INEC ta faɗi rumfunan da za ta yi gwajin zaɓen shugaban ƙasa
Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta fitar da jerin rumfunan zaɓen da ta zaɓa domin gudanar da gwajin zaɓen shugaban ƙasa da za ta gudanar ranar 28 ga watan Nuwamban da muke ciki.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X ta ce a ranar za ta gudanar da gwajin abubuwa da dama da suka haɗa da tantance masu kaɗa ƙuri’a da kuma ɗora sakamakon zaɓe ta na'ura a faɗin ƙasar.
Hukumar ta ce za a gudanar da wannan gwaji ne a rumfunan zaɓe biyu a kowace mazaɓa daga cikin mazaɓun ƙasar 8,838.
INEC ta kuma wallafa rumfunan da ta zaɓa a shafinta na intanet domin masu ruwa da tsaki da kuma jama'a su gani.
Hukumar zaɓen ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen ne daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana.
“An tsara wannan gwaji ne domin auna yadda BVAS ke aiki, tantance hanyoyin tabbatar da masu zaɓe, da kuma gano duk wata matsalar fasaha da ka iya tasowa kafin babban zaɓen shekarar 2027'', a cewar INEC.