Yadda Chadi ta yi watsi da shirin Nijar na korar Larabawan Mahamid

.
Bayanan hoto, .
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Mahukuntan Chadi sun mayar da martani kan matakin da maƙwabciyarsu Nijar ta ɗauka na bai wa al'ummar Larabawan Mahamid wa'adin watanni biyu su fice daga ƙasar.

A makon da ya gabata ne hukumomin Nijar suka umarci al'ummar da su bar ƙasar kafin ranar 31 ga Disamban 2026.

Martanin Chadi ya zo cikin gaggawa.

Da BBC ta tuntuɓi hukumomin Chadi, sun bayyana cewa ba za su karɓi dubban Larabawan Mahamid da ke fuskantar barazanar kora daga Nijar kai tsaye ba, sai an tantance asalin ƙasar kowannensu daban-daban kafin a amince da karɓar su.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Chadi ta bayyana cewa za ta tsaurara matakan tsaro a kan iyakokinta, kuma mutanen da aka tabbatar 'yan ƙasar Chadi ne kaɗai za a bari su shiga ƙasar.

Ta ce "Za a bari 'yan ƙasar Chadi da aka tantance su koma gida, yayin da za a duba sauran lamurra daban-daban bisa yanayin kowannensu."

Dubban Larabawan Mahamid ne ke zaune a Nijar, musamman a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin ƙasar. Da dama daga cikinsu sun shafe shekaru da dama a yankin, inda iyalai na farko suka fara zuwa daga Chadi da Sudan a shekarun 1970.

Hukumomin Nijar ba su bayyana inda suke son wannan al'umma ta koma ba. Sai dai Ma'aikatar Harkokin Wajen Chadi ta shaida wa BBC cewa bai kamata a ɗauki mambobin al'ummar a matsayin 'yan ƙasar Chadi kai tsaye saboda asalinsu na ƙabilanci ba.

Makiyayan Larabawan na tattara kayansu, yayin da suke jiran korarsu daga sansanin N’Gortogole da hukumomin Nijar suka shirya yi a ranar 27 ga Oktoban 2006.

"Larabawan da ake magana a kansu 'yan Nijar ne."

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Larabawan da ake magana a kansu 'yan Nijar ne. An haife su a Nijar, sun rayu a can tsawon rayuwarsu kuma tushensu yana cikin ƙasar. Kasancewarsu cikin wannan al'umma ta ƙabila ba hujja ba ce da za ta tabbatar da cewa 'yan ƙasar Chadi ne," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa ya kamata Nijar ta bi hanyoyin shari'arta wajen hukunta duk wanda ake zargi da hannu a ayyukan da ke barazana ga tsaron ƙasar.

"Nijar dole ne ta sauke nauyin da ke kanta. Idan ana zargin wasu mutane da yunƙurin haddasa rashin zaman lafiya a ƙasar, to ya kamata su fuskanci shari'a a gaban kotunan Nijar. Laifin aikata laifi na mutum ne, kuma hakan ba ya halatta a kori al'umma gaba ɗaya daga muhallinta," in ji sanarwar.

Hukumomin Chadi sun kuma nuna damuwa kan yadda dubban mutane ke zaune a Nijar ba tare da ingantattun takardun izinin zama a ƙasar ba.

A 'yan shekarun nan, hukumomin Nijar sun ɗauki matakai kan wannan al'umma, lamarin da ya janyo damuwa tsakanin ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama kan yiwuwar nuna musu wariya da kuma haɗarin korar al'umma gaba ɗaya daga ƙasar.

Me ya sa Nijar ke son korar Larabawan Mahamid daga ƙasar?

Des Arabes nomades en fuite rassemblent du bétail au camp de N’Gortogole, anticipant leur expulsion par les autorités nigeriennes le 27 octobre 2006.

Gwamnatin Nijar ta bai wa al'ummar Larabawan Mahamid wa'adin kasa da watanni biyu su fice daga ƙasar kafin ƙarshen wannan shekara.

Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa shugaban yankin Diffa, Mamoudou Bonkano Abdoul Salam, ne ya sanar da wannan mataki a ranar Asabar, yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin gargajiya a garin Chetimari.

Ya bayyana cewa manyan hukumomin ƙasar ne suka sanya wa'adin, tare da kira ga shugabannin al'ummar da su sanar da sauran mambobinsu tare da tabbatar da cewa sun bi umarnin.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan matsalar tsaro a yankin Diffa, inda Nijar ta kwashe sama da shekaru goma tana yaƙi da ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi, ciki har da Boko Haram da ɓangaren da ya balle daga cikinta mai suna Islamic State West Africa Province (ISWAP).

Hukumomin yankin Nijar sun riga sun zargi wasu mambobin al'ummar Mahamid da hannu wajen safarar makamai da kuma samar da tallafin kayan aiki ga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Al'ummar Mahamid, waɗanda asalinsu daga Chadi ne, sun yi ƙaura zuwa kudancin Nijar shekaru da dama da suka gabata, inda da yawa daga cikinsu suka zauna a yankin na tsawon shekaru.