Afcon 2021: Hotunan yadda Super Eagles ta casa Sudan

An wallafa

Najeriya ta barje gumi da Sudan a yau Asabar a wasan rukunin na biyu a gasar cin kofin Afirka da ake gudanarwa a Kamaru.

An yi wasan ne a Garoua filin wasa na Roumde Adjia inda rukuni na hudu da ya kunshi Najeriya da Masar da Sudan da kuma Guinea Bissau suke ta su fafatawar.

G
Bayanan hoto, Cikin minti na uku da fara wasan dan wasan gaban Najeriya Samuel Chukwueze ya jefa kwallon farko a wannan wasa
G
Bayanan hoto, Ndidi da Simon lokacin da ake murnar cin kwallo ta biyu a dokewar da Spuer Eagles ta yi wa Sudan
G
Bayanan hoto, Wasan ya bai wa Najeriya damar tsallakawa zagaye na yan 16 na gasar
g
Bayanan hoto, Bayan Najeriya ta jefa kwallo ta uku ta samu nutsuwa a wasan duk kuwa da cewa daga baya ta fuskanci matsi daga hannun Sudan
G
Bayanan hoto, Matsin da Sudan ta yi ya sanya ta samu damar zare kwallo guda ta hannun dan wasanta Daiyeen ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida
G
Bayanan hoto, Tun bayan kwallo ta uku da Najeriya ta ci ba ta samu damarmaki ba kamar yadda ta samu a minti 45 din farko