Mutum uku aka kashe a hari kan filin jiragenmu - Saudiyya
Saudiyya ta ce hare-haren da aka kai kan wasu filayen jiragen saman kasarta a cikin kwanaki biyu da suka gabata, sun yi sanadin mutuwar mutum uku tare da jikkata wasu 36.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar ta ce filin jirgin saman Sarki Khalid da ke kusa da Riyadh da kuma filin jirgin saman Abha ne suka kasance wuraren da aka kai harin.
Kungiyar Houthi da Iran ke marawa baya ta ce ita ce ta kai wadannan hare-hare.
Kungiyar dai na iko da mafi yawan yankin arewa maso yammacin Yemen, kuma tana fafatawa da dakarun gwamnatin Yemen da Saudiyya ke marawa baya domin kwace iko da yankuna, bayan da yakin basasar kasar ya sake barkewa a watan Yuli.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sabon rikicin ya tilasta wa fiye da mutum dubu 200 tserewa daga muhallansu a cikin kasar.


















