Ni ne zan jagoranci gwamnatina, ba kamar Buhari ba - Peter Obi

Peter Obi
    • Marubuci, Madina Maishanu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News.
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ɗantakarar shugaban Najeriya na jam'iyyar NDC, Peter Obi ya bayyana yadda zai tunkari wasu manyan matsalolin da ƙasar ke fuskanta idan ya samu nasarar lashe zaɓen 2027 da ke tafe.

Cikin hirarsa da BBC, Peter Obi, wanda ya zo na uku a zaɓen 2023 ya nanata iƙirarin cewa shi ne ya lashe zaben 2023 da ya gabata, duk da cewa babu wata hujjar hakan da ya bayyana wa BBC.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya jaddada cewa wa'adi ɗaya zai yi idan ya samu nasarar a zaɓen 2027 da ke tafe.

A lokacin da jam'iyyar NDC ya sanar da miƙa wa yankin kudancin Najeriya takarar 2027, ta tabbatar da cewa wa'adi ɗaya shugabanci zai yi a kudancin ƙasar, sannan a mayar da shi arewaci.

''Ba zan ƙara ko kwana ɗaya bayan shekara huɗu'', kamar yada ya shaida wa BBC.

A cikin tattaunawar Mista Obi ya bayyana wa BBC yadda zai tunkari wasu manyan matsalolin ƙasar hudu.

Matsalar tsaro

Matsalar tsaro na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ci wa Najeriya tuwo a ƙwarya, inda ƴanbindiga ke kai hare-hare tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

To amma Peter Obi ya ce zai ɓullo da sabuwar hanyar magance matsalar, wanda ta ƙunshi tarewa a yankunan da suka fi fama da matsalar har zuwa lokacin ƙarewarta.

''Abin da ake buƙata shi ne shugaban ƙasa ya ƙudiri aniyar cewa wannan abin zai ƙare'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa zai je cikin al'umomin da matsalar ta shafa domin gano masu aikata laifin ta hanyar zuwa garuruwan da kansa.

''Zan je garuruwan da kaina, ba zai yiwu a sace mutum 600 a Neja, sannan na ci gaba da zama a Abuja ba, zan tare a Minna tare da jami'an soji domin tabbatar da ƙwato su'', in ji shi,

Peter Obi ya ce idan ya zama shugaban ƙasa ko hutu ƙasashen waje ba zai je ba, koda na kwana ɗaya ne.

''Zan yi tafiya ne kawai saboda wasu dalilai na aiki, zan tabbatar da na je wuraren da ke fama da matsalar tsaro'', in ji shi.

Tallafin man fetur

Batun tallafin man fetur na daga cikin manyan batutuwan da ke jan hankali a zaɓen 2027 da ke tafe.

A baya-bayan nan ɗantakarar ADC, Atiku Abubakar ya jaddada aniyarsa ta maido da tallafin idan har aka zaɓe shi a 2027, wani matsayi da bai yi wa gwamnatin APC daɗi ba.

Peter Obi na daga cikin mutanen da a baya ya riƙa sauya matsaya kan batun na tallafin man fetur.

Sai dai a yanzu ya ce shi bai taɓa sauya matsaya kan batun tallafin man fetur ba.

''Cin hanci da rashawa ne babbar matsalar da ke tattare da tallafin man fetur, wannan shi ne abin da ya jefa Najeriya cikin matsala''.

Ya ce abin da zai yi shi ne kawar da cin hanci da rashawa a fannin tallafin na man fetur.

''Abin da zan yi shi ne zan dawo da tallafi, amma zan cire duka cin hancin da ake yi a cikinsa, wannan ita ce matsayata'', in ji shi ɗantakarar shugaban ƙasar na NDC.

Cin hanci da rashawa

Cin hanci da rashawa ya kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ƴantakarar shugaban Najeriya ke yaƙin neman zaɓe da su cikin gomman shekaru.

Gwamnatoci daban-daban sun kafa hukukomin yaƙi da matsalar, amma har yanzu tana ci gaba da haifar da mummunan koma-baya ga tattalin arzikin ƙasar.

Peter Obi ya ce zargi gwamnatocin baya da sakaci wajen yaƙi da matsalar.

Ɗaya daga cikin gwamnatocin da suka yi fice a iƙirarin yaƙi da cin hanci, ita ce gwamnatin Buhari, wadda ita ma aka kama wasu daga cikin jami'anta bisa zargin cin hancin.

Amma Peter Obi ya zargi Buhari da rashin cikakken iko da gwamnatinsa.

''Shi Buhari ya kasance ba shi da cikakken iko da gwamnatinsa, ni kuma zan kasance mai cikakken iko da gwamnati na'', kamar yadda ya bayyana.

'Matsayata kan dunƙulewar ƴan'adawa'

Dangane da yunƙurin da wasu ƴan hamayyar ƙasar ke yi don ganin cewa jam'iyyun hamayyar sun dunƙule wuri guda don mara wa ɗan takarar hamayya ɗaya baya da nufin kawar da Tinubu na APC, Obi ya ce yana da matsaya ta daban.

Ya ce ya kamata ƴan hamayya su mayar da hankali kan yadda za a samar da ƙarin masu zaɓen miliyan 25.

Da aka tambaye shi ko zai janye idan ƴanhamayya suka dunƙule domin goyon bayan wani ɗantakarar da ba shi ba, sai ya ce abin da ake buƙata shi ne a yi abin da ya dace.

''A bar mutane su yi zaɓinsu, ki yi tunanin wani ya samu ƙuri'u miliyan 25 ɗin nan, zai lashe zaɓen kenan'', in ji shi.

A baya-bayan nan ana yawan samun ƙungiyoyin da ke kiraye-kiraye ga ƴan hamayyar ƙasar su dunƙule wuri guda domin mara wa ɗantakara ɗaya baya.