Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 2 ga watan Oktoban 2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Trump ya ce Amurka da Koriya ta Kudu sun ƙullar haɓaka samar da man fetur

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙasarsa ta cimma yarjejeniyar kasuwanci da Koriya ta Kudu da ta kai dala biliyan 8.4 domin wani aikin haɓaka samar da man fetur.

    Mista Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa: “Yarjejeniyarmu da Jamhuriyar Koriya na ci gaba da zama mafi alheri. Dala biliyan 8.4 za a zuba a wani aikin samar da man fetur. Yarjejeniyar ta ƙunshi ƙara yawan haƙowa da samar da mai da iskar gas da nufin ƙarfafa jagorancin Amurka a fannin makamashi da kuma tabbatar da tsaron makamashin duniya a nan gaba.”

    Wannan sanarwar ita ce ta baya-bayan nan cikin jerin yarjejeniyoyin tattalin arziki da saka hannun jari da Trump ke jaddadawa gabanin zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki na watan Nuwamba, a daidai lokacin da yaƙin da ake yi da Iran da kuma tashin farashin man fetur ke cikin manyan abubuwan da ke damun masu zaɓe a Amurka.

    A ranar Laraba ma, Trump ya sanar da shirye-shiryen Koriya ta Kudu na saka hannun jari har dala biliyan 200 a wasu manyan ayyuka a Amurka, ciki har da gina manyan tashoshin makamashin nukiliya guda takwas, wani aikin samar da iskar gas mai ruwa a Alaska da kuma tashar samar da wutar lantarki mai ƙarfin gigawatt shida a jihar Texas.

    Sai dai Koriya ta Kudu ta bayyana cewa har yanzu ba a kammala yanke hukunci kan shiga aikin iskar gas na Alaska mai darajar dala biliyan 54 ba, tana mai cewa za a ci gaba da aikin ne kawai idan an cika dukkan sharuɗɗan kasuwanci da na doka da ake buƙata.

    Gwamnatin Koriya ta Kudu ta ce ana ci gaba da gudanar da nazarin tattalin arziki da kuma bin hanyoyin shari’a da suka shafi wannan aiki.

  2. Pakistan ta zargi Indiya da kashe mata fararen hula biyu

    Majiyoyin tsaron Pakistan sun zargi dakarun kan iyakar Indiya da kashe wasu fararen hular Pakistan biyu a kusa da iyakar ƙasashen biyu a lardin Punjab.

    Majiyoyin sun ce wasu mazauna ƙauye uku daga gundumar Kasur sun yi tafiya ne suka ɗan ketare wani ginshiƙin da ke nuna iyaka da ƴan matakai kaɗan, inda suka ce an buɗe musu wuta ba tare da wani gargaɗi ba.

    Sun kuma ce mutum ɗaya ya jikkata a harbin.

    Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Indiya kan lamarin.

    Sai dai kafafen yaɗa labarai na Indiya sun ruwaito cewa an harbe mutum biyu da ake zargin sun yi yunƙurin kutsa kai cikin yankin Punjab na Indiya.

    Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da waɗannan ikirari mabambanta da ɓangarorin biyu ke yi kan abin da ya faru a kan iyakar ƙasashen.

  3. G7 ta amince da fitar da ganga miliyan 100 na man fetur

    Ƙungiyar G7 ta masu ƙarfin tattalin arziki, ta amince da fitar da gangar man fetur miliyan 100 daga rumbunan ajiyarta.

    A wani taro da shugabannin kasashen ƙubgiyar suka gudanar sun ce mambobin ƙungiyar sun “amince da ɗaukar matakan haɗin gwiwa domin magance matsalolin makamashi, tare da kare gidaje da kamfanoni daga fuskantar tashin farashin mai da ba a yi tsammani ba.”

    A cikin sanarwar bayan taron, ƙungiyar ta ce mambobin G7 za su riƙa musayar jadawalin gyaran matatun mai tsakaninsu domin kauce wa samun tangarɗa a ƙarfin tace mai a lokaci guda.

    Ƙungiyar ta kuma ce tana ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen da ke da manyan matatun mai domin ƙara yawan samar da man da aka tace a duniya, musamman dizal.

    Haka kuma shugabannin ƙasashen sun sake jaddada aniyarsu ta kauce wa ƙaƙaba takunkumin hana fitar da kayayyakin makamashi tsakanin ƙasashen G7.

    Dama dai shugaba Trump na Amurka ya bukaci ƙasashen Turai su fitar da mai daga rumbunan ajiyarsu domin magance tsadar man da yaƙin Iran ya janyo.

  4. Trump ya buƙaci Turai ta fitar da mai daga rumbunanta don rage farashinsa

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasashen Turai sun amince su fitar da man dizal “mai yawa” daga rumbunan ajiyarsu a wani mataki na rage tashin gwauron zabi da farashin man fetur ya yi sakamakon yaƙin Iran.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce ''Turai ta amince ta fitar da ɗimbin dizal daga rumbunan ajiyarta, kuma za a fara wannan nan take''.

    Tun da farko, ƙasashe membobin Tarayyar Turai sun yi nazarin wata shawara da Faransa ta gabatar na fitar da gangar dizal miliyan 50, yayin da ƙasashen da ke ƙarƙashin Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) za su saki gangar ɗanyen mai miliyan 50 daga rumbunansu.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya kuma ruwaito cewa gwamnatin Trump ta buƙaci manyan ƙasashen Turai, ciki har da Faransa da Jamus, su fitar da gangar dizal miliyan 100 zuwa kasuwa cikin kwanaki 20.

    Sai dai a lokaci guda, ƙasashen Turai sun yi nuni da cewa duk wata yarjejeniya ta ƙarin fitar da dizal daga rumbunanta ya kamata ta kasance tare da alƙawarin Amurka cewa ba za ta ƙaƙaba haramcin fitar da wannan man zuwa ƙasashen waje ita kaɗai ba.

  5. China ta cire harajim cinikayyarta da Afirka

    A yau ƙasar China ta cire duk wani haraji da ta sanya kan cinikayya da ƙasashen Nahiyar Afrika, amma wannan ban da ƙasar Eswatini, sakamakon hulɗar da ta ke yi da Taiwan.

    China tana da manufar cinikayyar da babu haraji da ƙasashe 33 na Afirka: yanzu kuma za ta faɗaɗa ta domin ta shafi kusan sauran ƙasashen nahiyar.

    Ita ce dai babbar ƙasa mai ƙarfin tattalin arziki ta farko da ta ɗebe wa ƙasashen Afirka haraji.

    Saɓanin haka ita kuma Amurka ta ɗora harajin kashi 10 cikin ɗari kan yawancin ƙasashen Afirka.

  6. Amurka ta sake tura babban jirgin yaƙi na uku zuwa Gabas ta Tsakiya

    Rundunar sojin Amurka ta sake tura wani jirgin ruwan yaƙi na uku zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, ɗauke da jiragen yaƙi, yayin da Shugaba Donald Trump ke gargaɗin yiwuwar ƙaddamar da wasu sabbin hare-hare kan Iran.

    Jirgen wanda ke ƙunshe da wata tawagar musamman ta kai hare-hare, na nuna yadda yanayin yaƙin da Amurka ke yi da Iran ke ci gaba da sauyawa cikin sauri, yayin da zaɓukan tsakiyar wa'adin mulki a Amurka ke kara gabatowa.

    Trump ya yi barazanar cewa ƙara tsananta hare-hare bayan zaɓen har yanzu na daga cikin matakan da za a iya ɗauka, duk da alƙawurran da ya yi a baya cewa yaƙin ba zai wuce makonni kaɗan ba.

    Tawagar da ke kan hanyarta ta zuwa Gabas ta Tsakiya na ɗauke da sama da sojojin ruwa 7,000 da kuma sojojin teku na musamman na Amurka (Marines) kusan 2,000.

    Tawagar ta haɗa da rundunar yaƙi ƙarƙashin jagorancin jirgin USS Theodore Roosevelt, da kuma rundunar USS Makin Island, wadda ta ƙunshi jiragen ɗaukar sojoji guda biyu.

    Wani jami'in Amurka da ya yi magana bisa sharadin ɓoye sunansa saboda muhimmancin bayanan ayyukan soji ya ce matakin na iya haifar da kasancewar jiragen yaƙi masu sauka da tashin jiragen sama guda uku a yankin nan da ƙarshen watan Oktoba.

    Idan aka haɗa da sojojin da tuni suke yankin Gabas ta Tsakiya, wannan matakin zai sa yawan jami'an ruwa da sojojin Marines na Amurka a yankin ya haura 20,000, tare da ɗaruruwan jiragen sama.

    A watan Afrilun wannan shekara ne rundunar sojin ruwan Amurka ta kafa tawagogin jiragen yaƙi guda uku a Gabas ta Tsakiya a lokaci guda, karo na farko tun shekarar 2003.

  7. Ana gwambza ƙazamin yaƙi a kudancin Yemen

    Ana ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa a kudu maso yammacin Yemen tsakanin ƴan Houthi masu alaƙa da Iran, da kuma dakarun gwamnatin ƙasar masu samun goyon bayan Saudiyya.

    Ana kyautata zaton cewa an kashe mayaƙa kimanin 80 cikin kwana ɗaya.

    Ana samun ƙaruwar faɗa a kusa da birnin Taiz mai matuƙar muhimmanci, da kuma yankin tuddan da ke kallon tekun Maliya wanda mayaƙan Houthi suka ƙwace a baya-bayan nan.

    Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa yunwa na ƙazancewa a yankin inda yawan mutane da ke gaza samun abinci ke ƙaruwa.

    MDD ta ce ƙazancewar yaƙin ya tarwatsa mutane aƙalla 150,000 a watannin baya-bayan nan.

  8. FlyDubai Pilot: Na ƙuduri aniyar hana a kashe fasinjojin jirgina

    Kyaftin ɗan ƙasar Indiya da ke jagorantar wani jirgin saman FlyDubai wanda ya ji rauni yayin wani hari da mataimakinsa ya kai masa, ya ce ya yi ta gwagwarmayar ceto rayuwarsa amma ya ƙudurta cewa ba zai bari wasu su mutu ba.

    Da yake magana da Firaministan Indiya, Narendra Modi, Smith Machar ya ce lokacin da ya fahimci jirgin na dab da faɗuwa kuma wajibi ne ya ɗauki matakin gaggawa, ɓangaren ƙasan ɗakin matuƙan jirgin ya rushe, lamarin da ya sa ya yi ƙoƙarin shawo kan halin da ake ciki tare da taimakon wani matuƙin jirgin.

    “Na kwanta a ƙasa da rauni a cikin ɗakin jirgin, amma na gaya wa kaina cewa sai na yi ƙoƙari na ƙarshe domin buɗe ƙofar daga ciki,” in ji shi.

    “Wasu mutane ma sun shiga suka taka rawa wajen shawo kan lamarin. Hakika ina fafutukar ceton raina ne, amma a lokaci guda na san bai kamata in bari wasu su mutu ba,” kamar yadda ya yi ƙarin haske.

  9. Trump ya yi iƙrarin cewa Iran na haɗa miyagun ƙwayoyi a cibiyoyin nukiliyarsu

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin a karon farko a wani jawabin yakin neman zabensa da ya gabatar a Durant, jihar Oklahoma, cewa cibiyoyin nukiliyar Iran da jiragen saman B-2 na Amurka suka kai wa hari ana amfani da su ma wajen haɗa miyagun ƙwayoyi. Sai dai bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da wannan ikirari ba.

    Yayin da yake tuna harin da Amurka ta kai kan waɗannan cibiyoyi, Mista Trump ya ce bama-baman sun shiga cikin abin da ya kira “masana'antun miyagun ƙwayoyi”, yana mai jaddada cewa wuraren “na nukiliya ne kuma na miyagun ƙwayoyi.” Daga baya ya riƙa kiran su da suna “masana'antun miyagun ƙwayoyi/nukiliya”.

    Wannan ne karo na farko da Mista Trump ya danganta hare-haren da Amurka ta kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran da batun samar da miyagun ƙwayoyi.

    Babu wani jami'in gwamnatin Amurka ko wata majiya mai zaman kanta da ake ganin abin dogaro ce da ta ce ana amfani da cibiyoyin nukiliyar Iran da aka kai wa hari wajen samar da miyagun ƙwayoyi.

    Shugaban na Amurka ya kuma sake bayyana a Denton, jihar Texas, cewa Amurka “ba ta da wani zaɓi” illa ɗaukar mataki a kan Iran domin, a cewarsa, ƙasar na gab da mallakar makamin nukiliya.

    Ya yi ikirarin cewa Iran saura makonni kaɗan ta samu irin wannan makami, ikirarin da ya yi sau da dama a baya.

  10. Yadda Kanawa ke murnar samun ruwan famfo bayan shekara 20

    Al'ummomin wasu unguwannin birnin Kano sun bayyana farin cikinsu bayan samun ruwan famfo a karon farko cikin gomman shekaru, inda wasu unguwannin suka yi shekara 20, wasu ma har kusan shekara 30.

    Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta kammala wani ɓangare na aikin gyaran manyan matatun ruwa da bututun da ke samar da ruwan sha ga wasu unguwannin birnin Kano.

    Matsalar ruwan sha dai na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da jihar ke fuskanta, wadda ta daɗe tana ci wa mutane tuwo a ƙwarya.

    A tsawon lokaci, gyarawa tare da samar da tsabtataccen ruwan sha na cikin manyan abubuwan da ƴan siyasa ke amfani da shi a wajen yaƙin neman zaɓe a duk lokacin da aka kaɗa gangar siyasa.

    Ga al'ummar da suka shafe shekaru suna dogaro da rijiyoyin gida na dauri da na burtsatse ko kuma suka ta'allaƙa kacokam kan sayen ruwa, dawowar ruwan famfo na nufin sauƙaƙa rayuwar iyalai, musamman masu ƙaramin ƙarfi.

  11. Sojojin Yemen sun kai hare-hare 20 kan sansanonin Houthi a Taez

    Mai magana da yawun rundunar sojin gwamnatin Yemen ya sanar cewa jiragen yaƙin ƙasar sun kai hare-hare ta sama guda 20 kan wuraren mayaƙan Houthi a Taez.

    Hare-haren sun kuma shafi motoci da sauran kayayyakin soji na Houthi da ke yankin.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Saudiyya da 'yan Houthi da Iran ke marawa baya ke ƙara tsananta, inda faɗan ya kai wani matsayi mafi muni tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da Majalisar Ɗinkin Duniya ta mara wa baya a shekarar 2022.

    Idan 'yan Houthi suka karɓe cikakken iko da Taez, da ke kudu maso yammacin Yemen, hakan zai ƙara faɗaɗa tasirinsu a gabar Tekun Maliya, tare da sauƙaƙa musu isa kudancin Yemen da birnin Aden mai tashar jiragen ruwa, inda gwamnatin ƙasar ke da mazauni.

    Sake ɓarkewar faɗan ya raba dubban mutane da muhallansu kawo yanzu, kuma yana iya sauya yadda ɓangarorin da ke rikici ke iko da yankuna daban-daban na Yemen.

    Haka kuma, lamarin na iya yin tasiri kan hanyoyin sufurin jiragen ruwa a Tekun Maliya da mashigin Bab al-Mandab.

  12. Ƴansanda sun ceto mutum 10 daga ƴan NYSC da aka sace a Imo

    Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta ce jami'an tsaro sun kai samamen da ya kai ga ceto mutum 10 da 'yan bindiga suka sace a kan titin Owerri zuwa Onitsha.

    Bayanin na ƙunshe a sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Henry Okoye, ya fitar ranar Alhamis.

    "Mutanen da aka ceto suna cikin aminci kuma ana kula da su. Ana ci gaba da tantance ainihin adadin mutanen da aka sace, kuma za a sanar da jama'a da zarar an tabbatar," in ji rundunar.

    'Yan sandan sun ce sun tura jami'ai na musamman da kayayyakin aiki domin gudanar da aikin nema da kuma ceto masu yi wa Ƙasa Hidima da wasu fasinjoji da aka sace.

    A cewar rundunar, wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari kan motocin bas biyu ɗauke da masu yi wa ƙasa hidima da wasu fasinjoji da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar Alhamis, 1 ga Oktoban 2026, a kusa da Umunoha.

    Lamarin na zuwa ne bayan rahotannin cewa an sace masu yi wa ƙasa hidima 20 a kan hanya, yayin da suke tafiya daga Ibadan a jihar Oyo zuwa sansanonin horas da masu yi wa ƙasa hidima a yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudancin Najeriya.

    Rahotanni sun ce masu yi waƙasa hidimar na tafiya ne a wata motar haya lokacin da 'yan bindigar suka tare su.

    Rundunar 'yan sandan ta ce motocin biyu suna ɗauke da masu yi wa ƙasa hidima da wasu fasinjoji daga Ibadan zuwa Uyo a jihar Akwa Ibom da Bende a jihar Abia lokacin da aka kai musu hari.

  13. Ma'aikata sun fara yajin aiki kan tsadar rayuwa a Najeriya

    Ma'aikatan gwamnati a faɗin Najeriya sun fara yajin aikin gargaɗi na kwana uku, lamarin da ke ƙara matsin lamba kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan tashin farashin fetur, ƙarancin albashi da kuma tsadar rayuwa.

    Yajin aikin, wanda ya fara yau Juma'a, zai ci gaba har zuwa Lahadi. Majalisar Tattaunawa ta Ƙungiyoyin Ma’aikatan Gwamnati ta Ƙasa (JNPSNC) ce ta kira yajin aikin. Ƙungiyar ta ƙunshi ƙungiyoyin ma'aikatan gwamnati guda takwas, ciki har da ma'aikatan gwamnati, ma'aikatan lafiya, ma’aikatan jinya da ma'aikatan kamfanoni da sauran hukumomin gwamnati.

    JNPSNC na cikin gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya, kuma tana aiki tare da manyan ƙungiyoyin ƙwadago biyu na ƙasar, wato NLC da TUC.

    Yayin da NLC da TUC ke wakiltar ma'aikata daga sassa daban-daban, JNPSNC ta fi mayar da hankali kan ƙungiyoyin ma'aikatan gwamnati da batutuwan da suka shafi aikinsu da walwalarsu.

    Ƙungiyoyin na neman a rage farashin fetur zuwa naira 500 kan kowace lita, a bai wa ma'aikata tallafin kuɗi domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa, sannan a fara tattaunawa tun da wuri kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

    Shugaban JNPSNC, Kwamared Benjamin Anthony, ya shaida wa BBC cewa ma'aikata na fama da matsananciyar rayuwa sakamakon halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

    Ya ce lokacin da aka fara aiwatar da mafi ƙarancin albashin da ake amfani da shi yanzu, ana sayar da litar fetur kan naira 600, amma a yanzu farashin ya kai naira 1,430. Ya ce farashin ya ninka fiye da sau biyu, abin da ya haifar da gagarumar matsala ga ma'aikata, musamman ganin cewa albashinsu ba ya iya biyan buƙatunsu nay au da kullum.

    Anthony ya kuma ce tashin farashin man fetur ya haifar da ƙarin farashin kayan abinci, kuɗin haya da sauran abubuwan buƙatun gida.

    Ana sa ran yajin aikin zai iya kawo cikas ga ayyukan gwamnati a faɗin ƙasar, ciki har da ma'aikatu da hukumomin gwamnati a matakan tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

  14. Ƙasashe sun yi kakkausar suka kan harin Houthi a Madina

    Ƙasashe da dama sun yi kakkausar suka kan harin da 'yan Houthi suka kai wata tashar rarraba wutar lantarki a birnin Madina na Saudiyya.

    Turkiyya da Pakistan sun yi allahwadai da harin, tare da bayyana goyon bayansu ga Saudiyya.

    Haka kuma, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Bahrain, Kuwait, Jordan, Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da Ƙungiyar Haɗin Kan Musulunci sun yi tur da harin, suna mai bayyana kai hari a Madina a matsayin "keta ƴancin Saudiyya ƙarara."

    Mai magana da yawun rundunar ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta, Turki al-Maliki, ya ce harin ya lalata tashar rarraba wutar lantarki ta birnin.

    Ya ce "Bincike da shaidun da hukumomin da abin ya shafa suka tattara, bayan nazarin abin da ya faru da kuma ɓurɓushin jirgin mara matuƙi da aka yi amfani da shi, sun tabbatar da hannun 'yan Houthi wajen tsarawa da aiwatar da wannan hari."

    Al-Maliki ya ce harin ya sa ɗaya daga cikin na'urorin sauya ƙarfin wutar lantarki daina aiki, amma hakan bai haifar da katsewar wutar lantarki mai yawa ba.

    Ya ƙara da cewa tashar tana samar da wutar lantarki ga Masallacin Annabi SAW, yana mai bayyana harin a matsayin "ci gaba da yunƙurin mayaƙai na kai hari kan Masallatai Masu Alfarma Biyu."

  15. Makarantu za su kasance a rufe kan zanga-zangar ɗalibai a Faransa

    Za a rufe fiye da makarantu 400 a faɗin Faransa a yau, a yayin da za a gudanar da darussa ta intanet saboda ana kyautata zaton za a ci gaba da zanga zangar da dalibai ke yi.

    A ranar Alhamis, 'yan sanda sun kama mutum kusan 2,000, bayan ɗalibai sun rufe makarantu domin nuna rashin amincewa da cunkoson ɗalibai a azuzuwa da kuma lalacewar kayayyakin makarantu.

    Rahotanni sun ce an kuma ƙona aƙalla makarantu biyu.

    Gwamnatin Faransa ta yi tir da zanga-zangar, inda ta bayyana ta a matsayin mai cike da tashin hankali , tare da zargin jam'iyyar adawar kasar mai ra'ayin 'yan mazan jiya da tunzura zanga zangar.

  16. Amurka na matsa wa Turai ta saki man dizal daga rumbun ajiyarta

    Amurka ta buƙaci ƙasashen Turai da su hanzarta bude rumbunsu na ajiyar man dizal domin taimakawa wajen magance ƙarancin dizal da ake fama a duniya, lamarin da ya haifar da tashin gwauron zabin farashinsa.

    Wakiliyar BBC ta ce Fadar White House ta ƙara matsa lamba kan ƙasashen Turai da su saki wani ɓangare na tanadin man dizal da suke da shi, domin taimakawa rage tsadar man fetur da direbobin Amurka ke fuskanta kafin zaɓukan rabin wa’adi da za a gudanar a watan gobe.

    Sakataren Baitulmalin kasar, Scott Bessent, ya ce bai kamata a bar gonaki da kamfanonin Amurka su kaɗai su ɗauki nauyin magance matsalar ba.

    Ƙasashen Turai sun tattaunawa a kan yadda za a tunkari rikicin, bayan da Shugaba Donald Trump ya ce yana tunanin haramta fitar da dizal daga Amurka zuwa ƙasashen waje.

  17. Barka da Juma'a

    Masu bibiyar wannan shafi, barkan mu da safiyar Juma'atu babbar rana.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da ni Nabeela Mukhtar Uba.

    Ku kasance da mu, inda za mu kawo muku labarai masu ƙayatarwa game da Najeriya da ma ƙasashe maƙwabta, da kuma sauran sassan duniya.