Me ya sa aka kafa ƙungiyar Izala, kuma mene ne aƙidunta?

Sheikh Abubakar Mahmud Gumi
    • Marubuci, Muhammad Buhari Fagge
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah (Izala) na ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyin addini a Najeriya da ma wasu sassan Afirka ta Yamma.

Izala dai na daga cikin manyan ƙungiyoyin addinin Musulunci da suka yi tasiri sosai kan harkokin wa'azi, ilimi da rayuwar addini a arewacin Najeriya cikin shekaru da dama.

An kafa ƙungiyar ne a ƙarshen shekarun 1970 ƙarƙashin jagorancin marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi tare da wasu malamai, da manufar yaƙi da abin da suka bayyana a matsayin bidi'o'i da kuma ƙarfafa koyarwar Musulunci bisa Alƙur'ani da Sunnah.

Tun daga lokacin, ƙungiyar ta bazu zuwa jihohi da dama na Najeriya da ma wasu ƙasashen Afirka tare da samun mabiya masu yawa.

Tun daga ranar farko da Allah ya nufi kafuwar ƙungiyar Izalatul Bidi'a dama ya yi ta ne ta kasance bisa gwagwarmaya, in Sheik Yusuf Sambo Rigachikun, ɗaya daga cikin ƙalilan na waɗanda suka shaida kafuwar Ƙungiyar Izala.

BBC ta samu wata tattaunawa ta musamman da, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun fitaccen Malami a kuma ƙusa a ƙungiyar, wanda ya bayyana mana wasu daga cikin tarihin gwagwarmayar kafuwarta.

Ya ce Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi ya fara fafutikar kafa ƙungiyar tun lokacin da yake koyarwa a tare da Aminu Kano da kuma Sa'adu Zungur a wata sakandire da ke garin Maru da ke jihar Zamfara a Arewacin Najeriya.

''Sheikh Gumi ya yi tafiya zuwa Saudiyya inda a can ya samo wani littafi na tauhidi da yake yaƙi da wasu abubuwa da suka dabaibaye addinin Musulunci a Najeriya'', in ji shi.

"Sheikh Gumi ya koyar da mu wannan littafi daga bangon farko zuwa na ƙarshe" inji Babban Malamin.

Daga cikin fitattun almajiransa har da Sheikh Sama'ila Idris wanda ya assasa ƙungiyar Izala.

Dalilin neman ɗukar malamai Musulmai da za su shiga soja su riƙa yi wa mutane wa'azi ya sa Sheikh Gumi ya bayar da sunan Sheik Isma'ila Idris kuma aka ɗuke shi aiki.

Ya fara da zama a Ibadan kan daga bisani a mayar da shin Kantagora, ya ja hankalin matasa da mutanen gari ganin yadda yake matashin soja, malami kuma mai wa'azi.

Barikin soja ta riƙa cikar kwari duk lokacin da yake karatu a tsakanin sallar magariba zuwa isha'i.

Ranar 12 ga watan Fabirairu mai cike da tarihi

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan mayar da shi Jos ne kuma wani tarihi mai zaman kansa ya fara ginuwa.

A lokacin shugaban barikin sojin suna da bambancin addini da Sheik Isma'ila Idris, wanda hakan ya sa ya riƙa fuskantar ƙorafin tara mabiyansa a cikin barikin.

''A wannan lokaci ne ya zo da shawarar raɗa wa ƙungiyar suna da samar da tsarin waɗanda za su yi shugabancinta'', a cewar Sheikh Sambo Rigachikun.

Ya ƙara da cewa a wannan lokacin ya raɗa mata "Jama'atu Izalatul Bidi'a" iya nan ya tsaya babu ƙari, sunan ya karbu mutane sun riƙa alfahari da sunan ƙngiyar suna cewa su 'yan Izalatul Bidi'a ne.

"Hakan ya faru a ranar 12 ga watan Fabirairun 1978, ko kuma 12 ga watan Maris ɗin shekarar in ban manta ba. Amma na fi ƙarfafa watan Fabirairu," in ji shi.

Sheikh Gumi bai samu zarafin zuwa ba, sai ya wakilta manyan almajiransa biyu, Sherik Lawal Abubakar da kuma Sheik Ibrahim Arab.

Daga nan manyan malamai suka shigo tafiyar irin waɗanda Sheikh Sambo ya ce zai iya tunawa sun haɗa da "Abdullahi Abubakar Tireta, Malam Hudu Ci Kaji, Muhammadu Sani Yahaya Jingir, Adamu Ibrahim Mai shafi, Muhammadu Rabi'u Aliyu Daura, Abubakar Imam Ikara, Alasan Sa'id Amad Jos, Sheik Sa'idu Hasan Jingir da dai sauransu".

''An kafa ta ne da manufar sunanta " Gusar da bidi'a da tabbatar da sunnar Annabi Sallahu Alaihi wasallam, gina makarantu da kuma koyar da addinin Musulunci", in ji shi.

Me ya janyo rabuwar Izalar Jos da Kaduna?

Fitaccen Malamin Izalar ya bayyana dalilan da suka janyo aka samu rabuwar kai tsakanin mabiya ƙungiyar Izala a 1991, har yakai an samu ta Kaduna da ta Jos.

"Shaidan yana da wasu suffofi uku da ko waye kai ba za ka iya musanta su ba, Shaidan ba rago ba ne, ba yaro ba ne, ba kuma jahili ba ne. Ya yi alƙawarin halakar da al'umar Annabi a littafi mai tsarki, shi ne ya shiga ya fita ya gwara kan mabiya," in ji Malam Sambo.

Matsaloli biyu ne, tun da fari ana zargin daman "an fi fifita ɓangaren gudanarwa sama da ɓangaren malamali da suke fita da'awa.

"Sai kuma rikicin kuɗi wanda ake zargin Sheik Isma'ila Idris ya sanya a asusunsa, in ban manta ba naira dubu 10 ne kudin da aka fita wa'azi aka samo," wannan lamari ya yi tasiri sosai ya kuma kai ga raba kan mutanen Izala.

A cewar Malamin, ɓangarori uku ne suka samar da ƙungiyar, ɓangaren malamai masu wa'azi, da ɓangaren gudanarwa da kuma ɓangaren 'yan agaji.

Shugabannin gudanarwa sun haɗa da: Alhaji Musa Maigandu Muhammad shi ne shugaban gudanarwa.

Shagabancin duka ɓangarorin uku kuma shi Sheikh Isma'ila Idris ne ke jagoranta tun da shi ne ƙashin bayan tafiyar.

"Rikicin ya samo asali ne kan wani wa'azi da muka je Maiduguri a jihar Borno daga nan ne kuma aka fara zaman doya da manja, da wanda aka ji a Fatakwal da Jos".

An ta yunƙurin sulhu amma abin ya ci tura, manyan mutane irinsu Abba Musa Riki tsohon gwamnan jihar Kaduna da Abdulƙadir Ahmad tsohon gwamnan babban bankin Najeriya.

Sheik Abubakar Gumi a lokacin ya yi baƙi larabawa da suka je (Daura) har zaunar da ɓangarorin biyu aka yi don sulhu abu ya ci tura.

"Daga nan ɓangaren gudanarwa suka haɗa kai da wasu malamai suka ce sun cire Sheikh Isma'ila Idris daga shugabanci".

Aka baiwa Malam Rabi'u Daura riƙon ƙwarya na shekara, "Muna Lafiya mun je taro Malam Rabi'u ya ga abu yaƙi ci yaƙi cinyewa ya ce ya haƙura da wannan shugabanci".

Aka gudanar da zaɓe aka zaɓi Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun a matsayin shugaban Majalisar Malamai ɓangaren Kaduna, a lokacin akwai malamai irinsu Sheikh Yakubu Musa Hassan, Abdullahi Bala Lau, Habibu Yahaya Ƙaura, Kabiru Haruna Gombe, Ibrahim Jale Jalingo duk suna ƙarƙashin ɓangaren Kaduna.

A ɓangaren Jos Sheik Isma'ila Idris na raye ya ci gaba da jagorantar ɓangaren, kafin daga bisani ya rasu a zaɓi Sheik Sani Yahaya Jingir.

Yunƙurin Sulhu a 2011

Shekaru na ta turawa, babu ga maciji da juna ɓangarorin biyu, har mabiya kan yi alfahari da cewa su ɓangare kaza suke, ga kuma banbancin fatawowi iri-iri.

Tun daga 1991 sai da aka kai 2011 Shugabancin Izala na ɓangaren Kaduna, ba kuma don mabiyanta na Jos sun amince ba ɗari bisa ɗari.

Ɓangaren Kaduna a wannan lokacin sun fi girmama ɓangaren gudanarwa inda Alhaji Musa Maigandu yake jagoranta.

Ana Hakan sai Allah ya yi wa Maigandu rasuwa. Sheikh Yahaya Sani Jingir ya umarci mabiyansu na ɓangaron Jos da sutattaro su je su yi wa mutanen Kaduna ta'aziyya.

A wannan lokacin ana zaman makoki ne a Bauchi lokacin da mutanen da ke ɓangaren Kaduna suka ga Sheikh Jingir da tawagarsa.

Ya yi musu ta'aziyya sannan ya yi wa'azi mai ratsa jiki kan haɗin kai da soyayyar juna, wannan ne ya sa aka kira zama a Sultan Bello domin neman mafita.

An yi gagarumin taro da kusan duk wanda ya amsa sunansa ɗan Izala a Najeriya sai da ya halarta.

An ruguza shugabancin ɓangarorin biyu da yardar kowa. Sannan aka samar da shugabanci guda.

An cakuɗa ɓangarorin biyu wajen shugabanci, Sheikh Jingir ya zama shugaban majalisar Malamai sannan aka naɗa Sheikh Sambo mataimakinsa.

Sheikh Abdullahi Bala Lau aka naɗa shugaban gudanarwa yayin da aka ba da wanda yake shugabancin gudanarwa daga ɓangaren Jos a matsayin mataimakinsa.

Daraktan 'yan Agaji na Kaduna Malam Mustapha Sitti ya koma mataimakin Isa Waziri Muhammad Gombe daga Jos.

Malam Kabiru Gombe daga Kaduna ya zama babban sakatare yayin da na ɓangaren Jos yake masa mataimaki.

Su wane ne Wahabiyyawa?

An yi wani babban malamin Tauhidi da ake kira Muhammad Abdulwahab, wanda ya haɗa kai da hukumomin Saudiyya domin aiki irin wanda izala ta kafu a kai.

"Lokacin da Izala ta kafu akwai harkokin tsubbu bokanci da bori sun baza ko ina, mata ba su damu da sanya gyale ko hijabi ba, amma da zuwan Izala komai ya fara sauyawa," in ji Sheikh Sambo.

To shi ma Sheikh Muhammad Abdulwahab, a ƙasarsu suna da irin waɗannan abubuwa, ya yi aiki da kira zuwa tauhidi, har ya yi fice.

"Kafin a raɗa ma Izala suna 'yan cewa ake "Na Gumi ne" dag kalmar Abdulwahab ta bayyana sai aka koma ce mana "Wahabiyyawa".

Babu wani ɗan Izala da yake jin haushi dan an kira shi Bawahabiyye, mu ɗaɗi muke ji ma saboda ana alaƙanta mu da Tauhidi.

Su wane ne Salafawa?

'Yan salafiyya asalinsu 'yan Izala ne, kuma suna kiran kansu Ahlu Sunna, ilimi da tarbiyyarus duka daga cikin izala suke a cewar sheikh sambo Rigachikun.

Yara ne da ba su san ma'anar Salaf ba in ji Sheik Sambo Rigachikun, "Duk waɗanda suke bayan Sahabbai salaf ake kiransu da waɗanda suka haɗa har da su Imamu Malik da dai sauransu,".

Akwai "wata ƙungiya da Yahudawan duniya suka samar suka raɗawa suna Salafawa kuma babu abin da suke yi sai ƙoƙarin ganin bayan addinin Musulunci''.

Akwai wata ha'ilau da ake kira Salaf wadanda wasu malamai da suke ganin akwai kura-kurai a tafiyar magata a wasu daga cikin Hadisai sau suka kafa wata ƙungiya da suke son ƙin yi biyayya ga wasu daga cikin waɗannan hadisan".

Malam ya ce har littafi ya rubuta da ya yi masa suna "Salafiyya wacce?" ciki a cewarsa ya yi bayani kan rabe-rabe da kuma yadda matasa ke cin mutuncin magabata wasu da saninsu wasu kuma ba tare da saninsu ba..