Ya dace ma'aikatan gwamnati su goyi bayan wani ɗantakara?

Asalin hoton, X/Multiple
Yayin da ake ƙara kusantar lokacin zaɓe a Najeriya, tambayoyi kan irin rawar da ma'aikatan gwamnati za su iya takawa a harkokin siyasa na ci gaba da tasowa.
Kodayake Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa ƴan ƙasa wasu haƙƙoƙi na siyasa, akwai kuma ƙa'idoji da dokoki da ke tsara yadda ma'aikatan gwamnati za su yi domin tabbatar da cewa aikin gwamnati ya kasance ɗanb ba ruwanmu ba tare da son rai ba.
A lokuta da dama, ana samun muhawara game da ko ma'aikatan gwamnati na da damar nuna ra'ayinsu na siyasa a fili ko shiga yaƙin neman zaɓe ko kuma bayyana goyon baya ga wani ɗan takara ko jam'iyya yayin da suke kan mukamansu.
Masana na cewa fahimtar bambancin da ke tsakanin haƙƙin ɗan ƙasa da kuma wajibcin ma'aikacin gwamnati na da muhimmanci, musamman a lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar hankali kafin zaɓe.
To amma mene ne dokokin Najeriya da ƙa'idojin aikin gwamnati suka tanada kan shiga siyasa ga ma'aikatan gwamnati?
Shin doka ta hana su bayyana goyon baya ga wani ɗan takara ko jam'iyya, ko kuwa akwai wasu iyakoki ne kawai da aka sanya?
BBC ta tattauna da masana kan abin da doka ta ce da kuma yadda ake fassara waɗannan tanade-tanade a aikace.
Wane ne ma'aikacin gwamnati?
Ma'aikacin gwamnati shi ne mutum da ke aiki a wata ma'aikata, hukuma ko cibiyar gwamnati ta tarayya, jiha ko ƙaramar hukuma, kuma albashinsa na fitowa daga kuɗaɗen gwamnati.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Aikin irin waɗannan ma'aikata shi ne aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati tare da yi wa jama'a hidima.
A Najeriya, ma'aikatan gwamnati na gudanar da ayyuka daban-daban da suka shafi ilimi da lafiya da noma da shari'a da tsaro da sauran fannoni na rayuwar al'umma.
Sai dai ba duk wanda gwamnati ta naɗa ake ɗauka a matsayin ma'aikacin gwamnati ba.
Masana kan bambanta tsakanin ma'aikatan gwamnati na dindindin, waɗanda ake ɗauka aiki bisa ƙa'idojin aikin gwamnati, da kuma masu muƙaman siyasa kamar ministoci, kwamishinoni da shugabannin hukumomi, waɗanda galibi ake naɗa su ne bisa dalilan siyasa.
Saboda rawar da ma'aikatan gwamnati ke takawa wajen yi wa gwamnati da jama'a hidima, an tanadi ƙa'idoji da dokoki da ke buƙatar su kasance masu adalci da tsayawa a tsakiya wajen gudanar da ayyukansu.
Wannan ne ya sa ake yawan tattaunawa kan iyakar shiga harkokin siyasa da kuma bayyana goyon baya ga 'yan takara ko jam'iyyun siyasa yayin da suke aiki a gwamnati.
Me doka ta tanadar wa ma'aikacin gwamnati kan goyon bayan ɗantakara ko jam'iyya?
Barista Sanusi Musa SAN, babban lauya ne mai zaman kansa, kuma masanin dokokin Najeriya, ya ce a ƙarƙashin dokokin Najeriya kowane ɗan ƙasa na da dama shiga siyasa, ciki har da bayyana ra'ayinsa kan jam'iyya ko ɗan takara tare da nema musu ƙuri'un mutane.
''Chapter 4 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi wasu manya-manyan haƙƙoƙin ɗan'adam cki har da bayyana ra'ayi na siyasa, kuma ba a keɓe wani mutum ba'', in ji shi.
Babban lauyan ya ce a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya ma'aikacin gwamnati ba a hana shi shiga siyasa ba.
''Dokokin Najeriya ba su hana ma'akacin gwamnati tallata jamma'iyyar da yake so ko ɗantakara ba, ba a hana shi yi mata yaƙin neman zaɓe ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Masanin dokokin Najeriyar ya ƙara da cewa abin da doka ta haramta wa ma'aikacin gwamnati game da siyasa shi ne ba zai tsaya takara ba matsawar yana aiki, sai idan ya ajiye aikinsa.
Ko shigar ma'aikata siyasa zai shafi ingancin aikin?
Wasu da dama na ganin shigara ma'aikatan gwmanati harkokin siyasa zai shafi ingancin aikin da aka ɗora musu.
Inda ma wasu ke fargabar gwmanati a ta iya fifita ma'aikatan da ke goyon bayan jam'iyyarsu fiye da waɗanda ba sa goyon baya, koda kuwa ba su cancanta ba.
To amma Barista Sanusi Musa SAN ya ce in da matsalar take shi ne rashin kishin ƙasa tsakanin ƴan Najeriya, amma abubuwa ne mabambanta.
''Shigarka siyasa daban; kuma aikin gwamnatinka daban idan kana da kishin ƙasa, don kana siyasa, ya kamata ka san ra'ayinka ne ba wanda ya isa hanaka, amma idan aka zo ɓangaren aikin gwamnatinka ya kamata ka yi abin da aka ɗora maka na aiki''.
Ya ƙara da cewa don kana siyasa bai dace ba ka bar ra'ayinka na siyasa na wuce kima ta yadda za ka fitar da sirrin gwamnati ko yi wa aikinka zagon ƙasa.
''To wannan shi aka rasa, an tsara kundin tsarin mulkin Najeriya da tunanin cewa kowane ma'aikacin gwamnati zai zama mai kishin ƙasa da kiyaye dokoki'', in ji ƙwararren lauyan
































