Ole Gunnar Solskjaer ya ce har yanzu Man Utd ta fi karfin Man City

Ole Gunnar Solskjaer da Pep Guardiola
Bayanan hoto, Pep Guardiola sau biyu yana doke Manchester United a Premier a kakar da ta gabata
An wallafa

Ole Gunnar Solskjaer ya yi imanin cewa har yanzu Manchester United ta fi karfin Manchester City.

Karo na bakwai kenan a jere da City ke za kasance saman abokiyar gabarta a Manchester, wanda bai taba faruwa ba tun 1930.

City ta lashe kofin Premier League sau uku tun wanda United ta lashe karo na 20 a 2013.

Kafin fafatawar da za a yi ranar asabar tsakanin kungiyoyin biyu na Manchester, an tambayi Solskjaer ko yana ganin har yanzu United ta fi karfin City sai ya ce: "Eh."

Ya kuma ce duk da suna fuskantar kalubale amma United ba za ta kariya ba.

Idan dai aka yi la'akari da yawan kofi, za a dauki lokaci kafin City ta kamo United amma kuma batun kudi City na iya ja da United.

Tun ritayar Sir Alex Ferguson a 2013, City ta doke United sau bakwai yayin da United ta yi nasara sau uku.

City kuma yanzu ta ba United tazarar maki 11 a tebur, amma Solskjaer ya ce burinsu shi ne datse yawan makin.