Jihohin Najeriya 10 da suka fi yawan masu rajistar zaɓe a 2026

Katunan zaɓe
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen Najeriya na 2027, Hukumar zaɓen ƙasar (INEC) ta bayyana cewa yawan masu rajistar zaɓe a ƙasar ya haura miliyan 110.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

Farfesa Amupitan ya bayyana matakan da hukumar ke ɗauka domin tabbatar da sahihin rajistar masu kaɗa ƙuri'a da kuma shirin gudanar da zaɓe mai inganci.

Bisa alƙaluman da hukumar ta fitar, wasu jihohi uku ne suka kasance a sahun gaba wajen yawan masu rajistar zaɓe, lamarin da ke nuna muhimmiyar rawar da za su taka a zaɓen shugaban ƙasa da sauran zaɓukan da za a gudanar a shekarar 2027.

Ga jerin johohin 10 da INEC ta ce sun fi yawan masu rajistar zaɓe.

1. Lagos — 7,488,633

2. Kano — 6,570,276

3. Kaduna — 4,662,640

4. Katsina — 3,876,051

5. Rivers — 3,736,434

6. Oyo — 3,588,111

7. Delta — 3,525,988

8. Benue — 3,052,225

9. Ogun — 3,037,981

10. Bauchi — 3,012,547

Shugaban na INEC ya bayyana jihar Ekiti da ke yankin kudu maso yammacin ƙasar a matsayin wadda ta fi ƙarancin masu rajistar zaɓe, inda take da mutum 1,055,708 Sai Bayelsa mai 1,200,691, da kuma Birnin Tarayya Abuja ke da mutum 1,732,043.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Farfesa Amupitan ya ce rajistar ta ƙaru ne sakamakon matakan da hukumar ta ɗauka na faɗaɗa damar yin rajista gabanin zaɓen 2027.

Mista Amupitan ya ce bayan zagaye uku na ci gaba da rajistar masu zaɓe da aka gudanar tsakanin Agustan 2025 zuwa Yulin 2026, yawan masu rajistar zaɓe ya kai miliyan 103.

Ya ce an yi rajistar sabbin masu zaɓe sama da miliyan 10.7 a dukkan zagayen uku, waɗanda za a tantance ta hanyar bayanan halittu (biometric verification) da hukumar INEC za ta gudanar.

Bisa ga jawabin da ya yi, Joash Amupitan ya ce manyan mutane ƴan shekara 35 zuwa 49 su ne suka fi yawa a kundin rajistar masu kaɗa ƙuri'a na babban zaɓen Najeriya na 2027, inda adadinsu ya haura mutum miliyan 43.

A cewar hukumar, wannan rukuni ne ya zama mafi girman kaso na masu rajistar zaɓe a ƙasar gabanin zaɓen 2027.

Masana harkokin siyasa sun daɗe suna kallon yawan masu rajistar zaɓe a matsayin ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke iya tasiri kan sakamakon zaɓe, musamman a jihohin da ke da ɗimbin jama'a.

A watan Janairun 2027 ne za a gudanar da babban zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokokin ƙasar, yayin da za a gudanar da zaɓukan gwamnoni a watan Fabrairu shekarar.