Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne gilashin Meta da ake amfani da shi wajen naɗar bidiyo a asirce?
Akwai na'urorin zamani da mutum zai iya amfani da su wajen ɗaukar hotuna ko bidiyo ba tare da ya riƙe waya ko kyamara a hannu ba.
Wasu daga cikinsu suna ba mutum damar yin hakan cikin sauƙi ba tare da waɗanda ke kusa da shi sun fahimci abin da yake yi ba.
Ɗaya daga cikin irin waɗannan na'urori shi ne gilashin zamani na Meta, wanda aka ƙera ta yadda mutum zai iya ɗaukar hotuna da bidiyo ta hanyar amfani da shi kamar yadda yake amfani da gilashin ido.
To amma mene ne ainihin gilashin Meta, ta yaya yake aiki kuma shin da gaske mutum zai iya amfani da shi wajen ɗaukar bidiyon wasu ba tare da saninsu ba?
Abubuwan da ke jikin gilashin
Gilashin Meta, wanda aka fi sani da Ray-Ban Meta Smart Glasses, wani nau'in gilashi ne mai amfani da fasahar zamani, wanda kamfanin Meta ya ƙera tare da haɗin gwiwar kamfanin Ray-Ban.
Shi ba kamar gilashin ido na yau da kullum ba ne, wannan gilashi yana ɗauke da ƙaramar kyamara da makirufo, waɗanda ke ba mai amfani damar ɗaukar hotuna da bidiyo, yin kira, sauraron kiɗa da kuma amfani da wasu fasahohin ƙirƙirarriyar basirar AI.
Abin da ya bambanta shi da kyamarar waya shi ne, mutum na iya ɗaukar bidiyo daga inda idanunsa ke kallo, ba tare da ya riƙe waya ko wata kyamara a hannunsa ba.
Sai dai wannan fasaha ta haifar da muhawara sosai kan yadda za a kare sirrin mutane, musamman game da yiwuwar amfani da gilashin wajen ɗaukar hotuna ko bidiyon wasu ba tare da izininsu ba.
Ga wasu daga cikin abubuwan da ke jikin gilashin:
- Ƙaramar kyamara: Gilashin na da kyamarar megapixel 12. Sabbin nau'ikansa na iya ɗaukar bidiyo mai ingancin 3K Ultra HD, wanda ke ba da damar samun hotuna da bidiyo masu tsafta da kuma cikakkun bayanai.
- Ma'ajiyar bayanai: Yana da ma'ajiyar bayanai ta 32GB, wadda ke ba shi damar adana hotuna da bidiyo kafin a tura su zuwa waya.
- Lasifika: Yana da ƙananan lasifika da ke ba mai amfani damar sauraron kiɗa, labarai da amsa kiran waya ba tare da sanya na'urar sauraro a kunnuwansa ba.
- Makirufo: Yana da makirufoni da ke ɗaukar muryar mai amfani yayin kira da sauran ayyukan na'urar.
Wannan nau'in gilashi na ƙara samun karɓuwa a kasuwannin duniya, inda wasu mutane ke amfani da shi saboda sauƙin da yake bayarwa wajen sadarwa da kuma ɗaukar hotuna da bidiyo.
Yadda ake amfani da shi wajen ɗaukar bidiyo
Mai amfani da gilashin Meta na iya fara ɗaukar bidiyo ta hanyar danna maɓallin da ke jikinsa ko kuma ba da umarnin murya.
A cewar kamfanonin Meta da Ray-Ban, akwai wata ƙaramar fitila mai hasken fari a jikin gilashin, wadda ke haskakawa domin sanar da mutanen da ke kusa cewa ana ɗaukar hoto ko bidiyo.
A wasu sabbin nau'ikan gilashin, kyamarar za ta daina aiki idan aka toshe wannan fitila.
Akwai kuma wani nau'in gilashin na Meta mai suna Meta Ray-Ban Display, wanda ke da ƙaramin launi mai a cikin ɗaya daga cikin gilashinsa.
Sai dai a yayin da shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg, ke nuna wa jama'a yadda gilashin ke aiki, wasu abubuwa ba su tafi yadda aka tsara ba.
Misali, ya yi ƙoƙarin kiran gilashin ta manhajar WhatsApp, wadda ita ma kamfanin Meta ya mallaka, amma kiran bai shiga ba duk da an yi ta ƙoƙarin maimaita matakin.
Zuckerberg ya ce wa mahalarta taron: "Ban san abin da zan gaya muku ba. Kullum ina ta yin kuskure a wannan abu."
Yaushe aka fara amfani da shi?
Kamfanin Meta ya fara shiga kasuwar zamani da gilashin ne a shekarar 2023, lokacin da ya ƙaddamar da gilashin Ray-Ban Meta, wanda ya ƙera tare da haɗin gwiwar kamfanin Ray-Ban.
Tun daga lokacin, kamfanin ya ci gaba da ƙara sabbin fasahohi a cikin gilashin, musamman waɗanda ke amfani da basirar AI.
A taron masu haɓaka manhajoji na kamfanin na shekara-shekara, mai suna Meta Connect, shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg, ya sanar da ƙaddamar da wasu sababbin nau'ikan gilashi da ya ƙera tare da kamfanonin Ray-Ban da Oakley.
Daga cikin sabbin kayayyakin da aka gabatar akwai gilashin Meta Ray-Ban Display, da kuma na'urar da ake ɗaurawa a wuyan hannu mai suna Neural Band.
Zuckerberg ya bayyana wannan fasaha a matsayin wani babban ci gaba a fannin kimiyya, yayin da yake gabatar da sababbin kayayyakin a gaban ɗaruruwan mutane a cibiyar kamfanin da ke Silicon Valley, Amurka.
Kamfanin ya ce ba ya bayyana adadin gilashin da ya sayar ba, amma ana hasashen ya sayar da kusan guda miliyan biyu tun lokacin da ya shiga kasuwar a shekarar 2023.
Nawa ake sayar da shi?
Farashin gilashin Meta ya bambanta dangane da nau'in gilashin da kuma fasahohin da ke cikinsa.
A yayin taron Meta Connect, shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg, ya sanar da cewa ana sayar da sabon nau'in gilashin Oakley Meta Vanguard kan dala 499, yayin da sabon Ray-Ban Meta ke kan dala 379.
A Najeriya kuwa, farashin gilashin Ray-Ban Meta na iya farawa daga kusan Naira 300,000 zuwa Naira miliyan 3.5, gwargwadon nau'in gilashin da wurin da ake sayar da shi.
A gefe guda, kamfanin Meta na kashe makudan kuɗaɗe wajen bunƙasa fasahohin AI da ke jikinsa.
A watan Yulin 2026, Zuckerberg ya bayyana cewa kamfanin zai kashe daruruwan biliyoyin daloli wajen gina manyan cibiyoyin adana bayanai da sarrafa fasahar AI a Amurka.