Ahmed Musa ya fitar da Super Eagles kunya

Ahmed Musa
Bayanan hoto, Ahmed Musa ya yi sujjada domin godiya ga Allah bayan da ya ci kwallon
An wallafa

Kwallo biyun da Ahmed Musa ya zura a minti na 49 da 75 sun bai wa Najeriya damar da doke Iceland da ci 2-0 a gasar kofin duniya.

Wannan nasara ta bai wa Super Eagles damar hada maki uku bayan wasa biyu.

Kuma a yanzu ita ce ta biyu a rukunin bayan Croatia wacce tuni ta kai mataki na gaba bayan da ta doke Argentina da ci 3-0 a ranar Alhamis.

A yanzu Ahmed Musa shi ne dan kwallon da ya fi kowanne ci wa Najeriya kwallo a tarihin gasar cin kofin duniya, inda ya zura hudu.

Najeriya za ta kara da Argentina a wasan ta karshe na rukunin D domin fayyace kasar da za ta bi Croatia domin zuwa zagayen kifa-daya-kwala 'yan 16.

Ahmed Musa
Mikel Obi
Musa
Super Eagles