Yaushe aka fara Mauludi, kuma wane ne ya fara shi?

Asalin hoton, Getty Images
A rana irin ta yau ta 12 ga watan Rabi'ul Awwal a duk shekara ne miliyoyin Musulmi a faɗin duniya ke bikin murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Bisa maganganu mafi rinjaye, an haifi Annabi Muhammad (SAW) ne ranar Litinin a shekarar 570 a birnin Makka da ke Saudiyya.
Annabi Muhammad (SAW) ya kasance ɗa ga, Aminatu bint Wahb da Abdullahi bin Al-Mutallib, tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su.
Mahaifin Manzon Allah, Abdullahi ya rasu tun kafin a haifi manzon tsira.
Ita ma Aminatu ta rasu a shekarar 675, shekaru biyar bayan haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).
Wane ne ya fara Mauludi?

Asalin hoton, Getty Images
Mafi yawan masana tarihi suna cewa Fatimiyawan Masar, waɗanda suka mulki Masar tsakanin ƙarni na 10 da na 12 Miladiyya, su ne suka fara gudanar da bukukuwan Mauludi a matakin gwamnati.
Suna tuna wa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) tare da wasu manyan mutane na Ahlul Baiti.
Sai dai akwai wani ra'ayi da ya shahara a tarihin Ahlus-Sunnah cewa sarkin Irbil na Iraki, Muzaffar al-Din Gökböri, ya shirya babban bikin Mauludi irin wanda ya yi kama da yadda ake yi a yau.
"An fara maulidi ne tun hijira na da shekara 604, wanda kuma ya fara yin sa shi ne Sarkin Erbil na wancan lokaci wato Mozaffar ad-Din," kamar yadda Sheikh Halliru Maraya, malamin addinin Musulunci a Kaduna ya shaida wa BBC a kwanakin baya.
Shin Mauludi Bidi'a ne?
Sheikh halliru Maraya ya yi raddi ga masu cewa Mauludi bidi'a kasancewar daga baya aka ƙirƙire shi.
"Annabi Muhammad SAW ne ya fara yin nuni ga murnar ranar haihuwarsa da ake kira Maulidi, saboda an tambayi Annabi Muhammad SAW dangane da azumin ranar Litinin da ya ke yi. Sai annabin ya ce ranar ne aka haife ni", in ji Sheikh Halliru.
"Babu a inda aka ambata a Ƙur'ani ko Hadisi ko kuma malamai su yi ijma'i cewa sai Annabi ya yi kaza ne abin ya zama halal. Babban abin da za a yi la'akari da shi, shi ne Allah ya hana? Ko Annabi ya hana?"
Sheikh Halliru Maraya ya kuma ƙara da cewa ko ba komai ya kamata a girma watan da aka haifi Annabin da ya kawo musu addinin Musulunci.
"Ya kamata Musulmi su girmama watan na Maulidi kasancewar a watan ne Allah ubangiji ya bai wa duniya kyautar da babu irinta ga duniya wato haihuwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi," in ji Sheikh Maraya.
A kwanakin baya, BBC ta tambayi Sheikh Nazifi Alƙarmawi dangane da abubuwan mamakin da suka faru a lokacin haihuwar fiyayyen halitta.
- Tsagewar katangar Kisra
- Rashin naƙudar mahaifiyar Annabi SAW
- Haske ya bayyana
- Halartar annabawa da mala'iku domin karɓar haihuwa
- Annabi ya yi sujjada bayan zuwansa duniya
- An haifi Annabi da askinsa da shayinsa
- Annabi ya fara rarrafe kafin ranar suna
Abubwan da ya kamata a yi ranar Mauludi
Sheikh Halliru Maraya ya kuma lissafa wasu abubuwan da ya ce su ne ya kamata Musulmi su mayar da hankali kai a watan na Mauludi.
- Taro domin nuna mu'ujizar Annabi da halayensa domin yin koyi da shi
- Yin azumi
- Sada zumunci
- Ziyartar marasa lafiya a asibiti
- Yin sadaƙa
- Ciyar da jama'a
Sai dai malamin ya ce bai kamata a yi duk abin da shari'a ba ta amince da shi ba kamar:
- Cakuɗuwar maza da mata
- Ihwace-ihwace
- Shaye-shaye
Jerin nasabar Annabi Muhammad SAW

Asalin hoton, Getty Images
A cewar malaman nasaba, wannan sashe daga Annabi Muhammad (SAW) zuwa Adnan shi ne mafi tabbaci kuma mafi karɓuwa tsakanin masu tarihin Musulunci.
Sai dai kuma wasu masana tarihin na danganta Adnan da annabi Isma'il dan Annabi Ibrahim. Saboda haka, Annabi Muhammad (SAW) yana daga zuriyar: Annabi Ibrahim (AS) ta hannun ɗansa Annabi Isma'il (AS).
Ga jerin salsalar:
- Muhammad bn Abdullah
- bn Abdul Muttalib (Shaiba)
- bn Hashim (Amr)
- bn Abd Manaf
- bn Qusayy
- bn Kilab
- bn Murrah
- bn Ka'ab
- bn Lu'ayy
- bn Ghalib
- bn Fihr (Quraysh)
- bn Malik
- bn al-Nadr
- bn Kinanah
- bn Khuzaymah
- bn Mudrikah (Amir)
- bn Ilyas
- bn Mudar
- bn Nizar
- bn Ma'ad
- bn Adnan











