Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Dujjal da yadda ake gane shi?
- Marubuci, Bashir Zubairu Ahmad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Dujjal ko Al-Masih ad-Dajjal ya na daga cikin manyan fitintinun ƙarshen zamani da aka yi bayaninsu a cikin hadisai na Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wa sallama. Kalmar Dajjal tana nufin yawan ƙarya da yaudara. A fahimtar Musulunci, Dujjal mutum ne da zai bayyana kafin tashin Alƙiyama, kuma zai yi babban ƙoƙari na saka mutane cikin ruɗani da kuma sa su gaskata cewa shi ne abin da ba shi ba.
A cikin hadisai, Dujjal ba wata alama ce kawai ko wata falsafa ba; an bayyana shi a matsayin mutum wanda zai fito a ƙarshen zamani. Fitinarsa za ta kasance babba sosai, har Annabi ya yi gargadi akai-akai game da ita.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da hadisai suka bayyana shi ne cewa Dujjal ba Allah ba ne, kuma Musulunci ya jaddada cewa Allah ba ya kama da halittu.
Malaman sun bayyana cewa bayyanar dujjal babbar fitina ce ta ƙarshen zamani, kuma dukan addinai sun amince da haka.
Matsayin Dujjal a addinin Musulunci
A cewar Dakta Sirajo Abubakar Magaji, Malami A kwalejin Ilmi ta tarayya ta Kwantagora a jihar Naija, "akwai wani muhimmin bambanci da ya kamata a sani, Alƙur'ani bai ambaci Dujjal da sunansa kai tsaye ba.
Bayanin Dujjal ya fito ne daga hadisan Annabi , musamman hadisai da suka zo a manyan littattafan hadisi kamar Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim.
Wannan shi ya sa malamai suke amfani da hadisai wajen bayanin siffofinsa da fitinarsa".
Dakta Sirajo ya ce, "babban haɗarin Dujjal shi ne yadda zai zo da abubuwan da za su ruɗi mutane. Hadisai sun bayyana cewa za a ba shi wasu abubuwa masu kama da mu'ujiza a idon mutane, kamar umarnin yin ruwan sama ko samar da albarkar albarkar ƙasa kamar fitowar shuka kenan, domin ya jarrabi imaninsu".
Ya ce, ba wai kawai za a gane shi dujjal ta fuskar sa ba. Babban gwajin shi ne imani da fahimtar gaskiyar Allah.
"Annabi ya yi gargadi cewa babu wata fitina daga lokacin Annabi Adam har zuwa tashin Alƙiyama da ta fi fitinar Dujjal girma", in ji shi.
Hujjoji a Musulunci game da dujjal
Addinin musulunci ya yi bayani cikakken fiye da sauran addinai akan matsayin dujjal. Dakta Sirajo Abubakar Magaji ya ce, ''Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi gargadi kai tsaye game da Dujjal
A Sahih al-Bukhari 7131, Anas bn Malik ya ruwaito cewa Annabi ya ce babu wani annabi da aka aiko face ya gargadi al'ummarsa game da Dujjal mai ido ɗaya, maƙaryaci. Hadisin ya kuma bayyana cewa akwai rubutun "Kafir" tsakanin idanunsa.
Sahih al-Bukhari 7131
Wannan hujja ce mai ƙarfi saboda ba wai hadisin ya ambaci kalmar Dujjal kawai ba; ya bayyana shi a matsayin wani mai zuwa wanda Annabi Muhammadu yake gargadin mutane a kansa.
A Sahih al-Bukhari 7128, Annabi Muhammad (SAW) ya bayyana Dujjal a cikin mafarki da cewa, ''mutum ne mai ƙarfi, mai gashin kai mai lanƙwasa, kuma ɗaya daga cikin idanunsa nakasasshe ne, kamar ƙwayar inabi da ta fito''.
Sahih al-Bukhari 7128
Haka kuma Bukhari 7407 ya sake kawo cewa Al-Masih ad-Dajjal yana da nakasa a idon dama.
Wannan yana nuna cewa a cikin hadisin Musulunci, Dujjal ba kawai wata alama ko karin magana ba ne; an gabatar da shi a matsayin wani mutum da zai bayyana a wani lokaci na ƙarshen zamani.
Annabi Muhammadu wanda shi ne annabin ƙarshe a addinin musulunci, ya ce Dujjal ba zai shiga Madina ba, inda ya ce mala'iku za su kasance a hanyoyin shiga Madina, kuma annoba da Dujjal ba za su shiga Madina ba.
Matsayinsa a Kiristanci
Kamar a Musulunci a Kirantanci ma an kawo hujjoji da dama da suka tabbatar da wanzuwar dujjal. A Kiristanci akwai ra'ayi mai suna Antichrist, wanda ake danganta shi da wani babban maƙiyin Almasihu ko mai yaudarar mutane a ƙarshen zamani.
Amma bai dace a ce Dujjal na Musulunci da Antichrist na Kiristanci abu ɗaya ne kai tsaye ba tare da ƙarin bayani ba.
Akwai kamanceceniya a wasu fannoni: duka suna da alaƙa da yaudara, kuma sukan zo a ƙarshen zamani, lokaci da aka samu rikici na addini. Amma nassosin Musulunci da na Kiristanci suna da bayanai da fahimtohi daban-daban game da waɗannan siffofi.
Saboda haka, idan ana kwatanta su, ya fi dacewa a ce akwai kamanceceniya tsakanin ra'ayoyin, ba wai dole ne su kasance mutum ɗaya bisa dukkan koyarwar addinan ba.
Hujjoji a Kiristanci game da dujjal
Akwai surori daga littafin Linjila na Baibul da suka yi magana akan dujjala a addinin kiristanci.
Yahaya 2:18
A cikin 1 Yohana 2:18, an ce "Kiristoci sun ji cewa Antichrist zai zo, sannan aka kuma ce akwai "antichrists" da yawa. Wannan shi ne ɗaya daga cikin mafi bayyanannun wuraren da kalmar Antichrist ta fito a Sabon Alƙawari"
Tasalonikawa 2:3–10
A wannan wuri an bayyana cewa akwai kamanceceniya mai ƙarfi da bayanin Dajjal a wasu fannoni. Bulus ya yi magana game da wani mutum da za a bayyana kafin "ranar Ubangiji." An kira shi
.
Matsayinsa a Yahudanci
A cikin Yahudanci na gargajiya, babu wani mutum da ya yi daidai da Dujjal na Musulunci a kowane bayani.
Akwai koyarwa da tatsuniyoyi daban-daban game da ƙarshen zamani, Almasihu, da wasu abokan hamayya ko manyan rikice-rikicen ƙarshen zamani. Amma tsarin Dujjal, musamman yadda hadisai Musulunci suka bayyana shi, ba shi ne ainihin tsarin Yahudanci ba.
Don haka ya kamata a guji cewa "Yahudawa suna da Dujjal" a matsayin magana ta gaba ɗaya. Wannan zai iya zama rashin daidaito da koyarwar Yahudanci.
Hujjojin Yahudanci game da dujjal
A Yahudanci ma kamar sauran addinan da suka ambato dujjal, an yi bayanai da dama da ake dangantawa da dujjal. Ga wasu jerin littafan da rubuce-rubucen da suka yi magana akansa:
Sefer Zerubbabel
Wannan shi ne ɗaya daga cikin muhimman rubuce-rubucen Yahudawa na annabcin ƙarshen zamani. An danganta shi da Zerubbabel, kuma yana magana game da abubuwan da za su faru kafin zamanin Almasihu.
A cikinsa an ambaci Armilus, wani mugun sarki da zai bayyana kafin Almasihun Yahudawa. Bayanin ya ce zai sami babban iko, ya yaƙi masu bin Almasihu, sannan daga ƙarshe Almasih ɗan Dawuda zai kayar da shi.
Otot ha-Mashiach da aka fi sani da "Alamomin Almasihu"
Wannan wani rubutu ne na Yahudawa game da ƙarshen zamani. Shi ma yana ambaton Armilus a matsayin babban abokin hamayyar Almasihu.
Abin sha'awa shi ne, bayanin ya ce Armilus zai yi ikirarin cewa shi ne Almasihu, har ma ya ɗauki kansa kamar Allah, kuma wasu mutane za su yarda da shi.
Wannan ne ya sa wasu masu kwatanta addinai suke ganin kamanceceniya tsakanin Armilus da Dajjal.
Tefillat Rabbi Shimon ben Yohai
Wannan ma yana cikin rubuce-rubucen apocalyptic na Yahudawa. A cikinsa an ambaci Armilus a matsayin babban maƙiyin Almasihu a ƙarshen zamani.
Midrash Vayosha
Wannan wani littafi ne da ke ɗauke da labaran ƙarshen zamani. A cikinsa ma akwai Armilus, wanda aka bayyana shi a matsayin mugun abokin hamayyar Almasihu.
Yaushe dujjal zai bayyana?
A dukan addinan nan uku na Musulunc da Yahudanci da Kiristanci ba a bayyana takamaiman rana ko shekarar bayyanar Dujjal ba. Babu wani ingantaccen nassi da ya ba da kwanan wata da za a ce: "A shekara kaza Dujjal zai fito."
Dakta Sirajo Abubakar Magaji ya ce, "Hadisai sun sanya bayyanarsa cikin manyan abubuwan da za su faru kafin tashin Alƙiyama. Amma ƙoƙarin ɗaura shi da wani takamaiman zamani ko wani mutum na yanzu ba shi da tushe tabbatacce daga nassosin Musulunci".
Saboda haka, idan wani ya ce ya san ainihin ranar bayyanar Dujjal, wannan magana tana buƙatar hujja mai ƙarfi, domin ilimin lokacin waɗannan abubuwa yana cikin abin da Allah Ya bar wa kanSa sani.
Ya ake gane dujjal?
An bayyana wasu siffofinsa na zahiri. Daga cikin shahararrun bayanan akwai cewa yana da nakasa a ɗaya daga cikin idanunsa, kuma an bayyana ɗayan idonsa da kalmar "kamar inabi mai kumbura" a wasu riwayoyi da hadisai an ce za a rubuta alamar a goshinsa, kuma mumini zai iya gane wannan alamar.
Haka ma Kiristanci ya bayyana dujjal da irin waɗannan siffofi na cewa zai danganta kansa da Allah, zai ƙaryata Yesu Almasihu zai zama mai yaudara da ruɗar da tunanin mutane.