Limaman da za su jagoranci Sallar Taraweeh da Tahajjud a Masallacin Harami a bana

Wasu daga cikin malaman da za su yi limanci a masallacin Harami a lokacin azumin bana
Bayanan hoto, Wasu daga cikin malaman da za su yi limanci a masallacin Harami a lokacin azumin bana
An wallafa

Hukumomin Saudiyya sun fitar da jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawi da Tuhajjud a Masallacin Harami da ke birnin Makka a lokacin azumin bana.

Shafin intanet na Haramain Sharifain ya bayyana cewa limamai shida ne za su jagoranci gudanar da sallolin a bana.

Ana sa ran za a fara Azumin wannan shekarar a cikin watan Afirilu mai zuwa.

Har wa yau, hukumomin Saudiyya sun ce bana babu wasu limamai da za a gayyato domin limancin sallolin, kamar yadda ake gani a shekarun da suka gabata.

Babban limamin masallacin Ka'abah Sheikh Abdul Rahman al-Sudais na daga cikin limaman da hukumomin suka ce za su yi jagorancin sallolin.

Ga hotunan limaman da za su ja ragamar Sallolin Tarawi da Tuhajjud.

Sheikh Abdul Rehman Al Sudais
Bayanan hoto, Sheikh Abdul Rehman Al Sudais
Sheikh Abdullah Awad Al Juhany
Bayanan hoto, Sheikh Abdullah Awad Al Juhany
Sheikh Maher Al Muaiqly
Bayanan hoto, Sheikh Maher Al Muaiqly
Sheikh Saud Al Shuraim
Bayanan hoto, Sheikh Saud Al Shuraim
Sheikh Yasir Al Dossary
Bayanan hoto, Sheikh Yasir Al Dossary
Sheikh Bandar Baleela
Bayanan hoto, Sheikh Bandar Baleelah