Hotunan yadda Liverpool ta yi bikin lashe kofin Premier

Karon farko cikin shekaru 30 da Liverpool ta lashe kofin Premier
Bayanan hoto, Karon farko cikin shekaru 30 da Liverpool ta lashe kofin Premier
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool ta yi bikin kofin da ta lashe na gasar Firimiya karon farko bayan shekaru 30

Liverpool ta karɓi kofin ne a gidanta Anfield bayan ta doke Chelsea 5-3.

Jordan Henderson - wanda ke jinya - shi ya karɓi kofin daga hannun tsohon fitaccen ɗan wasan ƙungiyar Sir Kenny Dalglish a mumbari na musamman.

Jurgen Klopp ya kafa tarihi a Anfield inda karo na uku a kaka a jere ba a doke Liverpool ba a gidanta.

Tun saura wasa bakwai a ƙarƙare gasar Firimiya, Liverpool ta lashe kofin kuma yanzu wasa ɗaya ya rage inda za ta kai wa Newcastle ziyara ranar Lahadi.

Liverpool yanzu ta bar Chelsea da neman maki ɗaya a wasan ranar ƙarshe da za ta karɓi bakuncin Wolves domin samun shiga jerin ƙungiyoyi huɗun saman tebur ba da zai ba ta damar buga gasar zakarun turai ta Champions League.

Duk da cewa Liverpool ta yi bikin lashe kofinta ba tare da magoya baya ba a fili saboda annobar korona, amma bai hana wa magoya bayanta mamaye harabar Anfield ba.

Sai da ƴan sanda suka tarwatsa magoya bayan Liverpool a Anfield waɗanda suka dinga wasan wuta domin murnar nasarar ta lashe kofi bayan shafe shekaru 30.

Ga yadda Liverpool ta yi bikin lashe kofin

Liverpool
Bayanan hoto, A karon farko a tarihi ba a doke Liverpool ba a gida a kaka uku a jere.
Liverpool
Bayanan hoto, Tun saura wasanni bakwai a ƙarƙare kaka, Liverpool ta lashe kofin
Liverpool
Bayanan hoto, Liverpool ta haɗa maki 55 daga 57 a Anfield a bana a Premier League
Liverpool
Bayanan hoto, A watan Oktoban 2015 Liverpool ta ɗauko Jurgen Klopp wanda kuma yanzu ya lashe mata kofin zakarun Turai da Premier League
Liverpool
Bayanan hoto, Kwallaye 19 Mohamed Salah ya jefa a raga a gasar Premier a bana
Liverpool fans in a pub
Bayanan hoto, Liverpool ta doke Chelsea 5-3 a wasanta na ƙarshe a gida a kakar bana
Thousands of supporters gathered in the streets
Bayanan hoto, Dubban magoya baya ne suka mamaye harabar Anfield
Liverpool fan wearing a mask
Bayanan hoto, Wasu magoya bayan Liverpool sun sanya takunkumi
Fans gather outside the stadium
Bayanan hoto, An toshe wasu hanyoyi na isa zuwa Anfield
Liverpool fans applaud the team bus
Bayanan hoto, Magoya bayan Liverpool sun yi jerin gwano suna taya ƴan wasa murna