawan man da ake kashewa a hanya.
Hakazalika, gwamnati ta ce sabon tsarin lambobin adireshi da NIPOST ta ƙaddamar zai taimaka wajen sauƙaƙa aiken kaya zuwa wurare, kamar yadda ake yi a shekarun baya.
A ƙarshe, hakan na iya taimakawa wajen rage farashin kayayyaki saboda kuɗin sufuri na daga cikin abubuwan da ke kara tsadar kaya a kasuwa.
Faɗaɗa amfani da CNG
Wata muhimmiyar hanyar da gwamnati ke ganin za ta taimaka wajen rage tasirin tsadar fetur ita ce ƙara yawan motocin da ke amfani da iskar gas ta CNG.
Tun bayan cire tallafin mai, gwamnati ta ɗora muhimmanci kan sauya wasu motocin sufuri daga amfani da fetur zuwa CNG.
A cewar gwamnati, CNG na da araha sosai idan aka kwatanta da fetur, inda kuɗin amfani da shi ke iya zama ƙasa da na fetur da kashi 60 zuwa 70 cikin 100.
Idan ƙarin motocin haya, motocin gwamnati da na kasuwanci suka koma amfani da CNG, kuɗin tafiya zai ragu sosai. Wannan kuma zai taimaka wajen rage nauyin da tsadar fetur ke ɗorawa masu zirga-zirga a kullum.
Sai dai akwai ƙalubalen samar da isassun tashoshin CNG da kuma kuɗin sauya motoci zuwa tsarin amfani da iskar gas. Duk da haka, gwamnati ta ce tana aiki tare da jihohi da masu zuba jari domin gaggauta fadada amfani da wannan makamashi.
Abin da ya rage
Dukkan waɗannan matakai sun fito ne a lokacin da gwamnati ke fuskantar matsin lamba daga jama'a kan tsadar rayuwa.
Duk da cewa gwamnati ta amince cewa cire tallafin mai ya jawo wahala ga mutane da yawa, tana cewa komawa tsohon tsarin tallafi zai iya jawo matsalolin da Najeriya ta taba fuskanta kamar ƙarancin mai, fasakwauri da sauran su.
Saboda haka, maimakon dawo da tallafin fetur, gwamnati ta ce rage tasirin tsadar mai ta waɗannan hanyoyin za su yi kyau
Tambayar da ta rage ita ce ko waɗannan matakai za su kai ga raguwar kuɗin mota, farashin kayan abinci da sauran buƙatun yau da kullum da miliyoyin ƴan Najeriya ke jiran gani a zahiri.