Trump ya buƙaci Turai ta fitar da mai daga rumbunanta don rage farashinsa

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasashen Turai sun amince su fitar da man dizal “mai yawa” daga rumbunan ajiyarsu a wani mataki na rage tashin gwauron zabi da farashin man fetur ya yi sakamakon yaƙin Iran.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce ''Turai ta amince ta fitar da ɗimbin dizal daga rumbunan ajiyarta, kuma za a fara wannan nan take''.
Tun da farko, ƙasashe membobin Tarayyar Turai sun yi nazarin wata shawara da Faransa ta gabatar na fitar da gangar dizal miliyan 50, yayin da ƙasashen da ke ƙarƙashin Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) za su saki gangar ɗanyen mai miliyan 50 daga rumbunansu.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya kuma ruwaito cewa gwamnatin Trump ta buƙaci manyan ƙasashen Turai, ciki har da Faransa da Jamus, su fitar da gangar dizal miliyan 100 zuwa kasuwa cikin kwanaki 20.
Sai dai a lokaci guda, ƙasashen Turai sun yi nuni da cewa duk wata yarjejeniya ta ƙarin fitar da dizal daga rumbunanta ya kamata ta kasance tare da alƙawarin Amurka cewa ba za ta ƙaƙaba haramcin fitar da wannan man zuwa ƙasashen waje ita kaɗai ba.


























