Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashe 10 da za su fi yawan Musulmai a duniya nan da 2050
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Musulmi na kan hanyar zarce Kiristoci a yawan mabiyansu a duniya nan da shekarar 2035, kamar yadda hasashen da Cibiyar Bincike ta Pew Research da ke Amurka (Pew Research Center) ta fitar ya nuna.
Sai dai addinan biyu za su ci gaba da ƙaruwa a yawan mabiya.
Tsakanin shekarar 2020 da 2070, ana sa ran yawan Musulmi zai ƙaru da kaso 80 cikin 100, daga biliyan 2.02 zuwa biliyan 3.64.
A gefe guda kuma, ana hasashen yawan Kiristoci zai ƙaru da kaso 30 cikin 100 zuwa biliyan 2.96, daidai gwargwadon yadda ake sa ran yawan al'ummar duniya zai ƙaru.
Rahoton ya ce ana sa ran Musulmi za su kasance rukuni mafi saurin ƙaruwa cikin manyan addinan duniya.
Sai dai ana sa ran mabiya addinin Hindu da Yahudawa za su ƙaru ne a hankali fiye da yadda yawan al'ummar duniya ke ƙaruwa.
Haka kuma ana hasashen yawan mabiya addinin Buddha da mutanen da ba su da wani addini zai ragu
Mene ne dalilin ƙaruwar?
A cewar binciken babban abin zai haifar da wannan sauyi shi ne yawan haihuwa.
Tsakanin shekarar 2020 da 2025, an ƙiyasta cewa mata Musulmai sun haifi matsakaicin yara aƙalla 3 zuwa sama kowacce, idan aka kwatanta da yara da ƙasa da 3 ga mata Kiristoci da kuma yara ƙasa da 2 ga mata daga sauran rukunan addinai.
Masana sun ce al'umma na buƙatar matsakaicin haihuwar yara 2 ga kowace mace domin yawan jama'arta ya ci gaba da dorewa ba tare da raguwa ba.
Binciken ya kuma ce adadin mulumin duniya zuwa 2050 zai kai biliyan 3,095, 470,000.
Binciken ya kuma nuna cewa ƙaruwar za ta fi yawa a ƙasashe masu rinjayen musulmi a halin yanzu.
Kan haka ne muka yi nazarin binciken tare da zaƙulo ƙasashe 10 da ake ganin ƙaruwar za ta fi yawa nan da 2050.
1. Pakistan
Cibiyar ta Pew Research Center ta yi hasashen cewa zuwa shekarar 2050 Pakistan da ke yankin Asiya za ta zarce Indonesia a yawan musulmai a duniya.
Binciken ya yi hasashen cewa zuwa 2050 yawan musulman Pakistan zai kai miliyan 378.
A bisa hasashen da Pew Reserch ta fitar a 2020, Pkaistan na da jimillar musulmai miliyan 230.
2. Indiya
Baya ga Pakistan sai kuma Indiya mai maƙwabtaka, wanda za ta zama ta biyu a yawan musulmai a duniya a shekarar 2050 a cewar binciken.
Pew Reserch ya yi hasashen cewa yawan musulmin Indiya a shekarar 2050 zai kai miliyan 300.
Indiya na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da addinai ke da matuƙar tasiri.
Binciken da cibiyar ta gabatar ya nuna cewa Addinin Musulunci ne na biyu mafi yawan mabiya a Indiya, baya da Hindu da ke kan gaba.
3. Indonesiya
Yanzu haka 2026 ƙasar Indonesia ne kan gaba yawan musulmai a duniya, wadda aka ƙiyasta yawan musulman ƙasar a yanzu ya kai tsakanin miliyan 249 zuwa 251 million.
Amma hasashen Pew Research ya nuna cewa adadin musulman ƙasar zai kai miliyan 275 a 2050.
Ƙasar wadda ke yankin kudu maso gabashin Asiya, kashi 87 cikin 100 na al'ummarta musulmai ne.
4. Najeriya
Sai kuma Najeriya, wadda ke yankin yammacin Afirka da za ta koma matsayi na huɗu a yawan musulmai a duniya a 2050 kamar yadda binciken ya nuna.
Pew Research ya ce yawan musulman Najeriya a 2050 zai kai miliyan 226.
Najeriyar ce kan gaba a yawan al'umma a nahiyar Afirka, kuma ita ce yanzu haka ita ce ta biyar a yawan musulmai a duniya.
A cewar binciken kuma zuwa 2070 ƙasar za ta koma ta uku a yawan musulma a duniya.
5. Bangladesh
Ƙasar Bangladesh mai iyaka da Indiya za ta kasance ta biyar a jerin ƙasashen da za su fi yawan musulmi a duniya a 2050.
A cewar binciken Pew Research zuwa 2050 yawan musulman ƙasar zai kai miliyan 203.
Ƙasar wadda ita ma ke yankin Asiya, kashi 91 cikin 100 na al'ummarta musulmai ne.
6. Masar
Sai kuma ƙasar Egypt, da ake kira Masar da Hausa, wadda ke yankin arewacin Afirka.
Hasashen Pew Research ya nuna cewa yawan musulman ƙasar zai kai miliyan 151.
A tarihin musulunci akwai annabawa da dama da suka yi rayuwa ko suka ziyarci Masar.
7. Turkiyya
Haka ma binciken Pew Research ya nuna cewa Turkiyya za ta kasance ƙasa ta bakwai a jerin ƙasashen da za su fi yawan musulmai nan da 2050.
A cewar binciken yawan musulman ƙasar zai kai miliyan 98 zuwa lokaci.
Turkiyya, wadda ke yankin Turai ta jima da musulunci, inda tarihi ya nuna cewa annabawa da dama sun rayu a ƙasar.
8. Iran
Iran da ke yankin Gabas ta Tsakiya na daga cikin jerin ƙasashen da binciken ya ce adadin musulman zai ƙaru da yawa.
Pew Reseach ya ce zuwa 2050 yawan musulman Iran zai kai miliyan 100.
Iran na da daga cikin ƙasashen duniya da Musulucni ke da matuƙar tasiri, inda malaman musulunci ke jagorantar harkokin mulki da na sojin ƙasar.
9. Ethiopia
Sai kuma Ethiopia da ita ma ke yankin gabashin Afirka, wadda Pew Research ya saka ta a matsayi tara a yawan musulmai.
Binciken ya nuna cewa yawan musulman ƙasar zai kai miliyan 93 a 2050.
Kamar dai Indiya Musulunci ne addini na biyu mafi girma a ƙasar bayan Kiristanci.
10. Sudan
Ƙasa ta ƙarshe cikin jerin 10 na farko mafiya yawan musulmai a 2050 ita ce Sudan.
Binciken Pew Research ya nuna cewa zuwa lokacin yawan musulman Sudan zai kai miliyan 87.
Sudan wadda a shekarun nan yaƙi ya ɗaiɗaita ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da ake zuwa domin karantar ilimin Addinin Musulunci a jami'o'inta.