Madrid na son McTominay, Chelsea na son Frenkie de Jong

Scott McTominay
Bayanan hoto, Scott McTominay
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid na tuntuba kan kwantargin Scott McTominay da Napoli, inda Madrid ɗin ke son ɗaukar ɗan wasan a ƙarshen kakar wasanni. (Tuttomercato)

Babu tabbacin cewar ko Manchester United za ta ɗauko McTominay saboda shirinsu na son siyen matasan ƴan wasa. (Football Insider)

Bayern Munich na son tsawaita zaman Michael Olise's contract, wanda kwantaraginsa ke zai ƙarewa nan da 2029, inda ake sa ran zai ci gaba da zama da ƙungiyar, sai dai idan ttaunawar da suke yi da Real Madrid ta fada. (Sky Sports Germany)

Manchester United ta baiwa JJ Gabriel, yarjejeniyar tallafin yin karatu sai dai zai iya samu fam dubu 350,000, idan ya yanke shawarar barin ƙungiyar, zuwa wata ƙasa. (Guardian)

Chelsea na son ɗaukar ɗan wasan Barcelona Frenkie de Jong, a matsayin wanda zai maye gurbin Enzo Fernandez, da ya koma Manchester City. (Sport - in Spanish)

Liverpool ta ware wasu kuɗaɗe na fam miliyan 59.5 na ɗaukar an wasan Bayer Leverkusen Jarell Quansah, ko da kwantaraginsa bai kare ba, sai dai ana alakanta shi da Real Madrid ko Chelsea - maimakon Anfield. (Football Insider)

Juventus na kokwanton ɗaukar Nick Wolte, da ke Newcastle United a matsayin ɗan wasan aro, kuma suna neman wadan zai maye gurbinsa, inda suke sa ido kan ɗan wasan Monaco Folarin Balogun. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Newcastle da Everton na kokawar aukar ɗan wasan Galatasaray Gabriel Sara. Ɗan wasan ya shafe shekaru biyu, a Norwich City kafin daga bisani ya koma Turkiya.(Webaslan)

Hull City na dab da ɗauko Deniz Donmezer, da ke taka leda a Kayserispor, kan fam miliyan 1.5 (TeamTalk)