Yadda Kanawa ke murnar samun ruwan famfo bayan shekara 20

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Al'ummomin wasu unguwannin birnin Kano sun bayyana farin cikinsu bayan samun ruwan famfo a karon farko cikin gomman shekaru, inda wasu unguwannin suka yi shekara 20, wasu ma har kusan shekara 30.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta kammala wani ɓangare na aikin gyaran manyan matatun ruwa da bututun da ke samar da ruwan sha ga wasu unguwannin birnin Kano.

Matsalar ruwan sha dai na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da jihar ke fuskanta, wadda ta daɗe tana ci wa mutane tuwo a ƙwarya.

A tsawon lokaci, gyarawa tare da samar da tsabtataccen ruwan sha na cikin manyan abubuwan da ƴan siyasa ke amfani da shi a wajen yaƙin neman zaɓe a duk lokacin da aka kaɗa gangar siyasa.

Ga al'ummar da suka shafe shekaru suna dogaro da rijiyoyin gida na dauri da na burtsatse ko kuma suka ta'allaƙa kacokam kan sayen ruwa, dawowar ruwan famfo na nufin sauƙaƙa rayuwar iyalai, musamman masu ƙaramin ƙarfi.

Ruwan famfo ya zama baƙo ga yara a Kano

A unguwar Aikawa da ke Kwanar Dala, kusa da Kantin Ɗan Kurma, wasu yara da mazauna yankin sun shiga shewa da farin ciki a daidai lokacin da suka yi ido biyu da ruwan famfo.

Ga waɗannan ƙananan yara, wannan ne karon farko da suka ga ruwan famfo na kwarara a unguwarsu, kasancewar da yawansu tun kafin a haife su ruwan famfo ya daina zuwa.

Shamsu, wani mazaunin Jakara, ya ce da misalin karfe 10 na safe ne ruwan ya fara ɓulɓulowa a unguwarsu.

"Mun yi farin ciki. Muna godiya, duk da cewa nauyi ne ya sauke, amma mun gode. Wannan unguwa ce ta masu ƙaramin ƙarfi, saboda haka muna matuƙar farin ciki da wannan gyara da aka yi."

Shi ma Shuaibu Tsoho, wani mazaunin yankin, ya ce samun ruwan ya rage musu wahalar ɗebo ruwa da sayensa.

"Mun yi farin ciki sosai saboda muna shan wahala wajen ɗebo ruwa da sayo shi. Yanzu kuwa mun same shi, muna godiya ga Allah."

Sai dai wasu mazauna Jakara sun bayyana fargabar cewa kada ruwan ya sake daina zuwa.

Wani mazaunin yankin ya ce sun shafe sama da shekara 20 ba tare da samun ruwan famfo ba.

"Mu a Jakara mun fi shekara 20 babu ruwa, amma jiya kawai sai ga ruwa ya fara malala. Amma yau ban ga ruwan ba. Na ji sanarwar cewa ana gyara ne. Muna fata Allah ya sa ya ɗore, ba tare da an mayar da shi batun kamfe ko siyasa ba."

Unguwannin da suka fara samun ruwan famfo

Ga wasu daga cikin unguwannin da aka fara ganin ruwan famfo:

  • Kansakali
  • Goron Dutse
  • Dokawa
  • Kofar Wambai
  • Ƴan Mota, Kwanar Gabari
  • Jakara
  • Kwanar Dambazau
  • Aikawa
  • Kwanar Dala

'An kashe kusan naira biliyan 22'

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kano, Hashim Ɗahiru, ya ce gwamnatin jihar ta kashe sama da kusan naira biliyan 22 wajen gyaran manyan matatun ruwa da bututun da ke kai ruwa zuwa birnin Kano.

A cewarsa, aikin ya haɗa da gyaran matatun ruwa da manyan bututun da ke tura ruwa daga Chalawa da Tamburawa zuwa wuraren ajiya da rarrabawa a cikin birnin.

Ya bayyana cewa ruwan daga Chalawa yana tafiyar kusan kilomita 15.6 kafin ya haura zuwa Goron Dutse, inda ake da manyan ma'ajiyar ruwa da ke iya daukar kusan lita miliyan 40.

Kwamishinan ya kuma ce an gyara wasu daga cikin ma'ajiyar ruwa da ke Goron Dutse, waɗanda suka shafe sama da shekara 20 ba a amfani da su yadda ya kamata.

A cewarsa, dawo da waɗannan ma'ajiyoyi da bututun ruwa cikin aiki ya taimaka wajen fara isar da ruwa zuwa wasu unguwannin birnin.

Ya ce gwamnati na sa ran faɗaɗa aikin zuwa sauran unguwannin da har yanzu ba sa samun ruwan famfo.

"Ko ina za a samu ruwa, kuma muna da tabbacin cewa zai dore. Burinmu shi ne dukkanin gidajen ruwa su koma aiki dari bisa dari," in ji shi.

'Dalilin da ya sa aka samu tsaiko'

Kwamishinan ya ce wasu daga cikin bututun da aka gina shekara 10 zuwa 30 da suka gabata sun lalace, yayin da wasu kuma suka samu matsala sakamakon ayyukan gine-gine da tituna da aka yi a kansu.

Ya ce bayan an saki ruwa, jami'an hukumar na bibiyar layukan ruwa domin gano wuraren da suka lalace da kuma gyara su.

"Mun saki ruwa, sannan muna bi a hankali muna duba wuraren da bututun suka lalace domin gyara su," in ji kwamishinan.

Yayin da wasu unguwannin ke murnar sake ganin ruwan famfo bayan shekaru masu yawa, mazauna yankunan sun ce babban burinsu shi ne ruwan ya ɗore, ba a lasa musu zuma a baki ba.