Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda kogi ya tafi da yara uku ƴan gida ɗaya a Abuja
Wani mummunan ibtila'i ya auku a yankin Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja, inda wasu yara uku 'yan gida ɗaya suka rasa rayukansu bayan ruwa ya tafi da su a wani kogi.
Mahaifin yaran Architect Aliyu Abubakar mazaunin rukunin gidaje na El-Rufai da ke Kuje ya ce al'amarin ya faru ne ranar 1 ga watan Oktoba a lokacin da dukkannin ƴan makaranta ke hutu.
Yaran dai su uku mabiyan juna ne a haihuwa Maryama mai shekara 12 da Umaru mai biye mata da ke da shekara 10 sai kuma ƙaramar Hanifa mai shekara 8.
An ce ganin abin da ya faru ya sa sauran 'yan'uwansa biyu suka yi yunƙurin cetonsa, amma ƙoƙarinsu ya ci tura yayin da su ma ruwa mai ƙarfi ya ja su cikin kogin.
Yadda haɗarin ya faru
Architect Aliyu Abubakar wanda shi ne mahaifin yaran ya shaida wa BBC cewa yaran nasa sun haɗu tare da na maƙwabta suna ta wasa sakamakon babu makaranta a ranar inda har ta kai sun nemi izinin mahaifiyarsu domin su fita zuwa waje.
"Iyayen sun hana su fita amma da suka ka ga sun dame su sai suka aike su zuwa Freedom Estate domin su sayo musu Kunun Aya....To haka yaran nan suka taka har zuwa kimanin mita 400 zuwa kogin nan da ke bayan Estate ɗinmu," in ji mahaifin yaran.
Daga nan kuma sai ƙaramin ƙanen ya fara shiga ruwan Kogin wanda yake da ƙarfi sakamakon ruwan sama da aka yi kwana daya kafin nan.
"Ƙaramar ƴartawa sai ta je ta shiga tana wasa a baki-baki, sauran kuma suna ta wasa ba su shiga ruwan ba...Kawai sai ɗan uwanta ya ga yarinyar nan ta fara nutsewa a cikin ruwan nan. Shigar da ya yi ya kamo ta sai shi ma ruwan ya ja shi. Ita kuma babbar ƴar tawa tana daga nesa sai ta fito a guje saboda ta ga ruwan ya fara tafiya da su sai ta shiga ruwan domin neman ceto yaran guda biyu amma gabaɗaya Allah ya sa ruwan nan ya cinye su," in ji Architect Aliyu Abubakar.
Ƙoƙarin ceto gawarwaki
Architect Aliyu Abubakar ya ƙara da shaida wa BBC cewa jim kaɗan bayan fadawar yaran nasa cikin kogin sai wani dattijo wanda ke kusa da wurin lokacin da al'amarin ya faru ya nemi kai musu ɗauki.
"Akwai wani mutum da ke motsa jiki a kusa da wurin ya yi ƙoƙari domin har ya samu ya kamo hannun ita wannan yarinya ta ƙarshe to amma shi ma da yake bai iya ruwa ba kuma dattijo ne da ya manyanta sai ya ƙyale ta.
To amma ya nemi taimakon mutane inda kuma aka je wurin amma tuni ruwan ya tafi da su. Haka aka ci gaba da nema ta hanyar amfani da katakai da rassan bshiya da waɗanda suka iya ruwa amma dai Allah bai sa za a gan su ba har zuwa ƙarfe 12 na dare ba a same su ba a ranar.
"To haka washegari da safe mun yi amfani da masunta daga Kuje har zuwa Gwagwalada amma sai zuwa ƙarfe 5 na yammar ranar aka tsinci gawar ƙaramar da ta fara.
Sai kuma bayan kwana biyu aka sake tsintar gawar babbar a can Payi gaban Kwali wanda cikin jihar Neja ne. Shi kuma namijin har yanzu Allah bai nuna mana gawar Umaru ba kwanaki fiye da bakwai...," in ji mahaifin mamatan.
'Maryama mahaddaciyar Al-Qur'ani ce'
Architect Aliyu Abubakar ya ce akwai ƙauna da shaƙuwa sosai tsakaninsa da yaran nasa.
"Ita Maryama zuwanta kenan daga Kano inda ta yi haddar Al-Qur'ani kuma dawowarta ce ta sa yaran suke ta farin ciki suna ta ɗaukar hotuna.
Wadannan yara mun shaƙu sosai. Lokacin da na samu labarin rasuwar tasu na yi kuka na yi kuka. Amma kuma Allan da ya ba mu shi ne ya dauke su.
Lokacin da ya ba mu su ba mu san su ba. Bai yi shawara da mu ba. Shi ne kuma a yanzu ya ɗauki kayansa a lokacin da ya ga dama kuma ba sai ya yi shawara da mu ba.
Lallai muna yi wa Allah godiya da damar da ya ba mu muka haife su kuma muka tarbiyyantar da su har zuwa wannan lokaci," in ji mahaifin yaran, Architect Aliyu Abubakar.