Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴansiyasa 5 da suka yi wa Tinubu alƙwarin miliyoyin ƙuri'u a 2027
A yayin da ake ƙara tunkarar babban zaɓen Najeriya na 2027, wasu fitattun ƴan siyasa da ƙungiyoyi masu tasiri sun fara bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda wasu ma ke yi masa alƙawarin miliyoyin ƙuri'u daga yankuna da sassa daban-daban na ƙasar.
Daga arewacin ƙasar zuwa kudanci, an ji alƙawuran da suka kai miliyoyin ƙuri'u, yayin da wasu masu ruwa da tsaki ke cewa za su tabbatar da gagarumar nasara ga shugaban ƙasar.
Sai dai duk da irin waɗannan alƙawura masu ɗaukar hankali, tambayoyin da ake yi sun haɗa da irin tasirin waɗanda suka yi su, da kuma ko za su iya cika alkawurran nasu idan lokacin zaɓe ya yi.
A wannan muƙala za mu duba wasu daga cikin manyan alƙawuran ƙuri'un da aka yi wa Tinubu, da kuma yiwuwar tabbatuwarsu a zahiri.
Bello Matawalle - ƙuri'a miliyan 20
Ɗaya daga cikin ƴansiyasa na gaba-gaba da suka yi wa Tinubu alƙawarin ƙuri'u shi ne ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Bello Matawalle da ya ce zai samar wa Tinubu ƙuri'a miliyan 20.
Matawalle ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen kafa wata ƙungiyar siyasa mai suna 'Tinubu Agai' a Abuja.
Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya ce ya kafa ƙungiyar ne da nufin samar wa shugaban ƙasar goyon bayan masu kaɗa ƙuri'a daga tushe.
"Dole ne mu je ga jama'a domin wayar musu da kai, mu sanar da su irin abubuwan da wannan gwamnati ke yi, da abubuwan da Bola Ahmed Tinubu ke yi wa al'umma, da shirye-shiryensa da manufofinsa da hangen nesansa, da kuma abin da yake da niyyar yi wa 'yan Najeriya," in ji Matawalle.
Bagudu Network for Tinubu - miliyan 19
Baya ga Matawalle, wata ƙungiyar siyasa mi suna 'Atiku Bagudu Grassroots Network for Tinubu 2027' ita ma ta yi wa Tinubu Alƙawarin samar masa ƙuri'a miliyan 19 daga jihohin arewacin ƙasaar 19.
Ministan Kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ne a matsayin uban ƙungiyar.
Shugaban ƙungiyar, Hon Ali Oriri, ya ce ƙungiyar za ta faɗaɗa ayyukanta a faɗin arewacin ƙasar domin samar wa Tinubu goyon bayan masu zaɓe tundaga tushe.
A makon da muke ciki ne ƙungiyar ta yi zamanta a Abuja da nufin ƙarfafa yadda za ta tunkari wannan aiki da ke gabanta domin cika alƙawarin da ta ɗauka.
Tunji Alausa - ƙuri'a miliyan 10
Wani ɗansiyasar da ya yi wa Shugaba Tinubu alƙawarin ƙuri'a shi ne ministan ilimin ƙasar, Tunji Alausa da ya yi masa alƙawarin ƙuri'a miliyan 10.
Ministan ya yi wannan alƙawari ne a ranar Talata yayin taron farko na Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, ɓangaren ilimi, inda ya yi kira da a ƙaddamar da gangamin wayar da kai a faɗin ƙasar domin samun goyon bayan shugaban ƙasa daga ɗalibai, malamai, malaman jami'o'i da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.
Ministan ya ce ɓangaren ilimi, kasancewar yana da faffaɗan cibiyoyi da mambobi a sassan ƙasar, yana da damar samar da gagarumin yawan ƙuri'u ga Bola Ahmed Tinubu.
"Idan muka yi aiki tuƙuru, ya kamata mu iya tara ƙuri'u miliyan 10 daga ɓangaren ilimi kaɗai ga shugaban ƙasa," in ji shi.
Gwamnan Edo - ƙuri'a miliyan 2.5
Jam'iyyar APC ta jihar Edo, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Monday Okpebholo sun yi alƙawarin samar wa Tinubu ƙuri'a miliyan 2.5 daga jihar.
Mista Okpebholo ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wani gangamin tattara magoya baya ga jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Ikpoba-Okha, inda ya gabatar da 'yan takarar jam'iyyar domin zaɓukan 2027.
"Jam'iyyar APC ta gina ingantaccen tsari a faɗin jihar, kuma tana cikin kyakkyawan matsayi gabanin gudanar da zaɓukan."
Ya ƙara da cewa jam'iyyar na da ƙwarin gwiwar samun nasarar sakamakon yadda ta kafa ginshiki mai ƙarfi a matakin ƙasa da na ƙananan hukumomi.
Ɗantakarar gwamnan Ogun - ƙuri'a miliyan biyu
Wani ɗansiyasar da ya yi wa Tinubu alƙawarin ƙuri'a shi ne ɗantakarar gwamnan jihar Ogun na jam'iyyar APC, Sanata Adeola Olamilekan, da ya yi wa Tinubu alƙawarin ƙuri'a miliyan biyu a zaɓen na 2027.
Yayin da yake jawabi yayin bikin ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar City Boy Movement na jihar, Sanata Olamilekan, wanda aka fi sani da Yayi, ya a shirye yake don tallafa wa ƙungiyar wajen samar wa Tinubu ƙuri'un a faɗin jihar.
"Jihar Ogun na da sama da masu rajistar zaɓe miliyan uku, kuma da wannan adadi, ina ganin ya kamata mu ba wa Shugaba Tinubu aƙalla ƙuri'u miliyan biyu a zaɓen 2027," in ji Olamilekan.
Shin alƙawura za su iya tabbata?
Masana siyasa na ganin da wahala irin waɗannan alƙawura su iya tabbata kasancewar, wasunsu ma sun zarta tunani.
A zaɓen 2023 da ya gabata Tinubu ya yi nasara da ƙuri'a miliyan takwas da ɗoriya ne, cikin jimillar ƙuri'u ƙasa da miliyan 25.
Lamarin da ya sa wasu masu sharhin siyasa ke kallon wannan ikirari a matsayin kamalam siyasa.
Dr Kabiru Sa'id Sufi, Malami a Ƙwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasar ƙasar ya ce neman fada ce ta saka ƴansiyasar yin wannan iƙirari.
''Jawabai ne na siyasa kowannensu na ƙoƙari ne na burge ubangidansa domin samun fada'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ƴansiyasar sun yi iƙirarin ne ba tare da la'akari da yawan masu rajistar zaɓe da johohin ke da su ba.
''Idan aka duba ƙididdigar yawan masu rajistar zaɓe da INEC ta fitar a baya-bayan nan za a fahimci cewa yawan masu rajistar zaɓe a wasu johohin ma bai kai adadin ƙuri'un da ƴansiyasar suka yi wa Tinubun alƙawari daga jihohin nasu ba'', in ji masanin siyasar Najeriyar.
Ya ci gaba da cewa wannan kawai jawabai ne na siyasa da ƙarfafa gwiwa, amma ba abu ne da zai tabbata ba.
Me sa ya ƴansiyasa ke irin waɗannan alƙawura?
Dokta Kabiru Sufi ya ce akwai dalilai kamar uku zuwa huɗu da ke sa ƴansiyasar yin irin waɗannan alƙawura.
- Neman fada a wajen shugaban ƙasa
- Ƙarfafa gwiwa ga magoya bayansu
- Ƙara wa kansu matsayi a siyasance
- Idan an samu sakamako mai kama da haka, kada mutane su yi mamaki.
Ya ƙara da cewa mafi yawan ƴansiyasar suna yin wannan alƙawura ne domin tanadin gaba.
''Wato idan an ci zaɓe a yi tafiyar gwamnati da su'', in i shi.