Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Putin ke yawo da akwatin makamin nukiliya a asirce
- Marubuci, Mariam Mjahid
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Yayin da shugabannin Amurka da China da kuma Rasha suka isa birnin Shenzhen da ke kudancin China a ranar Alhamis domin halartar tattaunawa tsakanin ƙasashen uku a gefen taron APEC, wani mutum sanye da kayan sojan Rasha ya ja hankalin jama'a saboda wani baƙin akwati na musamman da yake ɗauke da shi.
Yayin da kyamarar gidan talabijin na gwamnatin Rasha ta mayar da hankali kan jami'in rundunar ruwa da ke cikin tawagar Shugaba Vladimir Putin, ɗan jarida Yevgeny Popov ya nuna akwatin yana mai sanar da masu kallo cewa shi ne akwatin makullin makaman nukiliya.
Jami'in ya yi murmushi tare da tabbatar da cewa lallai akwatin ne, wanda ake kira Cheget, kuma shi ne ke bai wa shugaban Rasha damar sadarwa kai tsaye da sojojin da ke kula da makaman nukiliyar ƙasar.
Bayyanar Putin da tawagarsa tare da wannan na'ura da ake dangantawa da makaman nukiliya ta sa wasu ke kallon hakan a matsayin nuna ƙarfin soji.
Sai dai Rasha ba ta bayyana a hukumance ko tana ɗauke da wani makamin nukiliya a lokacin ba.
Lamarin ya tayar da muhawara kan ko shugaban na iya bayar da umarnin kai harin nukiliya yayin da yake halartar wani taron ƙasa da ƙasa, ko a cikin jirgin sama, ko kuma a otel.
Mkoba wa nyuklia ni nini hasa?
Akwatin nukiliyar wata na'ura ce ta musamman da ke bai wa shugaban ƙasa damar sadarwa kai-tsaye da sojojin ƙasar da ke kula da makaman nukiliya, kuma idan buƙata ta taso, ya aika da umarnin amfani da su.
An fara ƙirƙirar irin waɗannan tsare-tsaren ne a lokacin Yaƙin Cacar Baki, lokacin da Amurka da tsohuwar Tarayyar Soviet suke fafatawa sosai a fannoni na soja da makaman nukiliya.
A wancan lokaci, ana fargabar cewa za a iya kai harin nukiliya ba zato cikin ƙanƙanin lokaci.
Saboda haka, ya zama dole shugabannin ƙasashe su samu wata hanya da za ta ba su damar tuntuɓar kwamandojin soji kai tsaye ko da ba sa wuraren aikinsu na hukuma.
Hakan ne ya sa aka samar da na'urorin sadarwa na musamman waɗanda shugabanni ke iya amfani da su wajen aika saƙonni ko umarni cikin gaggawa idan wata barazanar tsaro ta taso.
Rasha na kiran wannan jakar da Cheget.
Mene ne 'Cheget' ?
Ana kiran jakar nukiliyar Rasha da suna Cheget, sunan da aka samo daga wani tsauni da ke yankin Caucasus.
An fara amfani da ita ne a shekarar 1983, a lokacin tsohuwar Tarayyar Soviet. A al'ada, wani jami'in rundunar ruwa ne ke ɗaukar jakar shugaban ƙasar.
Cheget tana da alaƙa da tsarin sadarwa da kula da ayyukan sojin Rasha da ake kira Kazbek.
Ta hanyar wannan tsari ne shugaban ƙasa ke iya sadarwa da manyan shugabannin soja tare da isar da umarni da suka shafi amfani da makaman nukiliya.
Rahotanni sun ce Rasha na da irin waɗannan jakunkuna guda uku, waɗanda ke hannun shugaban ƙasa da ministan tsaro da kuma babban hafsan hafsoshin sojin ƙasar.
Bisa manufar Rasha kan makaman nukiliya, shugaban ƙasa ne ke da ikon yanke hukuncin amfani da irin waɗannan makamai.
Sai dai makaman masu linzami ba sa iya kai hari da kansu saboda kawai an bayar da umarni.
A maimakon haka, akwai wasu tsare-tsare da matakan soja da dole su shiga tsakani wajen karɓa da tabbatar da umarnin, kafin daga bisani a aiwatar da shi.
Me ya sa shugabannin Rasha ke yawo da jakar?
Babban dalilin samar da irin wannan tsari shi ne tabbatar da cewa shugaban ƙasa na ci gaba da samun damar sadarwa da bayar da umarnin soja ba tare da la'akari da inda yake ba.
Hari na nukiliya na iya aukuwa a lokacin da shugaban ƙasa ke tafiya wata ziyara, ko yana halartar taron ƙasa da ƙasa, ko ma yana wani otel.
A irin wannan yanayi, dogaro kawai da tsarin sadarwa da ke cikin fadar shugaban ƙasa na iya zama wata matsala.
Saboda haka, an tsara tsarin irin na Cheget ne domin tabbatar da cewa shugaban ƙasa na kasancewa cikin hulɗa da manyan hafsoshin soja a kowane lokaci.
Haka kuma, kasancewar irin wannan damar na da muhimmanci a dabarun hana maƙiyi kai hari.
Manufar ita ce ƙasar da maƙiyanta suka sani cewa za ta iya mayar da martani ko da bayan an kai mata harin nukiliya, za ta fi samun kariya daga yiwuwar irin wannan hari.
Wannan shi ne abin da ake kira hana hari ta hanyar barazanar mayar da martani, wato abin da masana ke kira nuclear deterrence.
A wannan ma'ana, bayyanar wani jami'i ɗauke da jakar Cheget tare da Shugaba Vladimir Putin a China ba batun tsaro kaɗai ba ne.
Masana harkokin tsaron duniya na kallon hakan a matsayin wata hanya ta nuna ƙarfin nukiliyar Rasha a daidai lokacin da shugabannin manyan ƙasashe ke tattauna makomar tsaro da zaman lafiyar duniya.
Sauran shugabannin duniya na yawo da irin wannan jaka?
Ba Rasha kaɗai ke da irin wannan tsarin sirri ba. Amurka ma tana da makamancinsa wanda ake kira nuclear football.
Wata jaka ce ta musamman da ke tafiya tare da shugaban Amurka, wadda ke ba shi damar sadarwa da tsarin umarnin soja kan batutuwan da suka shafi amfani da makaman nukiliya.
Sai dai ba duk ƙasashen da ke da makaman nukiliya ba ne suka bayyana a sarari ko shugabanninsu na tafiya tare da irin waɗannan na'urori.
A Birtaniya, alal misali, ikon amincewa da amfani da makaman nukiliya na hannun Firaminista ne.
Duk sabon firaminista kan rubuta wasiƙu huɗu da ake kira Letters of Last Resort, waɗanda ake miƙa wa kwamandojin jiragen ruwan ƙarƙashin teku guda huɗu masu ɗauke da makaman nukiliya.
Wasiƙun suna ƙunshe da umarnin abin da za a yi idan harin nukiliya ya lalata gwamnatin Birtaniya tare da katse sadarwa da shugabancinta.
A Faransa, shugaban ƙasa ne ke da ikon yanke hukunci na ƙarshe kan amfani da irin waɗannan makamai.
Ita kuwa China, ta ce tana bin manufar "ba za ta fara amfani da makamin nukiliya ba" (no-first-use policy), ma'ana ba za ta kai wa wata ƙasa hari da makaman nukiliya ba sai idan ita kanta an kai mata irin wannan hari.
Duk da haka, ba a san ko Shugaba Xi Jinping yana tafiya tare da wata jaka ta musamman irin ta nukiliya ba.
Indiya kuma ta ce ikon amincewa da amfani da makaman nukiliya yana hannun Majalisar Siyasa ta Rundunar Umarnin Nukiliya (Nuclear Command Political Council), wadda firaminista ke jagoranta.
Pakistan da Koriya ta Arewa ma suna daga cikin ƙasashen da aka san suna da makaman nukiliya.
Ana kuma kyautata zaton cewa Isra'ila tana da irin waɗannan makamai, duk da cewa ba ta taɓa tabbatar da hakan a hukumance ba.
Sai dai bayanai kan irin na'urorin da shugabannin waɗannan ƙasashe ke amfani da su wajen sadarwa da tsarin sojojinsu na nukiliya ba su da yawa a bainar jama'a.