An ci gaba da musayar wuta tsakanin Saudiyya da Houthi

Asalin hoton, Getty Images
An sake samun musayar wuta a tsakanin Saudiyya da kuma 'yan tawayen Houthi a Yemen.
Mahukuntan Saudiyya sun ce sun daƙile wani harin makami mai linzami da aka kai kan birnin Riyadh, sai dai rahotanni sun nuna tarkacen makamin da ya faɗo ya haddasa ɓarna a wasu wurare.
A nasu ɓangaren, ƙungiyar Houthi ta ce jiragen yaƙin Saudiyya sun kai hare-haren sama kan babban birnin Yemen, Sanaa.
Tun da farko Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya gana da babban kwamandan rundunar sojin Amurka a yankin, Admiral Brad Cooper, inda suka tattauna kan halin da ake ciki.
Faɗan da ake tsakanin ƙawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta da kuma mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran ya ƙara tsananta a watan jiya.

